
26/07/2025
KIRA GA GWAMNATI: TALAKA NA BUKATAR TALLAFI MAI MA'ANA!
Duk da saukin farashin abinci da ake ta yayatawa, talaka har yanzu bai ji sauki ba._ Manomanmu na kokarin siyar da kayan gona, amma kudin da suke samu bai kai ga sayen takin noma ba. Farashin kayan masaruf da bukatun rayuwa na nan a sama—rayuwa tana ƙara wahala.
Malamai sun yi kira ga gwamnati da ta, Saukaka farashin kayan abinci da masarufi bada tallafin manoma da rage haraji da kuma duba batun kasuwaci ta hanyar daidaita farshin Kaya.
Wannan matsala ba ta talaka kadai ba ce—ta shafi rayuwar al’umma gaba ɗaya. Muna bukatar shiri mai dorewa da zai saukaka rayuwa a karkara da birane.
Muna roƙon gwamnati da hukumomi masu ruwa da tsaki da su duba wannan batu da idon rahama- Inji Manoma
—Abbas Saad Buhari