03/05/2025
Manajan Daraktan Bankin Masana’antun "Bank of Industry" (BOI), Dr. Olasupo Olusi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai dangane da shirin da aka gudanar a ranar Juma’a a jihar Kano.
Wakilinsa, Aminu Yusuf, wanda shi ne Manajan BOI na yanki Kano, ya bayyana cewa Jihar Kano kadai ta samu mutane 51,033 da s**a ci gajiyar shirin, inda aka raba musu fiye da Naira biliyan 12.54.
Ya ce an ware Naira biliyan 50 daga cikin kudaden tallafin domin taimakawa masu kananan sana’o’i guda miliyan daya, ciki har da Mata ‘yan kasuwa, masu gyaran tayoyi (Vulcanisers), masu sayar da abinci, masu sana'ar ɗinki (Teloli) da sauransu, da tallafin Naira 50,000 ga kowannensu cikin kananan hukumomi 774 a fadin Najeriya.
Olusi ya bayyana cewa wannan rabon kudaden wani bangare ne na Naira biliyan 200 da gwamnatin Bola Tinubu ta ware a matsayin tallafin Gwamnatin Tarayya don farfado da kananan masana’antu da kuma bunkasa bangaren kera kayayyaki a Najeriya.
Ya bayyana cewa shirin yana bayar da lamunin har zuwa Naira miliyan 5 da kaso 9 cikin dari na riba cikin shekara ɗaya, tare da wa’adin biyan kudin cikin shekaru uku ba tare da bukatar jinginan komai ba.
Haka kuma, ya jaddada cewa har yanzu akwai Naira biliyan 75 a karkashin shirin tallafawa Masana’antun "Manufacturing Sector Fund" (MSF), wanda aka ware domin magance matsalolin da masana’antun Najeriya ke fuskanta, k**ar hauhawar farashin kayayyaki, gibin ababen more rayuwa da kuma cikas a tsarin samar da kayayyaki.
A nasa bangaren, Bashir Jafa, Manajan hukumar raya kananan da matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN) reshen Jihar Kano, ya ce hukumar na ci gaba da wayar da kan ‘yan kasuwa yadda za su amfana da tallafin da kuma lamunin.
NAN