
21/08/2025
Wane irin tallafi gwamnati da al’umma za su iya bayarwa domin ganin matasanmu sun yi fice a irin wannan fage na duniya?
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi bakuncin gwani Sanusi Bukhari Idris, wanda ya zama na uku a gasar Musabaqar Qur’ani ta duniya da aka gudanar a Masarautar Saudiyya.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa gwamna Yusuf ya taya matashin ɗan asalin Kano murnar samun wannan matsayi mai daraja a rukunin Qirā’āt da Tafsiri.
Sanarwar ta ce, wannan nasara ba kawai alfahari ce ga Sanusi Bukhari da iyalansa ba, har ila yau babban farin ciki ne ga Kano, Najeriya da al’ummar Musulmi gaba ɗaya.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa wannan gagarumar nasara ta sake ɗaga martabar jihar da ƙasar Najeriya a idon duniya, tare da tabbatar da kyakkyawan tarihi da Kano ke da shi wajen ilimin Qur’ani.
A ƙarshe, gwamnatin ta yi addu’ar Allah ya ci gaba da bai wa matashin ilimi mai amfani, ya kare shi kuma ya ɗaukaka matsayin sa wajen hidima ga addinin Musulunci da al’ummar Kano, musamman matasa.