Adamu Rabiu Adam

Adamu Rabiu Adam Knowledge in youth is wisdom in age..........

18/04/2026
MINTI BIYAR.....A cikin minti biyar kacal za ka iya maimaita SUBHANA LLAHl WA BIHAMDIHI SUBHANA LLAHIL AZEEM 100.INSHA A...
18/04/2026

MINTI BIYAR.....

A cikin minti biyar kacal za ka iya maimaita SUBHANA LLAHl WA BIHAMDIHI SUBHANA LLAHIL AZEEM 100.

INSHA ALLAH ZA KA SAMU:
✓. Gafarar zunubai ko da sun kai kunfan teku ne.
✓. Qarin tattalin arzikin lada a wajen Allah.
✓. Samun dashen bishiyar Dabino guda dari mai saiwar zinare a gidan Aljannah.
✓. Qaruwar hanyoyin arziqi, albarka da natsuwar zuci.

Ɗan'uwa duk fa a cikin minti biyar!!. To me mu ke jira?

Dr. Jameel Muhammad Sadis
HAFIZAHU LLĀH

Allah ya sa mu dace.

18/04/2026

"Wanda Duk Yake Son Ya Karantar A DAARUL HADEETHIS; Ya Zauna Yayi Karatu A DAARUL HADEETHIS, Wataran Zai Iya Zama Shugara A Cikinta, Wataran Zai Iya Zama Malami A Cikinta"

Sheikh Albaniy Zaria Rahimahullah

18/04/2026

Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!
DAARUL HADEETHIS SALAFIYYAH
Zaria - Nigeria
GAGARUMAR
MUHADARA TA MUSAMMAN
Ana gayyatar Maza da Mata zuwa wannan muhimmin taro na ilimi da za a gabatar kamar haka:
Wuri: Daarul Hadeethis Salafiyya, Zaria- Nigeria
Malami Mai Gabatarwa:
Prof. Muhammad Sani Umar(Rijiyar-Lemo OON Hafizahullah)
Rana: Lahadi 12/4/2026
Lokaci: 10:00 na safe

18/04/2026

"Kun gan mu a DAARUL HADEETHIS SALAFIYYAH ɗin nan; watarana za ku ji mun gayyato
-Bishop na wusasa, ba abinda ya shafe mu, watarana za kaji mun gayyato
-Shehin Ɗariqar Tijjaniyyah, za kaji watarana mun gayyato
-Shehin Ɗariqar Qadiriyya, watarana zakaji mun gayyato
-Shugaban Izala, watarana zakaji mun gayyato
-Jundullahi, watarana zakaji
-Ahbabullahi duka zamu gayyato su, ba abinda ya shafe mu.
Ba ya nuna mun zama SU, baya nuna su sun zama MU!

Amma abinda ake cewa shine kar kirjinka yayi kunci, kace kawai sai ɗan ƙungiyar ka kawai zaka saurara, kayi kuskure!

Ka bude kirjinka ka saurari kowa, amma fa in ruɗaɗɗe ne kai, to kuma wannan kam ka tsaya ga abinda bazai ruɗa ka ba!!"

Albani Zaria Rahimahullah

Address

Atiku Abubakar Road
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Adamu Rabiu Adam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Adamu Rabiu Adam:

Shortcuts

Share