Gaskiyar Alkalami

Gaskiyar Alkalami Broadcast and Media Production company
https://youtube.com/?si=HooLL5tYw3yJ3SDp

Barrister Abba Hikima ya samu ganawa da Dan Takarar Shugabancin kasa Alhaji Atiku Abubakar a yau.Kamar yanda aka bayyana...
28/09/2026

Barrister Abba Hikima ya samu ganawa da Dan Takarar Shugabancin kasa Alhaji Atiku Abubakar a yau.

Kamar yanda aka bayyana a shafin sada zumunta na Atiku, haduwar ta su ta faru ne tun lokacin da Abba Hikima ya fara fafutukar gwagwarmayar TMG.

Shin ya ku ke ganin wannan hadin na Abba Hikima da Atiku?

An gama baka ta neman aiki a ma'aikatar cikin gida wacce ta hada:- Civil Defense- Correctional Service- Fire Service- Im...
28/09/2026

An gama baka ta neman aiki a ma'aikatar cikin gida wacce ta hada:

- Civil Defense
- Correctional Service
- Fire Service
- Immigration.

Idan ka sami offer a daya daga cikin wadan nan wana farin ciki za ka yi?

Ya kamata a ci girma a barwa yaya da jikoki.
28/09/2026

Ya kamata a ci girma a barwa yaya da jikoki.

26/09/2026

RANAR TUNA KARYA TA DUNIYA.

Yau ce Ranar Tuna Karya ta Duniya, A Cikin Wadannan Karairayi Guda 10, Wacce tafi baka Haushi ?

1)- Zan Dawo da Farashin Man fetur Naira 45 akan kowace Lita.

2) - Zan Gyaran Matatun Man Nijeriya in kuma gina wasu Sabbi a Cikin shekarar Farko ta Mulkina.

3) - Zan Bayar da Naira 5000 ga Marasa Aiki a Kowane wata

4) - Zan Samar da Ayyukan Yi Miliyan Uku a kowace Shekara.

5) - Zan Kawar da Kungiyar Boko Haram a Cikin Wata Uku

6) - Zan Dawo da darajar Naira daidai da Dollar Amerika

7) - Zan Hana duk wani Jami'in gwamnati fita kasashen Waje don neman Lafiya.

8) - Zan Bada ilimi Kyauta tun daga Firamare har Jami'a a Zamanin Mulki na

9) - Zan dawo da Kamfanin Jirage Na Nigeria Airways

10) - Zan Farfado da kamfanin Sarrafa karafuna na Ajaokuta.

Shin wannene yafi baka haushi?
Haka kuma wannene yafi baka dariya?
Kuma wannene aka cika ?

Daga: Bilkisu Sani

Domin morewa ingantattun labarai ku yi following din page din mu: Gaskiyar Alkalami

INNALILLAHI WA INNA'ILAIHI RAJIUN 😭😭 Wannan wasu daga Cikin mutanen da Allah ya hada zamanmu dasu ne Anan Kasar Libya  S...
26/09/2026

INNALILLAHI WA INNA'ILAIHI RAJIUN 😭😭

Wannan wasu daga Cikin mutanen da Allah ya hada zamanmu dasu ne Anan Kasar Libya S**a taho zuwa gida Shekaran jiya s**a sami matsalar Lalacewar Mota Kishirwa da yunwa tayi Silar Mutuwarsu baki daya kusan su 37
Wannan fa an fita neman yadda za'a rufawa kai asiri ne anje an nemo a hanyar dawowa Gida ne baki daya Allah ya karbi Rayuwarsu.

Ubangiji Allah ka jaddada Rahama a garesu Allah ka yafe musu Laifukansu Gaskiya kam hanyar Libya akwai Kalubale mai tarin yawa Fatanmu Ubangiji Allah ya bamu abinda mukazo nema na Alkhairi ya maidamu gida Cikin iyalinmu Lafiya Ameen ya hayyu ya kayyum

Sheikh Kabiru Gombe tare da iyalansa.Gaskiyar Alkalami
25/09/2026

Sheikh Kabiru Gombe tare da iyalansa.

Gaskiyar Alkalami

DA DUMI-DUMI: Kotu ta soke tikitin takarar Pantami, ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwaniBabbar kotun taray...
24/09/2026

DA DUMI-DUMI: Kotu ta soke tikitin takarar Pantami, ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani

Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Gombe ta umarci Jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani domin tantance ɗan takararta na gwamnan Jihar Gombe.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar tsayar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Garry ya ƙalubalanci tsayar da Pantami bayan PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takara tilo a ranar 26 ga Yuni 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani da ya dace ba.

Pantami, wanda tsohon ɗan takarar APC ne, ya koma PDP ne bayan APC ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na yarjejeniya.

Daga bisani, Pantami ya samu tikitin PDP ta hanyar amincewa da baki yayin zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayu.

Sai dai kotun, a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe.

Credit: Daily Nigerian Hausa

Lallai Shugaban kasar Iran yana kaunar mutanansa.A lokacin da ya halarci taron majalisar din kin duniya na bana, bayan d...
24/09/2026

Lallai Shugaban kasar Iran yana kaunar mutanansa.

A lokacin da ya halarci taron majalisar din kin duniya na bana, bayan da ya mike zai yi bayani sai ya daga hoton marigayi Ayayollah Khamenei, wanda Amurka ta kashe shi a gidansa.

A hannun sa na hagu kuma sai ya daga jakar Yan makaranta wanda sojojin Amurka s**a wullawa bomb a lokacin da yara ke tsaka da karatu.

Wannan shi ake kira da sign language, wato symbolic sign ne, jaka da jini tana representing din yaran da aka kashe a makaranta, hoton kuma Khamenei yana representing na har yanzu supreme leader dinsu yana tare da su a zuciya.

Gaskiyar Alkalami

KARKA SAYI Dangote Refinery shares. Daga: Adamu Yusuf A Shekarar 2007, shekaru 19 kenan, na sayi shares na Dangote Flour...
23/09/2026

KARKA SAYI Dangote Refinery shares.

Daga: Adamu Yusuf

A Shekarar 2007, shekaru 19 kenan, na sayi shares na Dangote Flour Mills da kuɗi ₦150,000. Ina da certificate ɗin shares ɗin, kuma sunana yana kai t gatanan na tura a wannan post din. 📜

Ban taba samun dividend (ribar da ake rabawa masu hannun jari ba), sannan har kawo i yau ban samu uwar kuɗi naba wato (capital) nawa ba. Na yi ƙoƙarin bibiyar lamarin ta hannun stockbroker (dillalin hannun jari), amma ban samu wanda zai taimaka min a kusa ba. Har sai da na je Lagos a shekarar 2019. 🚗✈️

Na kuma je banki sau da dama na cika e-Dividend forms, amma daga ƙarshe sai na lura cewa an cire Dangote Flour Mills daga cikin jerin kamfanonin da ke ciki. 🤦‍♂️

A shekarar 2022, aka fara samun ofisoshin Pension da Stockbrokers a Gombe. Na je wani ofishi, ma’aikacin wurin ya gaya min cewa Dangote Flour Mills ta sayar da kamfanin, sannan aka mayar da kuɗin masu hannun jari zuwa gomnati wato NIPF (National Investment and Protection Fund).

Daga nan akace na je SEC, inda aka ce zan cika e-Mandate form. Na cika shi, amma har zuwa yanzu shiru kakeji. 😔

Saboda wannan ƙwarewar da na samu, ba zan iya ba mutum shawarar ya yi gaggawar sayen shares ba tare da ya fahimci yadda tsarin yake ba. Ka bincika sosai, ka san inda za ka nemi dividend ɗinka da kuma uwar jarinka idan kamfanin ya canza tsari ko ya daina aiki. 📊💰

Yanzu kuma ina son masu ilimin lissafin kuɗi sumin lissafi nawane darajar: ₦150,000 na shekarar 2007, idan aka duba exchange rate da darajar kuɗi a wancan lokacin, kusan nawa ne darajarsa a yau? 🤔💵

Wassalam. 🙏

Senator Abdul'aziz Yari ya gana da Malamai, a inda kuma s**a amimce tare da go yawa tafiyar Tinubu baya a Zango na biyu....
22/09/2026

Senator Abdul'aziz Yari ya gana da Malamai, a inda kuma s**a amimce tare da go yawa tafiyar Tinubu baya a Zango na biyu.

Shin za kubi ra'ayin malamanku na siyasa, ko kuma kuma kuna da naku ra'ayin?

Address

Kano
700231

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiyar Alkalami posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gaskiyar Alkalami:

Shortcuts

Share