Jaridar Arewa

Jaridar Arewa Labarai da Dumi-duminsu

Tsohon shugaban AMAC a Abuja ya ayyana kudurinsa na neman takarar gwamnan Anambra a zaɓen 2025 karƙashin inuwar APC - Du...
08/01/2025

Tsohon shugaban AMAC a Abuja ya ayyana kudurinsa na neman takarar gwamnan Anambra a zaɓen 2025 karƙashin inuwar APC - Duba ƙarin bayani a sashen sharhi.

Hoto: Charles Chikwuma Soludo, Prince Nicholas Ukachukwu/Facebook

09/07/2023

Allah yabamu damuna me Albarka

Ina aka kwana batun mayar da tsaffin kudade da aka sabunta bankuna?Ina mafita a mahangar ku?
24/01/2023

Ina aka kwana batun mayar da tsaffin kudade da aka sabunta bankuna?
Ina mafita a mahangar ku?

Comrade Yaji Wuta
03/06/2022

Comrade Yaji Wuta

24/05/2022

Kisan Fatima da Yaranta 4 Zaluncine ,Yan Arewa na bukatar abimata Hakkinta

Yanzu Yanzu Senator Malam Ibrahim Shekarau Yabayyana Ficewarsa Daga APC zuwa NNPP
16/05/2022

Yanzu Yanzu Senator Malam Ibrahim Shekarau Yabayyana Ficewarsa Daga APC zuwa NNPP

Yanzu yanxu...An hangi Kwankwaso a fadar Sardaunan Kano dake Mundubawa
15/05/2022

Yanzu yanxu...
An hangi Kwankwaso a fadar Sardaunan Kano dake Mundubawa

08/05/2022
07/05/2022

Gwaman Kano Abdullahi Ganduje Ya chanjawa Rukunin gidajen "Jaba" Suna Zuwa "NEW ENUGU CITY"

07/05/2022

AA ZAURA TV

KIRA GA AL'UMMA

Assamu Alaikum,

Anjawo Hankalina Kan wasu al'umma Dake amfani da Sunana suna Cutar da Mutane ta hanyar siyar musu da form din koyon sana'a ko Wani Abu da yadanganci Haka.

BABU Wani form da zai fito daga wajena ko gidauniyata ta AA ZAURA Foundation da Za a Siya ko abiya kudi kafin a sameshi, bugu da Kari, Domin mu kaucewa irin wannan muguwar al'ada yasa mukaimaida tsare tsaren mu na tallafi ta hanyar yanar gizo Kamar yadda Mukayi na tallafin karo Karatu Wanda yanzu haka ake aikin tantancewa Kuma za a fara biya Nan Bada jimawaba da yaddar ALLAH.

Saboda haka daga yau, duk Wanda yazo muku da Wani form da sunan AA Zaura ko Gidauniyata to a mikashi ga Hukuma don yin Binchike.

Kuma idan akwai Wani Abu Mai kamada haka, Za a sanar ta kafafenmu da yaddar Allah.

Nagode.

07/05/2022

Shekarau ya sansanta da Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya sansanta da Gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Ganduje, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta gano.

Idan za a iya tuna wa, APC ta dare gida biyu a Kano tun bayan zaɓen shugabannin jam'iya na jiha, inda Shekarau ya jagoranci ɓangare ɗaya, ya kuma tsayar da Amadu Haruna Zago a matsayin shugaban jami'ya, shi kuma Abdullahi Abbas, a matsayin shugaban jam'iyar na tsagin Ganduje.

Haka a ka ci gaba da tafiya har ta kai ga ɓangarorin sun dangana ga kotun ƙoli, inda yanzu a ke jira ta yanke hukunci.

Sai dai kuma a bisa bayanan da wannan jarida ta samu, tuni dai Shekarau ya zagaye ya sasanta da Ganduje, kuma har yanki fom ɗin sake tsaya wa takarar Sanata, bayan an daddale da shi cewa za a dawo masa da takarar sa

Wannan jaridar ta jiyo cewa Shekarau da Ganduje sun raba dare a ranar Litinin, har zuwa awannin farko na Talata su na wata ganawar sirri domin sulhunta wa, inda daga ƙarshe dai a ka yarda cewa Shekarau zai koma kujerarsa ta Sanata.

Haka zalika an jiyo cewa sansanta war ta biyo bayan kiran da Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi na cewa a sansata da duk wani tsohon Gwamna da ke Majalisar Dattawa a kuma sake bashi takara a 2023.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa a yau Juma'a ne kuma Shekarau da Ganduje za su rankaya zuwa Abuja domin gana wa da Shugaban na APC na Ƙasa domin sake ƙarfafa sulhun da a ka yi tsakanin shugabannin biyu.

Tuni dai wannan lamari ya harziƙa magoya bayan G-7, har ya haifar da cecekuce, musamman tsakanin ɓangaren Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin da kuma na Shekarau ɗin.

Sai dai kuma Kakakin Shekarau, Sule Ya'u Sule, ya musanta batun cewa tsohon gwamnan ya bar ɓangaren G-7.

Ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa har yanzu Shekarau shi ne shugaban G-7, inda ya ƙara da cewa har yanzu ɓangaren na tafiya tare kuma duk wani mataki a na ɗauka ne tare.

Sule ya ƙara da cewa fom ɗin da Shekarau ya siya ba wai yana nufin ya bar ɓangaren bane.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Arewa:

Share