22/09/2025
Hotunan yadda tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, CON, ya jagoranci saukar Alqur’ani mai girma tare da musuluntar da maguzawa kimanin 280 a gidansa dake Kano.
Kamar yadda ya saba lokaci zuwa lokaci, Dr. Ganduje kan shirya irin wadannan addu’o’i da saukar Alqur’ani domin yi wa Jihar Kano addu’ada kasa baki daya.
Gidauniyar Ganduje Foundation cibiya ce da ta shafe sama da shekaru talatin (30) tana hidimtawa addinin Musulunci da kuma taimakawa al’umma. A cikin ayyukanta akwai gina masallatan Juma’a, gina makarantun Islamiyya, musuluntar da Maguzawa, da kuma yi wa masu larurar idanu aikin gani kyauta.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da iyalansa sun bada kalma ga Maguzawa tare da mika kyautuka, inda ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin iyalansa sun gaje shi wajen ci gaba da gudanar da irin wannan aikin alkhairi.
Aminu Dahiru
Visual Communication Aide to Dr. Abdullahi Umar Ganduje, CON
22nd September, 2025