GIDA DA WAJE

GIDA DA WAJE LABARAN GIDA DANA WAJE

Tashin Farashin Kayayyakin Najeriya Iri Ɗaya Ne Da Na Sauran Kasashe, Cewar EmefieleGwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN)...
27/11/2022

Tashin Farashin Kayayyakin Najeriya Iri Ɗaya Ne Da Na Sauran Kasashe, Cewar Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu bambanci tsakanin tashin farashin kayayyakin da ake fama da shi a kasar nan da na sauran kasashen duniya.

Ya ce hatta karin da aka samu na tashin farashin daga kaso 15.60 cikin 100 a watan Janairun 2022 zuwa kaso 20.77 a watan Satumba, iri daya ne da na sauran kasashen duniya.

Gwamnan Adamawa ya tsallake rijiya da baya
Emefiele ya bayyana haka ne yayin taron cin abincin dare da Cibiyar Kula da Aikin Banki ta Najeriya (CIBN) ta shirya a Legas karo na 57.

Gwamnan bankin ya ce yadda farashin kayayyakin ya yi tashin gwauron zabo a watan Satumba ya biyo bayan yadda ya rika sauka a shekarar 2021, sakamakon manufofin da s**a daidaita tattalin arziki a shekarar.

A cewarsa, “Har yanzu kayan abinci ne ke kan gaba wajen karuwar farashi. Hakan ya nuna karuwar da aka samu da kaso 23.34 a watan Satumba.

“Kazalika, a wannan tsakanin, ainihin farashin kayayyaki ya tashi daga kaso 13.87 zuwa kaso 17.60 a watan Janairu.

“Kari a kan ragowar dalilai na kasa da kasa, faduwar darajar Naira sakamakon yawan shigo da kaya daga ketare da kuma karuwar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankunan da s**a fi noma abinci a nan Najeriya su ma sun dada ta’azzara abubuwa,” inji Emefiele.

Gwamnan na CBN ya kuma ce annobar COVID-19 da aka yi fama da ita a shekarar 2020 wacce duniya ta shafe kusan shekara 100 ba ta fuskanci matsin tattalin arziki irin nata ba ita ma ta taimaka wajen kara hauhawar farashin kayan.

BARKANKU DA ZUWA PAGE DINMU, MUNA FATAN ALLAH YABIYAWA KOWA BUKATUNSHI NA ALKAIRI🙏
27/11/2022

BARKANKU DA ZUWA PAGE DINMU, MUNA FATAN ALLAH YABIYAWA KOWA BUKATUNSHI NA ALKAIRI🙏

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GIDA DA WAJE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share