04/09/2025
Rundunar Ƴan Sandan Kaduna Ta Aika Wa El-Rufai Sammaci
Daga Yasir Kallah
Rundunar Ƴan Sandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, da kuma wasu jagororin jam'iyar ADC na jihar Kaduna.
A dangane da wata wasiƙa da Daily Trust ta yi iƙirarin gani, rundunar ta gayyace su domin amsa tambayoyi a game da zargin aikata maƙarƙashiya, tayar da zaune tsaye a cikin al'umma, ɓarna, da kuma haifar da ƙuntatawa mai muni.
Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda mai kula da Sashen Binciken Laifuka (CID) na jihar, Uzairu Abdullahi ne ya sanya wa wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 4, ga Satumba, 2025, hannu.
Wasiƙar ta ce, "A yanzu haka wannan sashen yana bincike a kan taƙaddamar da aka ambata a sama wadda ta ƙunshi waɗannan mambobin na jam'iyyarku. Ana buƙatarka da ka taho tare da su zuwa SCID a ranar 8 ga Satumba, 2025, domin su yi bayani a kan zarge-zargen da masu ƙorafin s**a shigar a kansu.
"Mal. Nasir El-Rufa’i, Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed, wanda ake kira da 30, Nasiru Maikano, Aminu Abita, da Ahmed Rufa’i Hussaini, mai inkiya Mikiya.”
Da jaridar ta tuntuɓi mataimakin shugaban jam'iyyar ADC na yankin Arewa Maso Yamma, Jafaru Sani, wanda shi ma sunansa yana cikin waɗanda ake neman, ya bayyana mata cewa mafi yawansu sun samu labarin gayyatar da ƴan sandan ke musu a shafukan sada zumunta.
“E, mafi yawanmu mun ga jawabin a shafukan sada zumunta," ya faɗa, inda kuma ya ƙi yin ƙara bayani a kan batun.
A satin da ya gabata ne gwamnatin jihar Kaduna da El-Rufai s**a yi musayar kalamai masu zafi a game da rikicin da ya ɓalle a lokacin wani taron jam'iyyar ADC a Kaduna.
Gwamnatin ta zargi El-Rufai da shirya makircin dagula jihar ta hanyar taƙalo rikici da furta kalaman da za su harzuƙa mutane, inda shi kuma ya musanta aikata hakan.
A wani jawabi da Kwamishinan Tsaro da Harkoki na Cikin Gida, Dakta Sulaiman Shuaibu, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta naɗe hannu ta zuba wa El-Rufai ido ya maido da jihar cikin rikici, rarrabuwar kai, da rashin tsaro ba.