Bakin Alkalami news

Bakin Alkalami news BAKIN ALKALAMI NEWS
Gidan jaridar yanar gizo mai yaɗa sahihan labarai kan siyasa, ilimi, al'amuran al'umma da ci gaban ƙasa. GASKIYA DA GASKIYA

“IN KASAN MUNA GANIN MUTUNCINKA, TO KA JA MUTUNCINKA” — COMRD. MUSA SURAJO ME SHARA’AH FAGGEƊan gwagwarmaya Comrd. Musa ...
16/09/2026

“IN KASAN MUNA GANIN MUTUNCINKA, TO KA JA MUTUNCINKA” — COMRD. MUSA SURAJO ME SHARA’AH FAGGE

Ɗan gwagwarmaya Comrd. Musa Surajo Me Shara’ah Fagge ya bayyana cewa ba ya hana kowa tallata wanda yake so, amma ya ce ba zai amince da tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gabansa ba.

A cewarsa:

“In kasan muna ganin mutuncinka to ka ja mutuncinka. Bamu hana ka yi tallar wanda kake so ba, amma akan Tinubu muddin zaka kawo mana tallarshi wallahi zan iya yin gaba da kai har abada. Domin kai maƙiyin al’umma ne. Dan haka mun fada: TINUBU MUST GO.”

Cewar ɗan gwagwarmaya Comrd. MUSA SURAJO ME SHARA’AH FAGGE.

BAN ONLINE — GASKIYA DA GASKIYA

Ƙungiyar Daliban Najeriya ta Ƙasa reshen Ƙaramar Hukumar Fagge (NAF’S) ta kai ziyara ga Ɗan Majalisar Tarayya mai wakilt...
09/09/2026

Ƙungiyar Daliban Najeriya ta Ƙasa reshen Ƙaramar Hukumar Fagge (NAF’S) ta kai ziyara ga Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. M.B. Shehu Fagge.

A yayin ziyarar, ƙungiyar ta gabatar da buƙatu da dama da s**a shafi inganta harkar ilimi a Ƙaramar Hukumar Fagge, ciki har da gyaran wasu makarantu da ke buƙatar kulawa.

Haka kuma, ƙungiyar ta nemi a samar da rijiyar burtsatse/bohol na ruwan sha a makarantar Madorawa, domin samar wa ɗalibai da makarantar ruwa.

A nasa ɓangaren, Hon. M.B. Shehu Fagge ya yi alkawarin cewa, in Sha Allah, za a fara aikin cikin satin da za a shiga, tare da fatan kammala shi zuwa ƙarshen wata.

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

MATASHIN ƊAN SIYASA COMRD. HALIFA SPEAKER YA BAYYANA FICEWARSA DAGA JAM’IYYAR APCMatashin ɗan siyasa ɗan asalin Ƙaramar ...
28/08/2026

MATASHIN ƊAN SIYASA COMRD. HALIFA SPEAKER YA BAYYANA FICEWARSA DAGA JAM’IYYAR APC

Matashin ɗan siyasa ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Fagge, Comrd. Halifa Speaker, ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar APC.

Sanarwar ta zo ne jim kaɗan bayan ganawarsa da Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar PDP, Ambassador Muhammad Bello Dalhat.

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

COMRD. ALI GARBA LAWAN YA BAYYANA RA'AYINSA KAN NEMAN HADIN KAI GA MATASAƊan gwagwarmaya Comrd. Ali Garba Lawan, ɗan Jam...
26/08/2026

COMRD. ALI GARBA LAWAN YA BAYYANA RA'AYINSA KAN NEMAN HADIN KAI GA MATASA

Ɗan gwagwarmaya Comrd. Ali Garba Lawan, ɗan Jam’iyyar NDC, ya bayyana cewa ya kamata a haɗa kai wajen neman wanda zai kawo wa matasa offer ko jari, domin su samu damar dogaro da kansu.

Ya ce:
“Ajawone kawai zaice Da kabashi offer ko Jari, kwara kabashi machine na 700k.”

Cewar Comrd. Ali Garba Lawan, ɗan Jam’iyyar NDC.

🔷 BAN ONLINE — GASKIYA DA GASKIYA

RANA TA 3: HON. M.B. SHEHU FAGGE YA CI GABA DA EMPOWERMENT GA ‘YAN GWAGWARMAYA NA FAGGEA ci gaba da shirin tallafawa al’...
25/08/2026

RANA TA 3: HON. M.B. SHEHU FAGGE YA CI GABA DA EMPOWERMENT GA ‘YAN GWAGWARMAYA NA FAGGE

A ci gaba da shirin tallafawa al’umma, Hon. M.B. Shehu Fagge, Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Fagge, ya ci gaba da rabon kayan tallafi ga ‘yan gwagwarmaya na Ƙaramar Hukumar Fagge.

A wannan rana ta uku, an raba kayayyakin dogaro da kai da s**a haɗa da babura, firji, kekunan ɗinki da sauran kayan tallafi, domin taimaka wa waɗanda s**a amfana su samu abin dogaro da kansu.

Wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa matasa da sauran ‘yan gwagwarmaya wajen samun sana’a da inganta rayuwarsu.

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

JAM’IYYAR NDC TA SANAR DAHON. NASIRU SULE GARO A MATSAYINƊAN TAKARAR SANATAN KANO TA AREWABAN ONLINE🔷 GASKIYA DA GASKIYA...
21/08/2026

JAM’IYYAR NDC TA SANAR DA
HON. NASIRU SULE GARO A MATSAYIN
ƊAN TAKARAR SANATAN KANO TA AREWA

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

📝 ZABABBEN ƊAN MAJALISAR TARAYYA HON. MUHAMMAD BELLO SHEHU FAGGE YA GWANGWAJE MASALLACIN JUMA’A NA SABON BIRNI DA SABON ...
21/08/2026

📝 ZABABBEN ƊAN MAJALISAR TARAYYA HON. MUHAMMAD BELLO SHEHU FAGGE YA GWANGWAJE MASALLACIN JUMA’A NA SABON BIRNI DA SABON CARPET

Zababben Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Muhammad Bello Shehu Fagge, ya tallafa wa Masallacin Juma’a da ke Sabon Birni da sabon carpet domin ƙara samar da yanayi mai kyau, tsafta da nutsuwa wajen gudanar da ibada.

Wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin Hon. Muhammad Bello Shehu Fagge na taimaka wa al’umma da wuraren ibada domin inganta rayuwar jama’a.

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

HON. M.B. SHEHU FAGGE ZAI CI GABA DA SAKAWA ’YAN GWAGWARMAYA DA ABIN ALƘAIRIƊan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar H...
20/08/2026

HON. M.B. SHEHU FAGGE ZAI CI GABA DA SAKAWA ’YAN GWAGWARMAYA DA ABIN ALƘAIRI

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. M.B. Shehu Fagge, ya bayyana cewa zai ci gaba da tallafa wa ’yan gwagwarmaya na Ƙaramar Hukumar Fagge da abin alheri, daga yanzu har bayan zaɓe.

A cewarsa, wannan tallafi zai ci gaba da kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin taimaka wa ’yan gwagwarmaya domin su samu damar dogaro da kansu da inganta rayuwarsu.

“ya kara dacewa Isha Allah duk Wanda ya biyomu bazai hofinta ba indai yayi hakuri kowa sai ya amfana.”
— Cewar Hon. M.B. Shehu Fagge

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

📰 YAU AKA FARA KAMFEN NEMAN ZAƁEN SHUGABAN ƘASA NA 2027A yau, Laraba 19 ga Agusta 2026, aka fara wa'adin kamfen ɗin nema...
19/08/2026

📰 YAU AKA FARA KAMFEN NEMAN ZAƁEN SHUGABAN ƘASA NA 2027

A yau, Laraba 19 ga Agusta 2026, aka fara wa'adin kamfen ɗin neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Ƙasa na shekarar 2027, bisa jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.

A cewar jadawalin INEC, zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Ƙasa zai gudana ne a ranar 16 ga Janairu 2027.

Daga yau, jam'iyyu da 'yan takara za su iya fara gudanar da kamfen na jama'a bisa tanadin dokar zaɓe.

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

📰 ADELEKE YA LASHE ZAƁEN GWAMNAN OSUNGwamna Ademola Adeleke ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, inda ya samu nasarar koma...
16/08/2026

📰 ADELEKE YA LASHE ZAƁEN GWAMNAN OSUN

Gwamna Ademola Adeleke ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, inda ya samu nasarar komawa kan kujerar gwamna domin ci gaba da mulki a wa’adi na biyu.

Nasarar ta zo ne bayan kammala zaɓen da kuma bayyana sakamakon da hukumar zaɓe ta sanar.

A wannan nasara, Adeleke zai ci gaba da jagorantar gwamnatin Jihar Osun na wa’adin mulki na biyu.

BAN ONLINE
🔷 GASKIYA DA GASKIYA

Address

Kwachiri, Fagge
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bakin Alkalami news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share