23/07/2025
Mu ba ma son Adeleke ya dawo jam'iyyar mu domin ƙajaga zai zame mana - APC
Biyo bayan hukuncin Gwamna Ademola Adeleke na ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar PDP bayan makonni da dama na rade-radin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, jam’iyyar ta APC, reshen jihar Osun ta bayyana cewa ta ƙi karɓarsa saboda gazawarsa a mulki, wanda ya mai da shi ƙajaga ga jam’iyyar.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC, Kola Olabisi, ya fitar a yau Laraba, Shugaban jam’iyyar, Tajudeen Lawal, ya bayyana cewa sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa wata ba wani abu bane, amma sun ƙi karɓar Adeleke saboda tarin matsalolin da ke tattare da shi, wanda ke iya jawo wa jam’iyyar matsala.
“Ba ma son Gwamna Ademola Adeleke ya shigo APC ne saboda ana masa kallon wanda w zai shigo da ɓarna, wanda da zai lalata mutuncin jam’iyyar APC.”
Jam’iyyar ta ƙara da cewa PDP ta zama kamar gidan kutare da manyan ƴan siyasa masu nagarta ke barin sa.
Sai dai PDP, a cikin martaninta, ta bayyana cewa jam’iyyar nan cike take da ƙarfi kuma tana da goyon bayan al’umma a jihar.