AP Hausa

AP Hausa AP Hausa Shafi Na Farko Da Aka Ƙirƙira Domin Wayar Da Kan Al'umma. Muna Bibiyar Rubuce Rubucen

Muna Ɗauke Da Duk Wani Shirye Shiryen Da S**a Shafi Baƙon Mu Na Mako Dama Na GwarzayEn Shikara.

A SIYASAR NIGERIA TA 2023....Wacce kala zakayi, siyasa zakayi ko neman kudin siyasa....
10/01/2022

A SIYASAR NIGERIA TA 2023....

Wacce kala zakayi, siyasa zakayi ko neman kudin siyasa....

Kar ku bi jam'iyya ko addini a zaɓen 2023 - Sarki SanusiKhalifan Tijjaniyya na Najeriya Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bu...
09/01/2022

Kar ku bi jam'iyya ko addini a zaɓen 2023 - Sarki Sanusi

Khalifan Tijjaniyya na Najeriya Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bukaci wadanda s**a cancanci kaɗa ƙuri’a su je su yanki katin zaɓe gabanin babban zaben 2023.

Yana magana ne a wajen taron shekara-shekara na tunawa da ranar haihuwar mazon Allah Annabi Muhammad.

Sanusi ya yi kira ga jama’a idan zaɓen ya zo su zaɓi shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.

“Idan matasanmu s**a samu aikin yi, tattalin arzikin kasar baki daya zai inganta. Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba za mu iya naɗe hannayenmu mu yi watsi da siyasa ba.

“Duk dan Attijaniyya daga shekara 18 zuwa samanamiji ko maceje ka karbi katin zabe. Allah yana umurce ku da ku dogara ga hannun muminai amintattu. Yanzu muna wani lokaci da jama’a ne ke da ikon naɗa shugabanni, ƙuri’arku ita ce ƙarfin ku, kuna da nauyi a kanku’’ inji Sarki Sanusi.

Hausa Online News

Maganin hana daukar ciki ya yi karanci a ZariyaRahotanni sun bayyana cewa, mata masu zaman kansu na kokawa kan rashin sa...
09/01/2022

Maganin hana daukar ciki ya yi karanci a Zariya

Rahotanni sun bayyana cewa, mata masu zaman kansu na kokawa kan rashin samun maganin hana haihuwa na zamani a wasu sassan birnin Zariya, lamarin da ya tilasta wa mata amfani da kwaroron roba na kai tsaye.

Likitan Da Yake Yiwa Mata Maganin Muni A Amurka 1930s.'Micrometer,' wanda kuma aka sani da 'beauty calibrator,' wata na'...
08/01/2022

Likitan Da Yake Yiwa Mata Maganin Muni A Amurka 1930s.

'Micrometer,' wanda kuma aka sani da 'beauty calibrator,' wata na'ura ce da aka tsara a farkon shekarun Alif da Ɗari Tara da Talatin (1930) da babban masanin kyay Max Factor ɗan ƙasar Poland ya ƙera don taimakawa wajen gano wuraren fuskar mace wanda ke buƙatar ingantawa.

Zane na 'Beauty Micrometer' ya kasance ƙaton ƙarfe ne wanda ke auna gefuna na fuskar mace tare da sassauƙaƙƙen sassan ƙarfe waɗanda s**a yi daidai da yanayin fuskar mutum. Akwai yiwuwar a sami gyare-gyare Ɗari Ukuda Ashirin da Biyar (325), a fuskar mace.

Hausa Online News

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UN😭DA DUMI DUMINSU: Gobara Ta Tashi A  Kasuwar Nguru Dake Jihar YobeRahotanni daga ...
08/01/2022

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UN😭

DA DUMI DUMINSU: Gobara Ta Tashi A Kasuwar Nguru Dake Jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yoben Najeriya na cewa gobara ta tashi a babbar kasuwar Nguru da ke jihar.

Waɗanda s**a shaida lamarin sun bayyana wa BBC cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar Asabar.

Sun kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga sashen ƴan takalma da kuma ƴan robobi kuma ta laƙume shaguna ba iyaka.

Tuni dai jami'an kai agaji da kuma na kashe gobara s**a isa wajen domin kashe gobarar.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce tuni jami'an kashe gobara da matasa s**a haɗa hannu inda suke ƙoƙarin kashe gobarar.

Haka kuma ya tabbatar da cewa ƴan sanda da sauran jami'an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro.

~BBC Hausa

INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UNAllah Madaukakin Sarki Ya karbi rayuwar Sheikh Dr Ahmad BUK a yau juma'aDuniyar Hadis...
07/01/2022

INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN

Allah Madaukakin Sarki Ya karbi rayuwar Sheikh Dr Ahmad BUK a yau juma'a

Duniyar Hadisi tayi rashin kwararren Likitan Hadisi wanda akayi ittafakin babu wanda ya kaishi sanin ilmin Hadisi a Malaman Afirka

Marigayi Sheikh Dr Ahmad BUK ya karantar da manyan Malamai ilmin Hadisi a Nigeria da wasu kasashen Afirka

Daga cikin Dalibansa da ya karantar Hadisi akwai marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano, Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo, Sheikh Dr Idris Abdul-aziz Bauchi da sauransu

Hakika anyi mana babban rashi ALLAHU AKBAR!

Yaa Allah Ka jikan bawanKa, Allah Ka yafe masa laifukansa, Allah Ka hada fuskokinmu da nashi a cikin Aljannah

2023: APC ta sulhunta Goje da gwamnan Gombe, Yahaya Kwamitin Shugabacin Jam'iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin...
06/01/2022

2023: APC ta sulhunta Goje da gwamnan Gombe, Yahaya

Kwamitin Shugabacin Jam'iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni ya sulhunta tsakanin Gwamna Muhammad Yahaya na Jihar Gombe da kuma abokin burmin sa na siyasa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Ɗanjuma Goje.

Jami'in Yaɗa Labarai na Buni, Mamman Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

Ya ce Buni, da Shugaban Kwamitin Sulhu na APC, Sanata Abdullahi Adamu da Kashim Shattima, mamba a kwamitin, su su ka jagoranci sulhun.

Sanarwar ta ce wannan shine karon farko da manyan ƴan siyasar na Gombe su ka haɗu tun bayan da rigimar siyasa ta ɓarke tsakanin su a shekarar bara.

Buni, wanda shine kuma Gwamnan Jihar Yobe, ya baiyana jin daɗin sa game da sulhun da a ka yi.

Ya kuma ci alwashin sulhunta duk masu ruwa da tsaki a APC domin ƙarfafa jam'iyar yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023.

Babu Maganar komawa ta APC -- Kwankwaso Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da...
05/01/2022

Babu Maganar komawa ta APC -- Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da wani shiri na barin jam’iyyar sa ta PDP Zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya.

Sanata Kwankwaso ya baiyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon DW da ke Ƙasar Jamus.

DW ya rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a yanzu dai bashi da wata niyya ta barin jam’iyyar PDP Zuwa APC, k**ar yadda a ke ta jita-jitar zai bar jam’iyyar saboda rashin Ylyi da shi da ba a yi a jam’iyyar.

“Maganar sauya sheƙa babu ita a yanzu ɗin nan. Ba na magana da wasu mutane kan cewar kan koma APC” inji Kwankwaso.

Jita-jita ta yi ƙarfi cewa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC kuma zai sulhunta da abokin burminsa a siyasa, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje bayan da gwamnan ya kai masa ziyarar ta'aziyyar rasuwar ƙanin sa, Inuwa Kwankwaso.

Sai dai kuma a makon nan da mu ke ciki, sai gwamnatin Ganduje ta yi wa Kwankwason raddi kan kalaman da ya yi cewa gwamnan bai ci zaɓe ba a shekarar 2019.

Idan za’a iya tunawa an fara raderadi Kwankwaso da Ganduje zasu yi Sulhu ne tun bayan da Gwamna Ganduje ya Kaiwa Sanata Kwankwason Ziyarar ta’aziyyar kaninsa da ya rasu a kwanakin baya.

Bayan shafa ta tsanaki, al'aurar mace na fara kumbura domin nuna shiryawa ko amincewa da sabon sakon da aka aike mata, h...
04/01/2022

Bayan shafa ta tsanaki, al'aurar mace na fara kumbura domin nuna shiryawa ko amincewa da sabon sakon da aka aike mata, hakan na sanya mahaifa ta share hanya yayin da miji da mata ke karasa sauran aikin.

📸 AP Hausa

Korona ta k**a mutum 199 a KadunaHukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce an samu karin mutum 670 da s*...
04/01/2022

Korona ta k**a mutum 199 a Kaduna
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce an samu karin mutum 670 da s**a kamu da cutar korona a faɗin ƙasar.

Daga cikin sabbin wadanda s**a kamu jihar Legas ce ta fi yawan mutane inda ta ke da 277.

Korona ta kuma k**a mutum 199 a Kaduna daga farkon Janairu zuwa ranar Litinin.

A babban birnin Najeriya Abuja mutum 120, sai kwara mai 20 yayin da Abia ke da 14.

A Katsina da Gombe mutum tara tara cutar ta k**a a jihohin, a Bauchi mutum shida

Yawan masu kamuwa da cutar na ƙaruwa a Najeriya, tun ɓullar sabon nau’in cutar korona na Omicron a ƙasar

Nigerian Daily Hausa

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AP Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AP Hausa:

Share