SARAUNIYA

SARAUNIYA SARAUNIYAR JARIDUN HAUSA

SERAP Ta Maka Gwamnatin Tarayya da NCC A Kotu Kan Ƙarin Kuɗin Waya Daga Yasir Kallah Kungiyar SERAP, mai fafutukar yaƙi ...
26/01/2025

SERAP Ta Maka Gwamnatin Tarayya da NCC A Kotu Kan Ƙarin Kuɗin Waya

Daga Yasir Kallah

Kungiyar SERAP, mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta maka gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya, NCC, a kotu kan ƙarin kashi 50 cikin ɗari na cajin waya, saƙon tes, da data a Nijeriya, inda ta yi zargin cewa ƙarin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, da tsarin doka, kuma babu hankali da adalci a ciki.

A kwanakin nan ne hukumar NCC ta amince da ƙarin kuɗin, wanda ya ɗaga cajin minti ɗaya na waya daga ₦11 zuwa ₦16.5, farashin data 1GB daga ₦287.5 zuwa ₦431.25, sannan saƙon tes na SMS daga ₦4 zuwa ₦6.

Ƙarin kuɗin ya jawo ce-ce-ku-ce da s**a mai yawa ga hukumar NCC ɗin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ita ma ƙungiyar SERAP ta ruga kotu domin a dakatar da ƙarin.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/111/2025 wadda ta shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya, SERAP ta koka a kan ƙarin kuɗin ya keta haƙƙin al'umma na ƴancin magana da samun bayanai kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin duniya s**a ƙunsa.

SERAP ɗin ta roƙi kotun da ta bayyana cewa ƙarin kuɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin duniya na ƴancin ɗan'adam, sannan ta dakatar da aiwatar da ƙarin tare da soke shi baki ɗaya.

Boko Haram Ta Hallaka Sojoji 18 da Kwamanda Ɗaya A Borno Daga Yasir Kallah Aƙalla sojoji 19, ciki har da kwamanda ɗaya, ...
26/01/2025

Boko Haram Ta Hallaka Sojoji 18 da Kwamanda Ɗaya A Borno

Daga Yasir Kallah

Aƙalla sojoji 19, ciki har da kwamanda ɗaya, ne s**a rasa ransu a sa'ilin da mayaƙan Boko Haram s**a kai musu farmaki a sansanin sojin da ke Malam-Fatori, ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Malam-Fatori gari ne da ke kan iyakar Nijeriya da Nijar.

Majiyoyi masu tushe sun yi rahoton cewa maharan sun kai wa bataliyar ta 149 farmakin a ranar Juma'a, 24 ga Janairun 2025.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan sun isa sansanin a kan manyan motoci masu bindiga, inda s**a ƙone gine-gine da motocin sojojin a lokacin farmakin.

"Sojoji masu yawa sun samu mummunan rauni yayin da har yanzu ba a ga wasu ba," wata majiya ta bayyana wa gidan talabijin ɗin Channels.

"Kwamandan bataliyar, wanda Laftanal Kanal ne, da wasu manyan hafsoshi guda biyu, ciki har da daraktan lafiyar sansanin, na cikin waɗanda aka kashe a farmakin."

Wannan farmakin ya zo baya ƴan kwanaki kaɗan da ƙungiyar Boko Haram ɗin ta kai mummunan farmaki a kan wani sansanin sojin da ke Damboa, inda ta kashe tarin sojoji da ba a gama tantance yawansu ba.

Kotu Ta Hukunta Budurwa Da Ta Saɓa Alƙawarin Kai Wa Saurayinta Ziyara Wata kotun majistare a Ilesa, jihar Osun, ta umarc...
25/01/2025

Kotu Ta Hukunta Budurwa Da Ta Saɓa Alƙawarin Kai Wa Saurayinta Ziyara

Wata kotun majistare a Ilesa, jihar Osun, ta umarci wata budurwa mai suna Rhoda Audu da ta biya saurayinta mai suna Eru Dupe Naira 150,000 a matsayin diyya sakamakon karɓar Naira 3000 da ta yi a wajensa a matsayin kuɗin motar kai masa ziyara amma daga ƙarshe ta cinye kuɗin tare da saɓa alƙawarin zuwa.

An fara samun saɓanin a lokacin da Eru Dupe ya tura wa Rhoda kuɗin motar, inda ita kuma daga baya ta kashe wayarta tare da ƙin zuwa. Ganin cewa ta damfare shi ne ya ɓata masa rai, inda kai-tsaye ya kai ƙara ofishin ƴan sandan Ayeso, su kuma ƴan sanda ba su yi ƙasa a gwiwa ba s**a je s**a kamo Rhoda sannan s**a gurfanar da ita a kotu.

Yayin gabatar da shari'ar, Eru ya gabatar wa da kotun shaida, ciki har da shaidar tura kuɗin ta waya da kuma saƙonnin WhatsApp tsakanin shi da Rhoda.

A hukuncin da ta yanke, Mai Shari'a Okogun Oludare ta umarci Rhoda da ta biya Eru Naira dubu ukunsa da kuma ƙarin Naira 100,000 ta laifin saɓa yarjejeniya, da kuma ƙarin wata Naira 50,000 a matsayin diyyar sa shi a cikin damuwa.

Kotun ta kuma jaddada cewa ta yanke hukuncin domin ya zama izina ga masu irin wannan halin cin amanar.

– Yasir Kallah

Tsohon Ministan Abuja, Jeremiah Useni, Ya Mutu Daga Yasir Kallah Allah ya yi wa tsohon ministan Birnin Tarayya, Abuja, n...
23/01/2025

Tsohon Ministan Abuja, Jeremiah Useni, Ya Mutu

Daga Yasir Kallah

Allah ya yi wa tsohon ministan Birnin Tarayya, Abuja, na lokacin mulkin Marigayi Janar Sani Abacha, Laftanal Janar Jeremiah Timbut Useni, rasuwa.

A dangane da sanarwar iyalansa, ya rasu a yau Alhamis, 23 ga Janairun 2025, bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang, ma ya fitar da sanarwar mutuwar tsohon ministan ta bakin daraktan yaɗa labaransa, Gyang Bere.

Gwamnan ya bayyana mutuwar Janar Useni a matsayin babban rashi ba ma ga iya iyalansa ba, har ga rundunar sojin Nijeriya, da jihar Filato, da ma ƙasar bakiɗaya.

Za A Koma Rubuta Kowace Jarrabawa A Kan Kwamfuta A Nijeriya – Minista Daga Yasir KallahGwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙu...
23/01/2025

Za A Koma Rubuta Kowace Jarrabawa A Kan Kwamfuta A Nijeriya – Minista

Daga Yasir Kallah

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙudiri aniyar kawo ƙarshen rubuta kowace jarrabawa a kan takarda, inda ta ce za ta sauya zuwa rubutawa a kan na'urar kwamfuta daga shekarar 2027.

Ministan Ilimin ƙasar, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan yayin bikin ƙaddamar da kwamitin kyautata ingancin jarrabawa a Nijeriya, wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.

Alausa ya ce an ɗora wa kwamitin alhakin shawo kan manyan matsalolin da ɓangaren ilimi yake fuskanta a ƙasar, tare da daidaita ayyukan jarrabawa, da kuma tabbatar da gaskiya da inganci.

Ministan ya kuma jaddada ƙoƙarin gwamantin wajen magance satar amsa da ta yi yawa da kuma ƙarfafa ingancin jarrabawar ƙasar baki ɗaya.

A dangane da jawabinsa, magance satar amsa yana buƙatar mataki mai tsauri domin ba ɗalibai ba ne kawai suke aikata laifin satar amsar ba.

Ministan ya ce iyaye ma suna bayar da gudunmawarsu ta hanyar goya wa yaransu baya su yi satar amsar.

Ya kuma ce malaman makaranta, da shugabannin makaranta, da ma masu kula da jarrabawar suna da hannu a cikin yaɗuwar satar amsa a ƙasar.

Zanga-Zangar Unguwar Kurna: Yadda Ɗan Sanda Ya Harbe Salisu Player Daga Isyaku Kabir Rio "Jiya a can Ƙasan Layi faɗa ya ...
29/11/2023

Zanga-Zangar Unguwar Kurna: Yadda Ɗan Sanda Ya Harbe Salisu Player

Daga Isyaku Kabir Rio

"Jiya a can Ƙasan Layi faɗa ya rincaɓe tsakanin wasu yara har aka karya wa mutum biyu a hannu. Ana cikin rikicin ne wani yaro ya mari wata yarinya. Ganin hakan ne ya sanya yayan yarinyar ya ce Wallahi ba za su yarda ba, sai sun ɗau fansa. Shi ne ya je bakin titin Ƴan Doma Motors ya ɗauko ƴan daba domin su zo su ɗaukar wa ƙanwarsa fansa.

"Shi ne cikin daren nan ƴan daban s**a shigo domin ɗaukar wa ƙanwar abokinsu fansar marin da aka yi mata. To a dalilin haka ne aka sanar wa ƴan sanda s**a shigon cikin unguwar s**a kora yaran. To sai yaran s**a fito saman unguwar suna zage-zage, suna barazana ga mutane, suna saka mutane gudu, masu shaguna suna rufewa.

"To a daidai lokacin ne matasan unguwarmu, nan kan gadar gidan mai unguwa waɗanda suke bai wa unguwarmu tsaro s**a yi shiri domin hana waɗannan 'yan Dldaban shigowa cikin unguwar tamu su yi sata ko su ji wa mutane ciwo. A daidai lokacin matasan unguwarmu s**a tanadi duwatsu domin su ba su da makami irin na ƴan daba.

"Can muna tsaye sai muka hango mutane sun taho ana ta gudu. A daidai lokacin ne shi marigayi SALISU PLAYER ya ce min, "RIO ga su nan fa. Mu gudu, ƴan daba ne." Sai na ce masa 'wallahi ba inda za ni. Su zo mu gan su. Cikinsu babu wanda ba mu sani ba.' Ni ma na riƙe dutse a hannuna. Muna tsaye tare da ni akwai Deeni Amana. Shi kuma SALISU PLAYER sai ya gudu. Ashe bai tsira ba daga harbin tsinannen Ɗan Sanda😭😭

"Muna tsaye ayarin ya zo ya same mu. Waɗansu matasa ne da masu manyan kaya a jikinsu suna ihu ɗauke da makamai irin su katako, adda, barandami. Suna tafe suna ɗuɗɗura ashariya. Ganin haka sai su kuma waɗannan matasan masu kula da unguwa s**a sa musu jifa da duwatsun nan suna cewa ƙarya ne. Kawai a take a wurin sai na ji harbin bindiga daga cikin ƴan daban. Ashe wai ƴan sanda ne a cikinsu suna tare.

"Wallahi billahillazi ba mu ankara ba sai gani na yi a gabana an harbi ɗan uwana USMAN IG. Harsashin ya gogi hannunsa ya wuce cinyar SARKI ZILADAINI. Saii ya kara harba bindigar, shi ne ya kashe SALISU PLAYER 😭"

Falana Ya Koka A Kan Hukuncin Shari'ar Kano, Ya Ce Alƙalai Na Hukunta Masu Zaɓe A Kan Kura-Kuran Da INEC Take Yi Fassara...
03/11/2023

Falana Ya Koka A Kan Hukuncin Shari'ar Kano, Ya Ce Alƙalai Na Hukunta Masu Zaɓe A Kan Kura-Kuran Da INEC Take Yi

Fassarawa: Yasir Kallah

Babban lauyan nan mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam na Nijeriya, Femi Falana, SAN, ya koka a kan hukuncin shari'ar kotun sauraren ƙararrakin zaɓen kujerar gwamna ta jihar Kano wadda ta soke nasarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Idan ba a manta ba, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya, INEC, ta bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar gwamna ta jihar Kano da aka kaɗa a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Da yake jawabi a wani shiri na gidan talabijin ɗin Channels, Falana ya ce: "Bai kamata ka hukunta masu zaɓe a kan kura-kuran da INEC ta yi ba. Hakan ne abin da ya faru ba da jimawa ba a Kano, inda aka ce jami'an INEC ba su maka ƙuri'u dubu 65 ba."

Ya ƙara da faɗin cewa: "Muna kira ga alƙalai da su rungumi adalci, adalci na haƙiƙa, ta hanyar da ba za ka iya hukunta masu zaɓe a kan kura-kuran da INEC ta tafka ba."

A dangane da tsari na doka, matuƙar an ƙirga ƙuri'un sannan an bayyana wanda ya samu nasara, "Ba za ka iya ƙalubalantar ingancin takardun zaɓen ba".

"Saboda haka, ina ganin waɗannan ne wuraren da alƙalanmu ya kamata su koma baya su gyara," inji Falana.

Guguwar Juyin Mulki: Tsoro ya sa shugaban ƙasar Ruwanda ya kori manyan sojojin ƙasar A ranar Laraba, Paul Kagame, shugab...
31/08/2023

Guguwar Juyin Mulki: Tsoro ya sa shugaban ƙasar Ruwanda ya kori manyan sojojin ƙasar

A ranar Laraba, Paul Kagame, shugaban ƙasar Ruwanda, ya bayar da umarnin yi wa wasu sojojin ƙasar ritaya. Sojojin da ritayar ta shafa sun ƙunshi janar guda 95 da ƙananan sojoji 930.

Na gaba-gaba a cikin jerin sunayen sojojin shi ne Janar James Kabarebe, tsohon ministan tsaro, kuma tsohon babban hafsan tsaron ƙasar.

An wallafa sunayen sojojin da aka yi wa ritayar a kan sahihin shafin yanar gizon jami'an tsaron ƙasar a ranar Laraba.

Sanarwar ta fito bayan juyin mulkin da aka ƙaddamar a ƙasashen Niger da Gabon.

Kafin a yi masa ritaya, Janar Kabarebe ya kasance mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman a kan tsaro.

Wasu kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun bayyana cewa wasu daga cikin sojojin sun cimma shekarunsu 65 na ritaya yayin da wasunsu kuma aka zarge su a kan aikata wasu laifuka.

Juyin Mulkin Ƙasar Gabon: An tsare hamɓararren shugaban ƙasa a gida Daga Yasir Kallah Wani bidiyo da ba a san taƙamaiman...
30/08/2023

Juyin Mulkin Ƙasar Gabon: An tsare hamɓararren shugaban ƙasa a gida

Daga Yasir Kallah

Wani bidiyo da ba a san taƙamaiman inda aka naɗe shi ba da AFPTV ta fitar a ranar 30 ga watan Agusta, 2023, ya nuna hamɓararren shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo Ondinma, yana kira ga abokansa na kowanne ɓangare a duniya da su tashi hayaniya a kan hamɓarar da gwamnatinsa da sojoji s**a yi. Shugaban ƙasar ya yi kiran yayin da yake tsare a cikin gida.

Wasu sojoji ne s**a bayyana a talabijin ɗin ƙasar inda s**a sanar da juyin mulkin da kuma soke babban zaɓen ƙasar da aka gudanar.

Sanarwar ta ranar Laraba ta fito bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da cewa Ali Bongo Ondinba ya lashe zaɓen kujerar shugaban ƙasar a karo na uku, duk da dai jam'iyyar hamayyar ƙasar ta bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta ƙasar ta tafka babban maguɗi a zaɓen.

Iyalan Bongo, ɗaya daga cikin manyan iyalai masu ƙarfin iko a Afirka, sun kasance suna mulkar ƙasar tun 1967.

Shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa yana tsare a cikin gida, sannan ya yi kiran neman taimako tare da roƙar al'ummar ƙasar da su yi hayaniya a kan lamarin.

A ɓangaren al'ummar ƙasar kuma, an samu rahotannin bidiyo da s**a nuna yadda mutane ke murna a game da juyin mulkin a babban birnin ƙasar, Libreville.

MARIGAYI ALHAJI MUHAMMADU ƊANWAWU FAGGE: TUNAWA DA TSOHON SHUGABAN HUKUMAR WASANNI NA AREWACIN NAJERIYA DA AKA MANTA Dag...
18/07/2023

MARIGAYI ALHAJI MUHAMMADU ƊANWAWU FAGGE: TUNAWA DA TSOHON SHUGABAN HUKUMAR WASANNI NA AREWACIN NAJERIYA DA AKA MANTA

Daga: Jamilu Uba Adamu
Fassarawa: Yasir Kallah

Lokaci mai tsawo da ya shuɗe, kafin a ƙirƙiri sunan Kano Pillars FC a shekarar 1990, sunan tawagar ƙwallon ƙafar Kano na asali shi ne Kano XI.

A wancan lokacin, Kano XI ce tawagar ƙwallon ƙafar da ke wakiltar Yankin Kano a gasar kofin Challenge Cup na ƙasa.

Farfesa Adamu Baikie, a cikin tarihin rayuwarsa da ya rubuta, ya kawo labarin wasan ƙarshe na gasar kofin Challenge Cup ta shekarar 1953 da aka buga tsakanin Kano XI da PAN Bank, inda ya ce:

"Tawagogin Kudu sun mamaye gasar Challenge Cup, sannan tsawon shekaru masu yawa, kofin bai taɓa barin Legas ba.

"Manya-manyan ƴan wasan Najeriya na lokacin sun kasance a Legas inda suke buga wasa a tawagogin jihar kamar Marine, Railways, Police, Pan Bank, da sauran wasu masu yawa.

"Tawagogin Arewa da s**a iya kaiwa zagayen na kusa da na kusa da ƙarshe (Quarter-finals) a wasannin da aka buga a Legas, yawanci ba sa taɓa iya zuwa zagayen na kusa da ƙarshe (Semi-final). Idan sun kuma samu nasarar cimma zagayen, suna matuƙar ɗiban kashinsu a hannu a wasan.

"Ana haka, abin mamaki, sai labari ya sauya a 1953 lokacin da Kano XI ta kai wasan ƙarshe a Legas, inda za ta kafsa da tawagar Pan Bank ta Legas.

"Babu wanda ya bai wa tawagar Kano wata dama ta samun nasara saboda tawagar Pan Bank ɗin tawaga ce da wani sabon banki mai suna Pan Bank da ke kashe wa wasan ƙwallon ƙafa kuɗi ya kafa.

"Wajen da aka buga wasan ƙarshen shi ne filin wasan George the 5th da ke Onikan.

"Ba zato (ana tsaka da wasa), sai tawagar Kano ta jefa ƙwallo cikin ragar abokan hamayya.

"Abin al'ajabi!

"Tawagar Kano ta kuma jefa ƙwallo ta biyu!

"Tawagar Pan Bank ta farke ƙwallo ɗaya. An busa usir ɗin ƙarshe; wasa ya ƙare, inda Kano XI ta samu nasarar lashe kofin Challenge Cup, inda kuma ta rabo shi da Legas a karo na farko a tarihin gasar."

Ƙashin bayan cimma wannan gagarumar nasarar shi ne manajan tawagar Kano XI, Marigayi Alhaji Muhammadu Ɗanwawu, wanda ya kasance sanannen ɗan kasuwar fata.

An ce ya kasance yana matuƙar son wasan ƙwallon ƙafa kuma ya kashe kuɗinsa mai yawa domin ɗaukaka wasan.

An kuma yi rahoton cewa shi kaɗai ya ɗauki nauyin tawagar, ciki har da tafiyar da s**a yi Legas domin fafatawa a cikin gasar.

Sadaukarwarsa da gudunmawar da ya bayar wajen halarta da lashe gasar Challenge Cup ne ya sanya Sarkin Kano na wancan lokacin, Marigayi Alhaji Abdullahi Bayero, ya tarbe shi da sauran tawagar a fardarsa.

Sakamakon babbar gudunmawarsa ga wasannin motsa jiki, Marigayi Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello, ya naɗa shi Shugaban Hukumar Wasannin Motsa Jiki Ta Arewacin Nijeriya na farko.

Alhaji Ɗanwawu ya taka rawa sosai a cikin tarihin cigaban wasannin motsa jiki a jihar Kano da tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba.

Ya kasance mai matuƙar imani a kan tasirin da wasannin motsa jiki suke da shi wajen harhaɗuwar kawunan ƙabilu daban-daban.

Rahotanni kuma sun ce a lokacin da yana raye, gidansa da ke unguwar Fagge ya kasance a kullum cike da mutane ƙabilu mabambanta, yawanci daga Kudancin Nijeriya.

Duk da rawar da ya taka a gaba ɗayan yankin, abin mamaki ne a ce babu sunansa a wasu gine-gine da wurare na wasanni ko kuma wani al'amari domin tunawa da shi a Kano ko kuma wani waje na musamman a Arewacin Najeriya.

An haifi Marigayi Ɗanwawu Fagge a 1920, kuma ya rasu a ranar 23 ga watan Mayu. Har abada, gudunmawarsa, da nasarorinsa, da ƙoƙarinsa wajen ɗora Kano a kan taswirar ƙwallon ƙafa suna nan ba za su gushe ba.

Allah ubangiji ya rahamta masa.

Amin!

NEEHAL KITCHEN UTENSILS AND CATERING SERVICES: Babban Kamfanin Da Ake Yayi Kamfanin Neehal babban kamfani ne mai inganci...
08/07/2023

NEEHAL KITCHEN UTENSILS AND CATERING SERVICES: Babban Kamfanin Da Ake Yayi

Kamfanin Neehal babban kamfani ne mai inganci da nagarta da ke samar da nau'ikan abubuwa na alfarma cikin sauƙi da rahusa. Nau'ikan abubuwan da yake samarwa sun ƙunshi:

- Kayan kicin kamar kwanuka, robobi, tukwane, tangaraye, farantai, flask ɗin ruwa da na abinci, da sauransu.
- Kek da sauran kayan maƙulashe kamar meat pie, samosa, spring roll, da sauransu.
- Kayan ɗaki kamar zannuwan gado, shimfiɗu, labulaye, gado, da sauransu.

Kamfanin NEEHAL a shirye yake gamsar da ku a duk inda kuke a Nijeriya. Ana iya siyan ɗai-ɗai ko sari a cikin farashi mai sauƙi, kuma za a iya kai maka kayan a duk inda kake a Nijeriya.

Adireshi: Kusa da ofishin ƴan-sanda na Tal'udu, jihar Kano.

Lambar waya: Domin tuntuɓar mu, ana iya kiran wannan lambar: 08036666458

Baba Otu: Gwanin Yanka Da Kekketa Ƴan Wasa A Filin Ƙwallon Da Ba Za A Manta Da Shi Ba Wallafawa: Jamilu Uba Adamu Fassar...
11/06/2023

Baba Otu: Gwanin Yanka Da Kekketa Ƴan Wasa A Filin Ƙwallon Da Ba Za A Manta Da Shi Ba

Wallafawa: Jamilu Uba Adamu
Fassarawa: Yasir Kallah

Ƴan Nijeriya da dama sun manta da jerin ƴan wasan ƙwallon ƙafar da s**a taka leda a cikin shekarun 1970s da 1980s, musamman ma matasan wannan ƙarnin, sakamakon rashin tattarawa da taskance tarihin nasarorinsu da bajintarsu a wasan ƙwallon ƙafa.

A wannan ƙaramar maƙalar, na yi niyyar tunowa da wani gawurtacce kuma ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa da ya yi shuhura a tarihin ƙwallon ƙafar Nijeriya da na taso ina jin labarin kwarewarsa da bajintarsa a ƙwallon ƙafa, musamman ma a ɓangaren yanka da kekketa ƴan wasa.

Wannan ɗan wasan ba wani ba ne face Baba Otu Muhammad na tsohuwar tawagar ƙwallon ƙafar Raccah Rovers ta jihar Kano.

A nahiyar Afirka, musamman Nijeriya, yana da matuƙar sauƙi a manta da ƴan wasan ƙwallon ƙafar da s**a bayar da muhimmiyar gudunmawa gurin cigaban wasan har ya cimma inda yake a yanzu.

Akwai su da yawa da s**a ɓace a cikin tarihi, ko kuma ba a ba su karramawar da s**a cancanci a basu. Wasunsu ba a ma tunowa da su yayin da ake tattaunawa a kan gogaggun ƴan wasa ko lambobin da s**a buga sakamakon rashin isasshen rubutaccen tarihi a kansu.

A nahiyar Turai da ma Arewacin Afirka, akwai filayen wasanni masu yawa da wuraren zama waɗanda aka raɗa musu sunayen wasu mashahuran ƴan wasa. Akwai ma gumaka da yawa da aka gina na ƴan wasan da s**a yi bajinta domin adana tarihinsu. Irinsu sun haɗa da Kubala na Barcelona, Alfaredo Di Stefano na Real Madrid, Beckenbeur na Bayern, har zuwa George Best na Man Utd. Dukkansu an karrama su sakamakon nasarar da s**a samu da gudunmawarsu yayin da suke kan ganiyarsu a ƙwallon ƙafa.

Lokaci mai tsawo kafin a kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars FC, akwai wata shahararriyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Kano da ta yi fice a cikin tarihin ƙwallon ƙafar Nijeriya sakamakon salon wasanta mai matuƙar birgiewa da bayar da nishaɗi. Ana kiran tawagar da Raccah Rovers.

Da farko ana kiran Raccah Rovers da Darma United. Su ne tawaga ta biyu daga Arewacin Nijeriya da s**a ci gasar ƙasa (Nigerian League) a shekarar 1978. Bayan nan kuma s**a kai zagayen na kusa da na kusa da ƙarshe (quarter final) a Kofin Zakarun Afirka a 1979, wanda kuma yake daidai da gasar Kofin Zakarun Afirka (CAF).

Wasansu da ya fi shahara shi ne wani wasan sada zumunta da s**a yi da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fluminense FC ta ƙasar Brazil wanda s**a buga a 1978 a Kaduna inda aka ci su da ci biyu da ɗaya (2-1). Shahararren ɗan ƙwallon ƙafa na duniya, Pele, ya buga wasan.

Baba Otu Muhammad ne ya kasance babban ɗan wasan tawagar a wannan lokacin. Gwani ne a iya yanka da wasa da ƙwallo.

Mahaifinsa ɗan ƙaramar hukumar Bebeji ne ta jihar Kano. Kasuwancin goro ne ya kai mahaifinsa ƙasar Ghana, inda kuma ya zauna a can.

A can ƙasar Ghana aka haifi Baba Otu da sauran ƴan uwansa mata guda huɗu. A can kuma ya tashi.

Alhaji Isyaku Muhammad, Babban Daraktan kamfanin Afro International Group of Companies, ne ya gano Baba Otu yayin da yake buga wa tawagar Ghana Academicals a wani wasansu da Nijeriya.

Academicals a lokacin gasa ce tsakanin makarantun sakandare na Nijeriya da na Ghana.

A lokacin Alhaji Isyaku shi ne mai ɗaukar nauyin tawagar Mighty Jets ta Jos. Hakan ya sanya ya ɗauki Baba Otu domin ya koma buga wa Mighty Jets.

Ya kasance a tawagar na tsawon ƴan shekaru. Daga baya, sakamakon wasu rigingimu na cikin gida a tawagar, Alhaji Isyaku ya janye ɗaukar nauyin da yake yi wa Mighty Jets. Hakan ya sanya dole Baba Otu ya fara neman wata tawagar ƙwallon ƙafar da ta fi wannan.

Ana haka sai labari ya isar wa Raccah Rovers. Ba tare da ɓata lokaci ba s**a aika Marigayi Anas Muhammad da Salisu Yaro (jami'in jin daɗi da walwala na Kano Pillars a yanzu) domin su neme shi kan ya zo tawagar. Da s**a same shi bai ƙi ba.

Tawagar a wancan lokacin tana ɗauke da manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa kamar: Iliyasu Yashin, Abdulwahab Haruna, Ado Ebenezer, Mai Yawo, Godwin Bankole, Ayiye Muhd, Grandson Abbas, Abubakar, Abubakar Ba Ka Wasa, Anas Muhammed, Kalalah, Willie Cabis, Hussaini Alibi, Felix Owolabi, Ahmed Dangogo, Akawu Ƙofar Wanbai, da Nazifi Muhammed.

Shuwagabanni da sauran jagororin tawagar sun ƙunshi: Alhaji Ma’arruf, Alhaji Tadada, Alhaji Nasidi Boka, Alhaji Musa Kallah da Alhaji Abdulmumini.

Baba Otu Muhammad na ɗaya daga cikin tawagar Nijeriya a gasar Olympic ɗin da aka buga a Montreal, Kanada a 1976. Ya kuma buga wa tawagar Nijeriya ta Green Eagles a gasar Nation Cup a Ethiopia a 1976 da kuma Ghana a 1978, inda s**a zo na uku a gasar. An zabi Baba Otu a matsayin ɗan wasan gefen dama da ya zarce kowa a 1976.

A yanzu haka akwai wasu ƴan wasan ƙwallon ƙafa a Kano da ake musu laƙabi da sunansa.

LURA: Binciken marubucin ya dogara ga tattaunawa ta waya da mutanen da binciken ya shafa waɗanda suke raye da kuma wasu bayanai a yanar gizo. Yayan marubucin, Marigayi Salahudeen Uba Adamu ya kasance masoyin tsohon ɗan ƙwallon ƙafar.

Jamilu Uba Adamu marubucin wasannin motsa jiki ne mai zaman kansa.
[email protected]

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SARAUNIYA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to SARAUNIYA:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share