12/09/2022
ZAMAN KOTUN YAU (LITININ) TSAKANIN GWAMNATIN TARAYYA DA ƘUNGIYAR ASUU.
A yau Litinin ne kotun ɗa'ar Ma'aikata, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a, Justice Polycarf Hamman, ta fara sauraron ƙarar da Gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa (ASUU) a gaban ta, tana neman kotun ta tilastawa Malaman komawa bakin Ayyukan su (a yayin da ake cigaba da sauraron shari'ar), tare da buƙatar kotun ta tantance mata ko Yajin Aikin da ASUU ɗin take gudanarwa halastacce ne a idon doka ?, da sauran buƙatu.
Sai dai Jim kaɗan da fara sauraron shari'ar ne , sai ƙungiyar SERAP ta bayyana sha'awar ta ta kasance wa a cikin shari'ar, ta bakin lauyan da ke wakiltar ƙungiyar, Ebun-Olu Adegnoruwa (SAN), yana mai cewar su ma ƙungiyar su ta shigar da ƙara makamanciyar wannan a gaban kotun, inda take buƙatar kotun ta tilastawa Gwamnatin tarayya cika yarjejeniyar da s**a cimma da ƙungiyar ta ASUU, tun a shekarar 2009.
Inda yace SERAP tana buƙatar shiga cikin shari'ar ne domin sauƙaƙawa Kotun sauraron shari'a iri daban-daban, da s**a shafi lamari guda.
Sai dai kuma, Lauyan Gwamnatin tarayya, Tijjani Gazali (SAN), ya soki buƙatar ta SERAP na shiga shari'ar, yana mai bayyana cewar bai kamata waɗanda sunayen su basa daga cikin ƙunshin shari'a, a hange su a cikin shari'ar tsundum ba.
A nasa ɓangaren, fitaccen Lauyan nan, Femi Falana (SAN), da ke wakiltar ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa (ASUU), roƙar kotun ya yi da ta ɗage shari'ar zuwa wata rana, domin basu damar gabatarwa da kotun ƙunshin bayanan su, inda shi ma lauyan Gwamnati bai yi s**a ba, ya buƙaci kotun da ta ɗage shari'ar.
Inda anan ne kuma, kotun ta bayyana matsayarta na ƙin amincewa da buƙatar SERAP na shiga cikin Shari'ar, tare da ɗage shari'ar zuwa ranar Juma'a 16 ga watan Satumbar da muke ciki, domin fara gabatarwa da kotun bayanai daga kowanne ɓangare.
✍️Miftahu Ahmad Panda