Yasir Lawan Tarauni

Yasir Lawan Tarauni CEO
Yasla Medialinks🌏
(3)

20/08/2026

19/08/2026


Muyi hattara matasa.
Bakar ashana kona gari!

INEC ta sanar da cewa Adeleke na Jam'iyyar Accord shine ya lashe zaɓen Jihar Osun
16/08/2026

INEC ta sanar da cewa Adeleke na Jam'iyyar Accord shine ya lashe zaɓen Jihar Osun

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yana ƙal...
14/08/2026

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yana ƙalubalantar cancantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Atiku ya shigar da ƙarar ne kan zargin cewa Tinubu ya gabatar wa INEC da takardar shaidar kammala NYSC da ake zargin ta bogi.

A cikin ƙarar, Atiku ya nemi kotu ta haramtawa Tinubu shiga zaben saboda wannan zargi.

Kano na da yara 875,593 da ba sa zuwa makaranta — Jami’iWani sabon bincike ya nuna cewa jihar Kano na da yara 875,593 da...
14/08/2026

Kano na da yara 875,593 da ba sa zuwa makaranta — Jami’i

Wani sabon bincike ya nuna cewa jihar Kano na da yara 875,593 da ba sa zuwa makaranta.
Adadin ya ragu idan aka kwatanta da alkaluman shekarar 2023, abin da ke nuna akwai ɗan ci gaba wajen shawo kan matsalar.
Hukumomin jihar Kano na ci gaba da daukar matakai domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma tabbatar da cewa yara sun samu damar samun ilimi.

Zaben Osun dole ne ya kasance cikin ’yanci da adalci — Tinubu ya umurci INEC gabanin zaben AsabarShugaba Tinubu ya bukac...
14/08/2026

Zaben Osun dole ne ya kasance cikin ’yanci da adalci — Tinubu ya umurci INEC gabanin zaben Asabar
Shugaba Tinubu ya bukaci hukumar INEC da jami’an tsaro su tabbatar da cewa zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026, ya kasance cikin ’yanci, adalci da gaskiya.
Ya kuma bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da tsaron masu kada kuri’a da kuma gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

14/08/2026

Saƙon Nazifi Asnanic: Unguwa-Unguwa Movement for Abba Kabir Yusuf

Matatun man fetur na Nijeriya za su dawo aiki yadda ya kamata - TinubuShugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa...
14/08/2026

Matatun man fetur na Nijeriya za su dawo aiki yadda ya kamata - Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ma’aikatan man fetur na kasar cewa matatun man Nijeriya da s**a kwashe shekaru suna fama da rashin aiki yadda ya kamata, za su koma aiki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta Nijeriya (NUPENG) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Rahotanni sun ce jami’an leƙen asirin Amurka sun yi shakku kan wani bayani da Isra’ila ta bai wa Amurka cewa Iran na shi...
14/08/2026

Rahotanni sun ce jami’an leƙen asirin Amurka sun yi shakku kan wani bayani da Isra’ila ta bai wa Amurka cewa Iran na shirin kashe Shugaba Donald Trump. Wannan zargin ne ya sa aka ƙara tsaurara matakan tsaro yayin da Trump ke barin taron NATO a Turkiyya.
Jaridar The Washington Post ta ruwaito cewa jami’an leƙen asirin Amurka ba su ɗauki bayanan da aka samo daga Isra’ila a matsayin tabbataccen barazana ba, inda s**a bayyana matakin amincewarsu da bayanan a matsayin “ƙasa.”
Duk da haka, Hukumar Tsaron Fadar Shugaban Amurka (Secret Service) ta yanke shawarar cewa ba za ta yi sakaci da yiwuwar barazanar ba. Hakan ya kai ga wani shiri na sirri inda aka fitar da Trump daga jirgin Air Force One sannan aka kai shi wani ƙaramin jirgin soja domin komawa Amurka.
Binciken da aka gudanar daga baya bai gano wata hujja mai ƙarfi da ke tabbatar da cewa akwai wani shirin kai hari na gaggawa kan Trump ba.

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya shiga sahun Gwamnonin APC da mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na Ƙasa na jam...
13/08/2026

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya shiga sahun Gwamnonin APC da mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na Ƙasa na jam’iyyar, domin kai ziyara ta musamman zuwa Jihar Osun.
Ziyarar na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen Gwamnan Jihar Osun mai zuwa, yayin da shugabannin APC ke ƙara ƙaimi wajen neman goyon baya da ƙarfafa yakin neman zaɓen jam’iyyar.

Address

Kano Zoo Road
Kano
50017

Telephone

+2349077667142

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yasir Lawan Tarauni posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Yasir Lawan Tarauni:

Shortcuts

Share