
21/08/2025
INEC ta mika takardar shaidar nasara ga ƴan majalisun da aka zaɓe a zaɓen cike gurbi
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta ƙasa a ranar Alhamis ta bada takardar shaida ga zaɓabɓun ƴan takarar da s**a lashe zaɓe a zaɓen cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar a faɗin jihohi 12.
Daga cikin waɗanda s**a je hedikwatar domin karbar takardun shaidar lashe zabe akwai zaɓaɓɓen Sanatan Edo ta tsakiya da na Anambra da zaɓaɓɓen ɗan majalisar tarayya na Ovia.