
14/07/2025
Addinin Musulunci ya hana murna ko jin daɗi a lokacin da wani Musulmi ya mutu.
Duk wanda ke murna ko mummunar Addu'a zuwa ga marigayi BUHARI, kada ya manta shima zai mutu, kuma watakila kafin ya mutu zai iya aikata wani babban laifi da yake so mutane su nema masa gafara a wajen Allah bayan mutuwar sa.
Ko da mutum ya yi kuskure, ko ya aikata wani laifi, Wauta ne a lokacin mutuwarsa ka zake da murna kana dariya da jin daɗi kana masa mummunar Addu'a.
Bai k**ata Musulmi yayi mummunar Addu'a ga Musulmi ɗan uwansa wanda Allah ya karɓi rayuwarsa ba.
Ya k**ata mutuwar wani ta zama babban darasi ga mai hankali ba abin murna ba.
Amma sai ka ga wasu idan wani ya mutu: Suna dariya, Suna zagi, Suna murna da mutuwar sa, musamman saboda siyasa ko wata kiyayya ta Addini da suke masa.
Kowane rai zai mutu, wanda ke jin daɗi da murna shi ma zai mutu. Kuma Allah ne ke hisabi ba Mutum ba.
Ya Allah ka tsare mu daga Wauta da duhun zuciya. Ka ba mu ladabi da tausayi. Ka sa mutuwarmu ta zama alheri a gare mu.
Naxeer Kaoje