06/05/2026
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Dala Biliyan 3 Don Yin Jirgin Kasa A Kano Da Kaduna Da Legas
Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince da bayar da kwangilar gina manyan ayyukan layin dogo guda uku a biranen Kano da Kaduna da kuma Legas, domin bunkasa tattalin arziki da saukaka zirga-zirga.
Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele ne ya sanar da hakan ga manema labarai a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) da aka gudanar ranar Alhamis.
Ministan ya bayyana cewa an zabo wadannan biranen ne saboda matsayinsu na cibiyoyin kasuwanci da s**a dogara da kansu, inda ya ce zuba jari a cikinsu zai haifar da sakamako mai kyau ga rayuwar talakawa.
Ayyukan da aka amince da su sun hada da:
Birnin Kano: Za a gina layin jirgin kasa na cikin gari (Kano Metro City Rail) wanda zai rika daukar mutane zuwa sassan birnin.
Birnin Kaduna: Za a samar da tsarin jirgin kasa na "Light Rail" (wanda Gwamna Uba Sani ya nuna godiyarsa a kai a safiyar yau).
Birnin Legas: Za a fara aikin layin jirgin kasa na "Green Line" (Phase 1A).
Oyedele ya bayyana cewa wadannan ayyuka guda uku za su ci kimanin dala biliyan 2.99 (kusan Naira tiriliyan hudu da rabi).
Ya kara da cewa za a samar da kudaden ne ta hanyar kamfanin hannun jari na Ma'aikatar Kudin Kasa (MOFI), tare da hadin gwiwar wasu hukumomin bayar da tallafi na musamman.
"Mun sani cewa babu ci gaba ba tare da ingantattun hanyoyi da sufuri ba. Wadannan ayyukan an tsara su ne don bunkasa kasuwanci, saukaka wa ma’aikata da dalibai zirga-zirga, da kuma kyautata rayuwar jama’a a wadannan manyan biranen," in ji Ministan.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani bangare na shirin Shugaba Tinubu na tabbatar da cewa an farfado da bangaren sufuri domin rage tsadar rayuwa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a fadin kasar nan.
Masana tattalin arziki na ganin cewa idan aka kammala wadannan ayyukan, birnin Kano da Kaduna za su zama manyan cibiyoyin sufuri a Arewacin Najeriya, wanda hakan zai rage cinkoson ababen hawa da kuma saukaka jigilar kayan amfanin gona.