Arewa Pulse

Arewa Pulse Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Pulse, News & Media Website, 311 Zoo Road, Kano.
(6)

An samar da shafin Arewa Pulse tun shekarar 2011, An kaddamar da ita a shekarar 2019 ta fara aiki tun wancan lokacin A karkashin Jagorancin Shugabaninta ta inda take kawo abubuwan da suke faruwa a Arewa Dama Duniya baki daya 08109934185.

Haske Ya Girgiza Adamawa Yayin Da Yake Cigaba Da Zagaye A Fadin JaharDan siyasar nan mai tasowa kuma jigo a jam’iyyar AP...
11/05/2026

Haske Ya Girgiza Adamawa Yayin Da Yake Cigaba Da Zagaye A Fadin Jahar

Dan siyasar nan mai tasowa kuma jigo a jam’iyyar APC, Haske, ya kara daukar hankalin al’ummar Jahar Adamawa bayan fara rangadin ganawa da jama’a a fadin kananan hukumomin jihar.

A yau Litinin ne aka fara wannan zagaye inda aka tsara ziyartar kananan hukumomin Toungo, Ganye, Jada da Mayo-Belwa domin tattaunawa da jama’a tare da jin koken su da kuma bayyana manufofin cigaban da ake da su ga jihar.

Tun bayan bayyana jadawalin wannan “Engagement Tour” ne mutane da dama s**a fara bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin wannan yunkuri alama ce ta kusanci da jama’a da kuma kokarin hada kan al’ummar Adamawa.

Masu bibiyar harkokin siyasa a jihar sun bayyana cewa yadda jama’a ke nuna goyon baya ga Haske na kara fito da irin farin jinin da yake samu musamman tsakanin matasa da masu ruwa da tsaki a siyasance.

Jadawalin ya nuna cewa bayan kammala zagayen ranar Litinin, za a ci gaba da kai ziyara zuwa wasu kananan hukumomi daban-daban daga ranar Talata har zuwa Juma’a, domin tabbatar da cewa an kai ga al’umma a kowane yanki na jihar.

Wasu daga cikin magoya bayan sa sun bayyana wannan zagaye a matsayin wata dama ta kara dankon zumunci tsakanin shugabanni da talakawa, tare da nuna cewa irin wannan mataki yana kara karfafa siyasar APC a Adamawa.

Da Yuwuwar Gwamna Umaru Fintiri Ya Ayyana Abdulrahman Bashir Haske A Matsayin Magajinsa A 2027Ana ci gaba da samun bayan...
07/05/2026

Da Yuwuwar Gwamna Umaru Fintiri Ya Ayyana Abdulrahman Bashir Haske A Matsayin Magajinsa A 2027

Ana ci gaba da samun bayanai daga majiyoyi daban-daban da ke nuna cewa, akwai yiwuwar Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri zai bayyana sunan Abdulrahman Bashir Haske a matsayin wanda yake so ya gaje shi a takarar gwamnan jihar a zaben shekarar 2027.

Rahotanni daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar siyasar jihar sun nuna cewa, ana gudanar da tattaunawa mai zurfi tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyya domin ganin an cimma matsaya ta hadin kai kafin fara yakin neman zabe.

Masu bibiyar siyasar Adamawa na ganin cewa Abdulrahman Bashir Haske na kara samun karbuwa a tsakanin matasa, masu sana’o’i da kuma wasu manyan masu fada a ji a jihar. Hakan ne yasa ake ganin sunansa ya fara fitowa sosai a matsayin wanda zai iya daukar tutar jam’iyya a zaben da ke tafe.

Wasu na kallon wannan mataki a matsayin salon siyasar “consensus” wato tsarin da shugabannin jam’iyya ke zama su amince kan mutum guda domin kaucewa rikici da rabuwar kai tsakanin ‘yan takara. Wannan tsari dai ya saba bayyana a manyan jam’iyyun Najeriya musamman idan lokacin zabe ya karato.

Duk da cewa har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga bakin gwamnan ko shugabannin jam’iyya, amma masu sharhi kan siyasa na cewa alamomi na nuna akwai yiwuwar a bayyana Abdulrahman Bashir Haske a matsayin zabin da ake so ya jagoranci tafiyar siyasar jihar a nan gaba.

Haka kuma, wasu magoya bayan siyasa a Adamawa sun fara bayyana wannan labari a matsayin wani sabon babi da zai iya sauya yanayin siyasar jihar, musamman ganin yadda ake cewa ana neman matashi mai hangen nesa, ilimi da kuma kusanci da al’umma.

Idan har wannan batu ya tabbata, hakan na iya zama daya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da za su dauki hankalin jama’a a Arewa maso Gabas gabanin babban zaben shekarar 2027.

Sai dai masana siyasa na gargadin cewa har yanzu lokaci bai yi ba na yanke hukunci kai tsaye, domin siyasar Najeriya na da sauye-sauye masu zuwa cikin kankanin lokaci. Duk da haka, maganar Abdulrahman Bashir Haske na ci gaba da yawo a bakin jama’a tare da jawo muhawara a fagen siyasar Adamawa.

Arewa Pulse Report

YADDA ƘUNGIYAR MAGA HASKE TA TATTARO DIMBIN MATASA A YOLA DOMIN GOYON BAYAN ANIYAR ABDULRAHMAN BASHIR HASKE TA TAKARAR G...
27/04/2026

YADDA ƘUNGIYAR MAGA HASKE TA TATTARO DIMBIN MATASA A YOLA DOMIN GOYON BAYAN ANIYAR ABDULRAHMAN BASHIR HASKE TA TAKARAR GWAMNA 2027

A wani gagarumin taro da ya cika da dimbin jama’a, an ga Ƙungiyar MAGA HASKE ta fito da cikakken ƙarfi a Farfajiyar taro na Mahmudu Ribadu Square da ke Yola, yayin da Alhaji Abdulrahman Bashir Haske ke bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Adamawa a zaɓen 2027.

Taron ya ja hankalin matasa daga sassa daban-daban na jihar Adamawa, inda aka ga taruwar jama’a mai yawan gaske da ke nuna ƙwarin gwiwa da goyon baya ga burin siyasar Haske. Ƙungiyar MAGA HASKE ta taka muhimmiyar rawa wajen tattaro dimbin matasa, tare da nuna tsari da haɗin kai a lokacin taron.

Dandalin taron ya cika makil tun kafin fara jawabai, inda aka shaida yanayi na murna da farin ciki daga mahalarta. Fitowar matasa daga yankuna daban-daban ta ƙara wa taron armashi da ɗaukar hankali, lamarin da ya nuna irin tasirin da wannan sanarwa ta yi a fadin jihar.

A jawabinsa, Alhaji Abdulrahman Bashir Haske ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a 2027, inda ya jaddada kudirinsa na kawo sauyi mai ma’ana da inganta rayuwar al’umma idan aka ba shi dama.

An gudanar da taron cikin tsari mai kyau da lumana, ba tare da wata matsala ba, kuma an kammala shi lafiya cikin kwanciyar hankali—abin da ke nuna ingantaccen shiri da haɗin kai tsakanin masu shirya taron da mahalarta.

A ƙarshe, taron ya bar babban sako na haɗin kai da kuzari daga matasa, wanda ke nuna karuwar sha’awar siyasa da kuma sabon salo na shiga harkokin shugabanci a Jihar Adamawa.

Arewa Pulse Report

Anga Abun Al’ajabi a Jahar Adamawa; Abdulrahman Bashir Haske Ya Bayyana Aniyarsa ta Tsayawa Takarar Gwamnan Adamawa a 20...
26/04/2026

Anga Abun Al’ajabi a Jahar Adamawa; Abdulrahman Bashir Haske Ya Bayyana Aniyarsa ta Tsayawa Takarar Gwamnan Adamawa a 2027

An shaida wani babban tarihi mai ɗaukar hankali a jihar Adamawa State bayan da Alhaji Abdulrahman Bashir Haske ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a shekarar 2027. Wannan sanarwa ta zo ne a wani katafaren taro da aka gudanar a Mahmudu Ribadu Square, inda dubbannin jama’a daga sassa daban-daban na jihar s**a halarta domin nuna goyon baya.

Taron ya ja hankalin jama’a da dama, inda aka ga mutane na tururuwa suna ci gaba da shigowa wajen tun kafin fara taron. Rahotanni daga mahalarta taron sun nuna cewa an samu cunkoso da tarin jama’a daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar, lamarin da ya sanya wajen taron ya cika maƙil da masu goyon baya.

Alhaji Abdulrahman Bashir Haske, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin matasan da s**a yi fice wajen ayyukan ci gaban al’umma, ya bayyana cewa burinsa shi ne kawo sauyi mai ma’ana ga jihar tare da samar da ci gaba a fannoni daban-daban kamar ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar matasa.

Mutane da dama da s**a halarci taron sun bayyana cewa ba su taba ganin irin wannan taro ba a tarihin Adamawa State. Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa irin yadda jama’a s**a fito domin nuna kauna da goyon baya ga Alhaji Abdulrahman Bashir Haske ya nuna irin farin jinin da yake da shi a zukatan al’umma.

Masu sharhi kan harkokin siyasa a jihar na ganin cewa wannan mataki na bayyana aniya zai iya sauya yanayin siyasar jihar nan gaba, musamman ganin yadda matasa da kungiyoyi daban-daban s**a nuna cikakken goyon baya ga wannan yunkuri.

A yayin da ake ci gaba da tunkarar shekarar zaɓen 2027, wannan babban taro ya zama abin magana a faɗin jihar, inda mutane da dama ke bayyana shi a matsayin wani sabon babi a siyasar Adamawa State.

Arewa Pulse Report

26/04/2026

Kungiyar Mamuda Charas Sun Kayata wajen taron Alhaji Abdulrahman Bashir Haske da aka gudanar 25 ga watan Afrilu 2026

26/04/2026

Haske Zai Tsaya Takarar Gwamna: Cikakken Bayanin yadda taro ya wakana a Farfajiyar taro na Mahmudu Ribadu Square

Manufarmu Ita Ce APC Ta Yi Nasara a Adamawa 2027 Daga Sama Har Ƙasa Cewar Alhaji Abdulrahman Bashir Haske Daukar nauyi: ...
24/04/2026

Manufarmu Ita Ce APC Ta Yi Nasara a Adamawa 2027 Daga Sama Har Ƙasa Cewar Alhaji Abdulrahman Bashir Haske

Daukar nauyi: AB HASKE MAGA

Dan takarar gwamna, Alhaji Abdulrahman Bashir Haske, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ƙarfafa jam’iyyar APC a dukkan fadin Jihar Adamawa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Haske ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai ofishin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Adamawa, inda ya je domin taya shi murna tare da nuna goyon bayansa ga shugabancin jam’iyyar.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Haske ya ce dole ne jam’iyyar ta kasance cikin haɗin kai da tsari idan tana son samun nasara a zaɓuka masu zuwa. A cewarsa, manufar ba wai kawai samun kujeru ba ce, har ila yau ana son gina ƙaƙƙarfan tsarin siyasa da zai yi aiki “daga sama har ƙasa” wato daga manyan shugabanni har zuwa mambobin jam’iyya a matakin ƙasa.

Ya bayyana cewa dole ne mambobin APC su yi aiki tare kamar iyali guda, ba tare da la’akari da bambance-bambance ba, domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta ƙara ƙarfi a kowace unguwa, ƙaramar hukuma, da al’umma a fadin Jihar Adamawa.

Haske ya kuma yaba da kokarin Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, inda ya bayyana shugabancinsa a matsayin mai muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban jam’iyyar a Adamawa.

Ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa zai ci gaba da bada gudummawa da goyon baya ga duk wani shiri da zai ƙarfafa haɗin kai, aminci, da cigaban APC a jihar.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin wannan ziyara a matsayin wani bangare na ci gaba da tuntubar jiga-jigan jam’iyya da Haske ke yi gabanin zaɓen gwamna na shekarar 2027. Sakon da ya bayar ya fi karkata ne kan haɗin kai, shiri, da ƙarfafa jam’iyya domin fuskantar makomar siyasa a jihar.

Ziyarar ta ƙare ne da tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa tsarin jam’iyyar tare da ƙarfafa mambobi su ci gaba da mayar da hankali kan makomar APC a Jihar Adamawa.

Arewa Pulse Report

Cece-kuce ya kare; Abdulrahman Haske Zai Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Adamawa A Ranar 25 ga Afrilu Abdulr...
23/04/2026

Cece-kuce ya kare; Abdulrahman Haske Zai Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Adamawa A Ranar 25 ga Afrilu

Abdulrahman Haske ya kammala dukkan shirye-shiryen da s**a dace domin bayyana aniyarsa ta shiga takarar kujerar gwamnan Jihar Adamawa a zaɓen da ke tafe, a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Wannan mataki na zuwa ne a wani lokaci da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a faɗin jihar, yayin da masu ruwa da tsaki da magoya baya ke ci gaba da bibiyar masu neman shugabanci.

A cewar bayanan da aka samu, an shirya gudanar da babban taron bayyana wannan aniya ne a ranar 25 ga watan Afrilu, a dandalin Mahmud Ribadu Square da ke birnin Yola, babban birnin Jihar Adamawa. Ana sa ran taron zai zama ɗaya daga cikin manyan tarukan siyasa da za su ja hankalin jama’a daga sassa daban-daban na jihar.

Kungiyar MAGA dake karkashin Alhaji Abdulrahman Haske, ta bayyana cewa ana sa ran dubban mutane za su halarci wannan taro, inda ake hasashen kimanin magoya baya 100,000 za su taru domin nuna goyon baya ga wannan takara. taron zai haɗa da shugabannin jam’iyyar APC daga matakai daban-daban, manyan jiga-jigan siyasa, abokan hulɗa, ƙungiyoyin matasa da mata, da kuma sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi da al’ummomin jihar baki ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa ana gudanar da shirye-shirye masu faɗi domin tabbatar da cewa taron ya gudana cikin tsari da nasara, tare da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa mahalarta damar bayyana ra’ayoyinsu da goyon bayansu. Ana kuma kallon wannan taro a matsayin wani muhimmin mataki da zai iya nuna ƙarfin siyasar Abdulrahman Haske da yadda yake da farin jini a tsakanin jama’ar Adamawa.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa bayyana wannan takara na iya ƙara ɗaukar hankalin jama’a, musamman a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar shugabanci da ci gaban jihar. Haka kuma, ana sa ran wannan taro zai zama wata dama ta haɗa magoya baya da kuma bayyana manufofi da hangen nesa ga makomar Adamawa.

Arewa Pulse Report

Dubbannin Jama’a Sun Tarbi Abdulrahman Bashir Haske a Filin Jirgin Sama Gabanin APC Congress a Adamawa A wani gagarumin ...
19/04/2026

Dubbannin Jama’a Sun Tarbi Abdulrahman Bashir Haske a Filin Jirgin Sama Gabanin APC Congress a Adamawa

A wani gagarumin yanayi na nuna karfin siyasa da hadin kan magoya baya, dubbannin jama’a daga kungiyoyi daban-daban sun tarbi Alhaji Abdulrahman Bashir Haske a filin jirgin sama yayin da ya isa Jihar Adamawa domin halartar taron APC Congress. Tun kafin isowarsa, filin jirgin da hanyoyin da ke kewaye da shi sun cika da matasa, mata, da sauran magoya baya dauke da alluna da taken goyon baya, lamarin da ya nuna irin karbuwar da yake da ita a tsakanin al’umma.

Daga cikin manyan mutanen da s**a halarci wajen akwai Hajara Iya Aliyu tare da tawagarta, wadda ta kara armashi da daraja ga tarbar. Haka kuma Masud Ibrahim, Ahmad Gangnai, Mu'azzam Ibrahim canji, Hon. Auwal Bello, Muhammad Bako link man, zakiru barade da Ali Ishaku (Protocol) sun kasance cikin wadanda s**a halarci wajen, inda s**a hada kai da sauran magoya baya wajen nuna cikakken goyon baya.

Bayan isowarsa, an tarbi Haske da murna da tafiye-tafiye na rakiyar tawagarsa daga filin jirgin, yayin da jama’a s**a cika hanyoyi domin ganin sa. Wannan gagarumin tarba ya zama wata alama ta karuwar farin jini da tasirin siyasar sa a jihar.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa irin wannan taro na jama’a na nuni da karfin da Haske ke da shi gabanin taron APC Congress, wanda ake sa ran zai kasance muhimmin mataki a tsarin siyasar jam’iyyar a jihar. Haske ya nuna godiyarsa ga magoya bayan, tare da jaddada kudurinsa na ganin an samu hadin kai da cigaban Jihar Adamawa.

Wannan lamari ya kara daukar hankali tare da kafa sabon salo na yadda ake tunkarar muhimman tarukan siyasa a jihar, inda jama’a ke ci gaba da bayyana goyon bayansu ga zababbun ‘yan takara.

Sponsored MAGA HASKE MEDIA TEAM

AREWA PULSE REPORT

Duk Inda Fintiri Yake, Akwai Adalci Cewar Alhaji Abdulrahman Bashir HaskeDan takarar gwamna a Jihar Adamawa, Alhaji Abdu...
19/04/2026

Duk Inda Fintiri Yake, Akwai Adalci Cewar Alhaji Abdulrahman Bashir Haske

Dan takarar gwamna a Jihar Adamawa, Alhaji Abdulrahman Bashir Haske, ya bayyana cewa duk inda Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranta, ana samun adalci da gaskiya, yana mai jaddada cewa salon shugabancin sa yana tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.

Haske ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan saukarsa daga filin jirgin sama, yayin da yake kan hanyarsa ta halartar taron Progress na jam’iyyar APC da za a gudanar a jihar. A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar APC, musamman batun rikice-rikicen cikin gida, ya nuna cewa akwai bukatar shugabanci nagari domin tabbatar da hadin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya.

Ya yabawa Gwamna Fintiri bisa kokarin da yake yi na toshe duk wata baraka da ke kokarin tasowa a cikin harkokin siyasa, yana mai cewa irin wannan jagoranci ne ke tabbatar da dorewar zaman lafiya da cigaban al’umma.

A cewarsa, dole ne ‘yan siyasa su fifita bukatun jama’a a kan muradun kansu, yana mai kara da cewa ci gaba mai dorewa ba zai samu ba sai an gina shi a kan adalci, gaskiya da mutunta juna.

Haske ya kuma jaddada kudirinsa na bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban siyasar Jihar Adamawa, inda ya ce burinsa shi ne ganin an samu ci gaba mai dorewa tare da shugabanci nagari da kula da walwalar jama’a.

Sponsored by MAGA HASKE MEDIA TEAM

Arewa Pulse Report

Why the People of Adamawa Are Rallying Behind Abdulrahman Bashir Haske In Adamawa State, support for Abdulrahman Bashir ...
16/04/2026

Why the People of Adamawa Are Rallying Behind Abdulrahman Bashir Haske

In Adamawa State, support for Abdulrahman Bashir Haske continues to grow as many residents link their backing to what they describe as his consistent contributions to the state’s development.

Supporters say their loyalty is also a form of appreciation for his past efforts in supporting communities and investing in initiatives that promote growth and opportunity. His decision to bring his business interests and investments into Adamawa is widely seen as a rare commitment among political aspirants.

Many believe no other candidate has shown the same level of personal involvement in developing the state. For them, Haske represents not just a political choice, but a reflection of gratitude and trust in his continued vision for Adamawa’s progress.

Signed
AB HASKE MAGA MEDIA TEAM

Address

311 Zoo Road
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Pulse posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Pulse:

Share