15/09/2026
Akalla mutum tara ne ake fargabar sun rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun bude wuta kan wata motar haya a mahadar Dungus Junction, da ke yankin Kuuru a Karamar Hukumar Jos ta Kudu, Jihar Filato.
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:40 na dare, bayan da direban motar da ke kan hanyarta zuwa Jos ya tsaya a mahadar domin sauke wasu fasinjoji.
Rahoton ya ce maharan sun yi ta harbin motar, lamarin da ya jikkata wasu fasinjoji tare da haddasa asarar rayuka. An kuma ce an ga jini a cikin motar bayan harin.
Malam Lawan Suleiman, malamin daya daga cikin wadanda aka kashe, ya ce direban motar dalibinsa ne, yayin da wasu mutum uku daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su s**a fito daga yankin Bukuru.
A cewar sa, an kai gawarwakin wasu daga cikin wadanda s**a mutu asibiti, yayin da ‘yan uwansu ke kokarin karbarsu domin gudanar da jana’iza.
Kakakin Kungiyar Matasa ta Kabilar Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa daga cikin wadanda aka kashe har da wani jami’in Operation Rainbow.
Ya kara da cewa wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibiti, inda daga bisani wasu s**a rasu.
Ya zuwa lokacin wallafa rahoton, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ba ta fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba.