04/09/2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Duk Masu Gidaje Na Zama Da S**a Sauya Amfanin Su Zuwa Wuraren Kasuwanci Ba Tare Da Izini Ba Zasu Biya Tarar Naira miliyan 5 A Abuja
Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta sanya tara ta Naira miliyan 5 kan duk masu gidaje na zama da s**a sauya zuwa wuraren kasuwanci ba tare da izini ba a wasu manyan tituna na Abuja, ciki har da Titin Gana, Titin Gimbiya, Titin Aminu Kano, da Titin Ademola Adetokunbo.
Wannan matakin ya fito ne daga rahoton kwamitin wucin-gadi da Ministan Abuja Nyesom Wike, ya kafa a ranar 8 ga watan Agusta, 2025 domin tantance matsalolin amfani da Gidaje da kuma canjin dalilin bayar da filaye da ake yi ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Kula da Ci gaban Birni, Mukhtar Galadima, ya gano cewa mafi yawan gine-ginen da ke kan titunan Gimbiya a Garki, Gana a Maitama da kuma Ademola Adetokunbo a Wuse II an sauya su zuwa otal-otal, ofisoshi da shaguna ba tare da bin ka’idar Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ba.
Kwamitin ya ba da shawarar cewa a sake ayyana waɗannan gine-ginen zuwa wuraren kasuwanci ta hanyar biyan kuɗaɗen da s**a haɗa da:
-Bakwai da digo biyar na kimar gidajen a matsayin kuɗin canjin sauya amfani.
-Biyan sabbin kuɗaɗen mallakar fili (Statutory Right of Occupancy) bisa sabon nau’in amfani.
-Idan aka gano filin anyi kari ko an haɗe wani wuri da wani wuri ko an raba ba bisa ka’ida ba, za'a biya karin biyu cikin dari na kimar wurin
Kwamitin ya kuma bayyana cewa duk wanda bai bi wannan doka ba za a iya:
-Rufe gine-ginen,
-Rusa gini,
-Ko kuma kwace takardar mallakar fili
Hakazalika, kwamitin ya ba da shawarar cewa a soke tsofaffin takardun mallakar ƙasa sannan a sake fitar da sababbi na shekaru 99 bisa sabon yanayin amfani da ƙasa.
An kuma umarci masu filaye da ba su riga sun gina ba a cikin kwarya birni wato Central Business District da wani yanki da ake kira Phase II Sector Centres su fara gini cikin watanni uku ko kuma su fuskanci kwacewa.
Da yake karɓar rahoton, Ministan