27/12/2023
By Abubakar Danbaba
Akwai wani lokachi wajen 2010 Ghali Umar Na Abba yazo har gida ya gaida Sheikh Sharif Sani Janbulo Shida Alh Jamilu Ali Salga sai bayan sun gama tattaunawa sai yace da Sharif yana neman wata alfarma sai Sharif yace ta menene ya fada, sai yace yanaso a wannan satin ranar juma'a kazo da tawagarka gidana dake sharada ayi zikirin juma'a a can bayan munyi sallar magariba ka fada mana Annabi S.A.W nida iyalaina sharif yace ba matsala zamuzo insha Allah bayan munje munyi zikirin juma'a da magariba, Sharif ya fara fadar girman Annabi S.A.W wallahi yanayin da ghali ya shiga a wannan lokachin na tabbatar ba karamin so yakewa Annabi ba. Bayan antashi s**a shiga cikin falonsa tare da Sharif ina cikin wadanda s**a shiga falon da wasu daga yan"uwa. Waye zai iya tuna abunda ghali ya fada sanda muka shiga falonsa?
Allah yajikan Alhaji Ghali Umar Na Abba kasadashi da masoyinsa Annabi Muhammad S.A.W