
20/07/2025
YANZU YANZU: Da Alama Har yanzu akwai Soyayyar Buhari a Zukatan Talakawan Nigeria, Wani Matashi ya shafe kwana uku yana tattaki daga Bauchi zuwa Daura don ta'aziyyar rasuwar Buhari, ya koka kan rashin ganin iyalan Marigayin.
Matashin wanda ya share kwanaki uku yana tattaki daga Bauchi zuwa Daura, domin ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce har yanzu bai samu damar ganin iyalan Marigayin ba, domin yi masu ta'aziyyar rasuwarsa.
Ya ce tuni dai ya samu damar yi wa babban aminin Buharin Mamman Daura ta'aziyya, saidai ya ce har yanzu bai samu damar ganin iyalan Marigayin ba su Yusuf, don yi masu ta'aziyyar duk da cewa ya kwashe kwana biyu a garin Daura ɗin.
Me zaku ce?
Daga Usman Umar Katsina
Kana Son Duba Sahihan Labarai Shigo Jaridar 👉 Wakiliya 👈 Yanzu Yi Following Karku Bari Komai Ya Wuceku...