09/10/2025
YAKI YAZO KARSHE ALHAMDULILLAH🙏
Mayakan kungiyar H@ma$ na Fa|@$dinawa tare da Gwamnatin |$ra'i|a sun sanya hannu akan yarjejeniyar kawo karshen yaki na tsawon shekaru biyu da aka shafe ana gwabzawa
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya tabbatar da wannan labarin a cikin daren da ya gabata
Kungiyar Ham@$ zata sako duka ¥ahudawan da tayi garkuwa da su a harin 7 October 2023, sannan ita kuma |$ra'|a zata janye Sojojinta daga wasu muhimman gurare da ta yiwa kawanya a zirin Gaza
Donald Trump yace wannan shine matakin farko na yunkurin kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya, kuma ya tabbatar da cewa za'a yiwa kowani bangare tsantsar adalci
A karshe Donald Trump ya gode wa Kasashen Qatar, Egypt da Turkiyyah bisa shiga tsakanin Ham@$ da |$ra'i|a har aka samu sulhu da fahimtar juna domin a kawo karshen yaki da zubar da jini
A nata bangaren, kungiyar Ham@$ ta fitar da sanarwa akan an cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki bisa sharadin Sojojin |$ra'i|a zasu fice daga zirin Gaza tare da barin kayan agaji su shigo cikin Gaza da musayen fursunonin yaki
Sannan Ham@$ ta jinjina wa Gwamnatin Qatar, Egypt, Turkiyyah da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump bisa gudunmawa da s**a bayar domin a kawo karshen wannan yakin
A karshe Ham@$ tayi jinjina da yabo wa mutanenta da duk wadanda s**a nuna alhini akan abinda ya faru da su
Darasin da da zamu dauka
1- Babu wani karfi da ya zarce na Allah, |$ra'i|a da Amurka ance sun fi kowace Kasa a duniya karfin makami, sai gashi sun gagara samun na$ara akan mutanen da basu da 'yan ci, basu da wani taimako imba na Allah ba
2- Duk wanda ya tsayu akan hanyar Allah sai yayi nasara akan abokan gaba ko da ya cutu, cutarwan mai karewa ne, a karshe kuma zai yi nasara akan abokan gaba
3- Musulmi ya zama mai hakuri da juriya, ayi tanadi don su (abokan gaba) kamar yadda Allah Ya fada mana a cikin Al-Qur'ani Maigirma
Muna rokon Allah Ya tabbatar mana da zaman lafiya a duniya gaba daya