25/05/2024
Assalamu alaikum wa rahmatullah
Yanzu na shiga youtube na ci karo da wani video na Prof. Umar Sani Fagge, in da yayi tsokaci akan cryptocurrency.
Hakika Malam yayi maganganu masu taba zuciya kuma masu ma'ana. A cikin maganar da yayi ya bada ka'idoji guda uku da kasuwanci ke iya halatta, ma'ana idan ka cika wannan ka'idojin uku to abinda ka samu daga wannan kasuwancin Halal ne, indai ba akwai wani nassi karara da ya haramta abinda kake kasuwanci ba.
Na farko Malam yace kana bukatar hannun jari, ma'ana capital da zaka zuba domin juyawa da niyyar idan haja ta kara daraja ka sayar ka samu riba.
Na biyu Malam yace kana bukatar ilimin gudanar da kasuwanci, wanda idan muka dauko wannan maganar zuwa crypto zamu iya kiran wannan da ilimin Analysis (Both Technical, Fundamental, On-chain and other related skills) a trading.
Na uku malam yace idan ka hada wadancan abubuwa biyu, sai kuma ka jira masu saya.
Malam yayi wannan maganar cikin minti dayan farko na Video din, wanda kuma hakan ya fito da masu trading cryptocurrency na spot trading bisa ilimi cewa lallai Halal suke ci, domin mun cika duka ka'idojin; muna saka kudinmu a matsayin jari, sannnan mun bata lokaci shekara da shekaru muna neman ilimi har Allah ya mana muwafaka muka iya analysing kasuwa, mu gane me ya kamata mu saya, a ina ya kamata mu saya sannan a ina ya kamata mu sayar, sannan idan mukayi analysis sai mu sayi coins da muke ganin za'a samu riba dasu, mu rikesu mu jira har lokacin da farashinsu zai tashi kuma a samu masu saya mu sayar musu a exchange (DEX ko CEX).
Bayan Malam ya gama wannan bayanin sai ya tambayi almajiransa shin akwai wannan abubuwan guda uku? sai wasu s**a ce babu, wanda hakan ya tabbatar da cewa lallai basu fahimci menene crypto trading ba da yanda yake gudana. Wannan amsa da aka baiwa malam sai ya dora akanta, cewa toh indai babu wancan abubuwa 3 toh lallai haram ne kuma bai halatta ba, har ya kawo misalai wanda suke nuna Malam ya danganta crypto da ponzi schemes da sauran dampara da akeyi da kuma get rich quick schemes.
Amma da na tsaya na fahimci su almajiran, sai na gane suna kokarin danganta lamarin da mining ne; wanda shi kuma mining ba trading bane, wani aiki kake yi ake biyanka, wanda na tabbatar idan aka yiwa Malam bayaninsa shima, da yanda yake aiki tabbas malam bazai haramtashi ba.
In sha Allah a wannan satin (Ranar Litinin mai zuwa) zan yi hira a Premier Radio 102.7 FM dake Kano da misalin 7:05pm na yamma (Magariba zuwa Isha) domin yin bayani akan menene mining da kuma bambamcinsa da crypto da trading domin abubuwa su kara fita fili.
Ga link na video din a comment domin kuma ku kara zama alkalai, idan kuma akwai kuskure a cikin rubutuna sai ku min gyara.
Nagode
Sabiu Muhammad Danpullo