NBC HAUSA News

NBC HAUSA News NBC HAUSA News muna yada labarai cikin harshen hausa

Mazauna ƙauyukan Kaduna sun nuna damuwarsu tare da ankarar da cewa 'yan bindiga da ke tsere wa luguden wutar da ake musu...
11/05/2023

Mazauna ƙauyukan Kaduna sun nuna damuwarsu tare da ankarar da cewa 'yan bindiga da ke tsere wa luguden wutar da ake musu a Zamfara na samun mafaka a dazukan da ke kusa da su.

Garuruwan da ke iyaka tsakanin Zamfara da Kaduna ne s**a fitar da wannan korafi, tare da cewa suna ganin 'yan bindiga na yi musu shawagi.

Mazauna kauyen Damari a karamar hukumar Birnin Gwari sun ce 'yan bindiga na shigar garuruwansu da tsakar rana.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya da ta wallafa labarin, ta kuma rawaito wani Saeed Damari da ke cewa tun ranar Talata 'yan bindiga ke kwarara zuwa cikin dajin Kuduru.

Shugaban kasar Liberia George Weah ya ce Victor Osimhen na Najeriya na iya lashe kyautar Ballon d'or saboda hazakar da y...
11/05/2023

Shugaban kasar Liberia George Weah ya ce Victor Osimhen na Najeriya na iya lashe kyautar Ballon d'or saboda hazakar da ya nuna wajen ɗaga kofin Seria A a Italiya.

Weah a wani sakon ta ya murna da ya aikewa ɗan wasan, ya shawarci Osimhen kan ya ci-gaba da nuna jajircewa wajen cimma burinsa a duniyar tamaula.

Wasu gurɓatattun jami'an tsaro sun faɗa komar ƴan sanda a jihar Edo.An cafke jami'an tsaron ne da laifin yin fashi da ma...
10/05/2023

Wasu gurɓatattun jami'an tsaro sun faɗa komar ƴan sanda a jihar Edo.

An cafke jami'an tsaron ne da laifin yin fashi da makami .

Bayan fashi da makamin sun kuma tatsi makuɗan kuɗaɗe a hannun wani bawan Allah.

Dakarun Rapid Support Forces (RSF) da ke yaƙi da sojojin gwamnatin Sudan sun zargi sojojin da ƙaddamar da hari ta sama k...
10/05/2023

Dakarun Rapid Support Forces (RSF) da ke yaƙi da sojojin gwamnatin Sudan sun zargi sojojin da ƙaddamar da hari ta sama kan tsohuwar fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum, babban birnin ƙasar.

Mazauna birnin sun ce sun ji ƙarar bama-bamai a yankin, to amma sojojin sun musanta zargin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita zamansa a birnin landan na birtaniya zuwa mako daya domin duba lafiyar ha...
10/05/2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita zamansa a birnin landan na birtaniya zuwa mako daya domin duba lafiyar hakoransa, mai magana da yawunsa Femi Adesina ne ya bayyana hakan.

Shugaba buhari dai ya halarci bikin nadin sarkin ingila Charles III.

Turkiyya ta amince da sauya wa ofishin jakadancinta da ke Sudan matsuguni daga birnin Kahrtoum zuwa Port Sudan, bayan da...
06/05/2023

Turkiyya ta amince da sauya wa ofishin jakadancinta da ke Sudan matsuguni daga birnin Kahrtoum zuwa Port Sudan, bayan da aka harbi motar jakandanta da bindiga.

Yau shekara Goma sha uku (13) da rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya Umaru Musa ’Yar Adua.
05/05/2023

Yau shekara Goma sha uku (13) da rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya Umaru Musa ’Yar Adua.

Kotu a kasar birtaniya ta yankewa sanata ekweramadu hukuncin daurin shekara Tara a magark**a.Kazalika, kotun ta ɗaure ma...
05/05/2023

Kotu a kasar birtaniya ta yankewa sanata ekweramadu hukuncin daurin shekara Tara a magark**a.

Kazalika, kotun ta ɗaure matarsa Beatrice da kuma Dr Obeta.

Jakadan sudan a Najeriya Muhammad Yusuf ya roki ’yan Najeriya dalibai da su dawo kasar idan kura ta lafa.
05/05/2023

Jakadan sudan a Najeriya Muhammad Yusuf ya roki ’yan Najeriya dalibai da su dawo kasar idan kura ta lafa.

'Yan sanda a jihar Kano sun sanar da k**a matashin nan da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano.A wani sako da kakakin ...
05/05/2023

'Yan sanda a jihar Kano sun sanar da k**a matashin nan da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano.

A wani sako da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an k**a matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu'ammali da ƙwayoyi masu sa maye.

A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.

Rasha ta zargi Ukraine da yunƙurin hallaka shugabanta Vladimir Putin bayan da ta harbo wasu jirage biyu marasa matuƙa da...
03/05/2023

Rasha ta zargi Ukraine da yunƙurin hallaka shugabanta Vladimir Putin bayan da ta harbo wasu jirage biyu marasa matuƙa da s**a riƙa shawagi a Moscow cikin daren jiya.

Bidiyon da ba a tantance ba, da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna wani abu na shawagi a sararin samaniyar fadar gwamnatin ƙasar kafin ya tarwatse.

Ukraine ta ce babu abin da zai sa ta kai hari da jirgi maras matuƙi.

Mai magana da yawun shugaban Ukraine ya ce a yanzu abin da ke gaban Ukraine shi ne ƙwato yankunanta da ke hannun dakarun Rasha.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai ya ce duk mutumin da zai iya riƙe mata huɗu da 'ya'ya 28 k**ar shi, zai iya ne...
03/05/2023

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai ya ce duk mutumin da zai iya riƙe mata huɗu da 'ya'ya 28 k**ar shi, zai iya neman shugabancin majalisar wakilai zango na goma.

Alhassan Ado Doguwa ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba lokacin da a ƙa'idance yake sanar da aniyarsa ta neman kujerar mutum na huɗu mafi girman muƙami a Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito wata sanarwa daga shugaban masu rinjayen wadda a ciki yake mayar da martani gamasu cewa ba shi da ƙwarewa da kuma taushin halin da zai iya maye gurbin shugaban majalisa na yanzu saboda irin halayyarsa.

Address

Kano
700104

Telephone

+2349013133163

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NBC HAUSA News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to NBC HAUSA News:

Share