
04/08/2025
Uwargidar Gwamnan Jihar Kebbi Ta Bukaci FIDA Ta Kara Zage Dantse Wajen Yaki Da Cin Zarafin Mata
04/08/2025
Uwargidar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, ta bukaci Kungiyar Lauyoyin Mata ta Najeriya (FIDA), reshen Jihar Kebbi, da su kara himma wajen yaki da cin zarafin mata da yara a jihar. Ta bayyana haka ne yayin wata ziyarar girmamawa da kungiyar FIDA ta kai mata a ofishinta dake fadar Gwamnati a Birnin Kebbi, ranar Litinin.
A cewar Uwargidar Gwamna, akwai bukatar hadin gwiwa daga bangarori daban-daban domin rage cin zarafin mata zuwa mafi karancin matsayi a jihar. Ta yabawa FIDA bisa kokarinsu na bayar da tallafin shari’a kyauta ga wadanda abin ya shafa, tare da bayyana cewa ofishinta zai ci gaba da marawa ayyukan FIDA baya domin tabbatar da kare hakkin mata da bunkasa walwalarsu.
Tun da farko, Shugabar FIDA ta Jihar Kebbi, Barrista Hauwahu Usman, ta sha alwashin ci gaba da goyon bayan wannan gwamnatin tare da neman hadin kai da ofishin Uwargidar Gwamnan wajen inganta rayuwar mata. Ta yaba da irin kokarin da Uwargidar ke yi wajen tallafa wa mata da bunkasa walwalarsu a jihar.
Barrista Usman ta kuma bayyana wasu daga cikin ayyukan FIDA, musamman wajen bayar da kariya da kuma tabbatar da adalci ga wadanda s**a fuskanci cin zarafi.
Wannan ziyara ta kara tabbatar da kudirin FIDA na yin aiki tare da gwamnatin jihar Kebbi domin kare hakkin mata da bunkasa rayuwarsu.
Daga :
Hafiz Umar
Mai Baiwa Matar Gwamna Shawara Akan Kafafen Sadarwa
Sponsored!