06/05/2025
LABARI MAI ƊAUKE DA DARASI
Ya yi aure, kuma a daren farko na auren (daren farko na zama da matar), sai ya gano cewa ba budurwa bace.
A ranar farko ya shiga cikin tashin hankali, ita kuwa tana kuka tana roƙonsa da roƙon Allah Maɗaukaki da ya yafe mata, k**ar yadda ya riga ya shirya ta kafin a ɗaura auren.
Tana kuka sosai tana roƙonsa ya ji tausayinta, ya rufa mata asiri. Ta rantse masa cewa ta tuba domin Allah, ba domin mutane ba. Kuma tana cikin ƙunci, sai dai ta samu nutsuwa ne lokacin da ta k**a hanya ta gaskiya da addini.
Saboda yawan kukanta da roƙonta, sai ya ce mata:
“Zan bar ki tare da ni tsawon watanni 7, sai daga baya na kirkiro wata ‘ƙaramar matsala’ a gidan da za ta kai mu ga saki. Amma ki tabbata cewa ba zan taɓa ki ba, ke kuma ba za ki taɓa ni ba. Za mu zauna k**ar abokai ne kawai.”
Wannan ne mafita da ya yanke bayan duk ƙoƙarin da ta yi na riƙonsa.
Ba ya kusantar ta sam. Duk da haka suna fita tare zuwa wuraren cin abinci, kasuwa, har tafiya suna yi. Amma yana kallonta k**ar abokiyar tafiya ne kawai, ba mata ba.
Bayan da watanni 7 s**a wuce, sai lokacin saki ya yi. Ta shirya kanta, tana kuka, hawaye yana zuba k**ar ruwan sama.
Tana jiran ta ji kalmomin nan:
“Na sake ki… Na sake ki… ke sakakka ce.”
Sai ya ce:
“Ba zan sake ki yanzu ba. Mu je wurin da zan kai ki, in isar da ke gidan iyayenki, sai a can in sake ki kafin ki sauka daga mota.”
S**a tafi, ta ɗauki duk kayanta. Amma sai ya tsaya a gaban wani gidan kwalliya.
Ta ce masa: “Meye wannan?”
Ya ce:
“Ina so ki shiga ki yi gyaran jiki da kwalliya k**ar yadda kika kasance a ranar farko da na aure ki.”
Ta ce:
“Ba daidai bane, iyayena zasu tambayeni, kuma me yasa zan yi kwalliya lokacin da zan dawo gida bayan an sake ni?”
Ya ce:
“Wannan shine sharaɗi na. Idan kin ƙi, zan gaya musu dalilin ainihin sakinki.”
Tayi matuƙar jin tsoro, sai ta amince. Ta shiga wurin kwalliya ta gyara kanta k**ar amarya.
Da ta koma mota, sai ya ce mata ta buɗe drawer a cikin mota. Ta buɗe — sai ta ga takardun tafiy