Indaranka

Indaranka Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Indaranka, Media/News Company, NO. 525 yan awaki Road apposite move on print, Kano.
(3)

Jaridar ‎Inda Ranka na nufin zama babbar kafar yada labarai, wadda ke samun amincewar jama'a ta hanyar isar da sahihan labarai, kuna iya turo mana da labaran da kuke so mu wallafa muku muddin dai bai saɓa da ƙa'ida ba da hoto, bidiyo ta watsap 09039665766

02/10/2026

“Babban abin da zai dawo wa Najeriya kimarta tare da walwalar ’yan ƙasa, shi ne kwaikwayon kyawawan halaye da ayyukan shugabannin da s**a gabata. Domin kuwa, wasu shugabannin wannan zamani sun mayar da gwamnati wata hanya ta azurta kansu.”

— Farfesa Kamilu Sani Fagge

Ammasco Radio 90.7 FM

01/10/2026

Prime Minister Kasar Portugal Luis Montenegro ya kira waya da kansa domin kin bahasin meya faru akan Cristiano Ronaldo.

Me zaku ce?

🇳🇬 SHEKARU 66 DA ƳANCIN KAN NAJERIYAA ranar 1 ga watan Oktoba, Shekara 1960, Najeriya ta samu ƴancin kai daga turawan mu...
30/09/2026

🇳🇬 SHEKARU 66 DA ƳANCIN KAN NAJERIYA

A ranar 1 ga watan Oktoba, Shekara 1960, Najeriya ta samu ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya, inda aka fara sabon babi a tarihin ƙasar.

Shekaru 66 bayan haka, tarihin Najeriya ya ƙunshi nasarori masu yawa, lokutan ƙalubale, juriya da kuma ayyukan da har yanzu ba a kammala ba.

Mun ga bunƙasar birane, yaɗuwar ilimi, ci gaban harkokin kasuwanci, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire, tare da gagarumar gudummawar ƴan Najeriya a fannoni daban-daban a duniya.

Amma a gefe guda, akwai wasu manyan ƙalubale da ƴan Najeriya ke fuskanta a kullum, ciki har da talauci, rashin tsaro, rashin aikin yi, rashin daidaito, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma tsadar rayuwa.

Saboda haka, ƴancin kai ba ranar biki ba ce kawai. Wani nauyi ne na ci gaba da gina ƙasar da za ta bai wa kowane ɗan Najeriya damar samun ingantaccen ilimi da lafiya, samun abin dogaro da kai, da rayuwa cikin mutunci da kwanciyar hankali.

Yayin da muke bikin wannan rana, mu tuna da inda muka fito, mu fahimci inda muke a yau, sannan mu ci gaba da tunanin irin Najeriya da muke son bar wa waɗanda za su zo bayanmu.

Barka da Ranar Ƴancin Kan Najeriya. 🇳🇬

Address

NO. 525 Yan Awaki Road Apposite Move On Print
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Indaranka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Indaranka:

Shortcuts

Share