01/10/2025
Yau Najeriya take cika shekaru 65 da samun âyancin kai.
Wannan rana tana tuna mana tarihin Ćasa, ĆoĆarin da aka yi don kafa Ćasa mai Éorewa, da kuma muhimmancin haÉin kai tsakanin alâumma.
Tun kafin mulkin mallaka, Musulmai daga yankin da yanzu ake kira Najeriya suna zuwa Hajji, kodayake hanyoyin sun bambanta sosai. A farko, ana bi ta Ćasa ko teku, tafiyar tana Éaukar watanni, kuma mutane suna fuskantar Ćalubale iri-iri. Amma daga farkon Ćarni na 20, an fara samun tsarin tafiye-tafiye daga West Africa zuwa Hejaz, inda hukumomi da sarakuna s**a tabbatar da tsari da kiyaye lafiya. Misali, sarakuna k**ar Emir Muhammadu Dikko na Katsina sun yi Hajji cikin tsari na zamani a shekarar 1921, abin da ya nuna cewa Nijeriya ta fara haÉuwa da tsarin tafiya mai tsari.
Bayan samun âyancin kai, Najeriya ta kafa hukumomi irin su NAHCON da hukumomin jihohi domin tsara Aikin Hajji, kula da lafiyar maniyyata, da samar da tsarin da ya dace da zamani. Wannan ya sauĆaĆa abubuwa ga mutane, ya tabbatar da tsari da aminci, kuma ya ba da damar mutane daga sassa daban-daban na Ćasa su haÉu su yi wannan ibada cikin tsarki da ladabi.
Aikin Hajji a Najeriya ba wai tafiya zuwa kasa kawai bane; yana koya mana darasin haÉin kai, tsari, tawaliâu, da kishin addini. Duk shekara, Musulmai daga duk fadin Najeriya suna haÉuwa, suna barin bambancin kabilanci da arziki, suna tafiya a hanya Éaya zuwa wurin Allah, suna gudanar da ibada cikin tsari da ladabi. Wannan tafiya tana nuna cewa idan aka haÉa kai da tsari mai kyau, za a samu albarka da nasara, abu ne da kowace Ćasa ke bukata domin tafiya a sahun ci gaba.
Yayin da Najeriya ke cika shekaru 65, ya dace mu yi koyi da wannan: kowa ya taka rawar da ya dace, a yi aiki da gaskiya da tawaliâu, kuma a tabbatar da haÉin kai domin alâumma su ci gaba da wanzuwa cikin albarka, zaman lafiya, da tsarki. Kamar yadda tafiyar Hajji ke koyar da mu, tsari mai kyau da niyya mai tsarki suna jagorantar nasara ga kowa da kowa.
Allah ka gyara mana Ćasarmu ka amintar da ita.
Allah ka gyara mana shuwagabannin muđ