05/08/2026
A siyasa, adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya, kuma gaskiya ita ce tubalin amincewar jama'a da kowace jam'iyya. A yau muna kira ga shugabannin jam'iyyar ADC na ƙasa da su tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin tsarin da s**a kafa, domin tarihin jam'iyya yana ginuwa ne a kan gaskiya da adalci, ba son rai ko tasirin wasu ba.
His Excellency Shuaibu Idris Miƙati ya shiga wannan fafatawa bisa ƙa'ida, kuma kwamitin ɗaukaka ƙara (Appeal Committee) da jam'iyyar ta kafa ya tabbatar da sahihancin zaɓen da ya ba shi nasara. Wannan ya ƙara tabbatar da cewa an bi doka da ƙa'ida wajen gudanar da aikin da aka ɗora wa kwamitin.
Saboda haka, muna roƙon shugabannin jam'iyyar ADC na ƙasa da su mutunta rahoton kwamitin nasu, domin hakan zai ƙara ɗaukaka martabar jam'iyyar a idanun 'ya'yanta da sauran al'umma. Adalcin da aka yi shi ne ke haifar da haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin jam'iyya.
Idan kuma, saɓanin abin da kwamitin ya tabbatar, aka ayyana wani daban a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da hujja mai ƙarfi ba, to hakan zai zama abin takaici matuƙa. Duk da haka, za mu bi duk hanyoyin da doka ta tanada cikin lumana da mutunci wajen neman haƙƙinmu.
Mun yi imani cewa akwai kotuna da ke tabbatar da adalci, amma sama da komai akwai Kotun Ubangiji, wadda ba ta yin kuskure, ba ta karɓar son zuciya, kuma babu mai kuɓuta daga hukuncinta. Wannan shi ne abin da ke ƙarfafa zukatan masu gaskiya.
Allah Ya sa shugabannin ADC na ƙasa su yanke hukunci bisa gaskiya da adalci, domin nasarar jam'iyya ba ta ta'allaka ga wanda ya fi ƙarfi ba, sai dai ga wanda ya fi gaskiya. Adalci shi ne abin da ke gina jam'iyya, kuma zalunci shi ne abin da ke rusa ta.
Saƙon Comrd Muneer Abdullahi Yusuf
05/08/2027