Albarkatv

Albarkatv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Albarkatv, TV Channel, Kano.

  MAI HASKE NE A CIKIN DUNIYAR ALHERI Na rayu da mutane iri daban-daban tun daga yarinta zuwa girma na— na hadu da masu ...
24/10/2025

MAI HASKE NE A CIKIN DUNIYAR ALHERI

Na rayu da mutane iri daban-daban tun daga yarinta zuwa girma na— na hadu da masu hali iri-iri: masu kirki, masu tausayi, da masu son kai. Amma gaskiya, ban taɓa ganin irin Abdul Amart Maikwashewa ba.

Mutum ne da zuciyarsa ta ginu a kan adalci, halacci, taimako, da kyakkyawar niyya.
A hulɗarsa da mutane, gaskiya da adalci su ne ginshiƙansa.

Yana kallon kowa da idon mutunci, yana yanke hukunci bisa gaskiya, ba tare da son rai ba.

A rayuwarsa, kirki, kyauta, da taimako sun zama al’ada.

Yana haɗa zumunci, yana gina abokantaka, kuma yana yafe wa waɗanda s**a saɓa masa domin zuciyarsa ta fahimci cewa yafiya tana kawo natsuwa.

Tausayin na ƙasa da shi ya zama abin alfahari.

A dalilinsa, wasu sun samu muhalli, wasu sun samu abin hawa, wasu sun yi aure da kwanciyar hankali.

Akwai kuma waɗanda Allah Ya basu waraka daga rashin lafiya ta dalilin taimakon sa.

Iyalai da dama da s**a rasa mafaka, yau suna cikin farin ciki da murmushi saboda kulawarsa da gudunmawarsa.

Allah Madaukaki ya yi bushara da irin waɗannan mutane a cikin Al-Kur’ani mai girma, inda Ya ce:

> “Wa man ya‘mal mithqāla dharratin khayran yarah.”
(“Duk wanda ya aikata koda ƙwayar zarra ta alheri, to zai gan ta.”)
— Suratul Zalzala: 7

Haka kuma Allah Ya ce:

“Inna alladhīna āmanū wa ‘amilus-sālihāti innā lā nuḍī‘u ajra man aḥsana ‘amala.”
(“Lalle waɗanda s**a yi imani s**a aikata ayyukan ƙwarai, ba za Mu ɓata lada ga wanda ya aikata alheri ba.”)
— Suratul Kahf: 30

Wannan shi ne Abdul Amart Maikwashewa — mutum mai imani, tausayi, hangen nesa, da adalci.

Halinsa ya zama darasi ga matasa, abin koyi ga shugabanni, kuma haske ga al’umma baki ɗaya.

A gaskiya, tsohon abokina ne, amma saboda irin kyawawan halayensa, tausayi, da kulawa da yake nuna wa mutane — yanzu ya zama ɗan uwa a zuciyata.

Allah Ya ƙara maka lafiya, natsuwa, da albarka a dukkan al’amuranka.

Allah Ya saka maka da alkhairi a duniya da lahira.

Barka da Juma’a — Allah Ya amshi ibadunmu, Ya sanya mu cikin waɗanda ake yi musu rahama a yau.

02/09/2025

📢 Official Announcement – Jastaheer Data Professional Application

https://www.jastaheerinformationtechnology.com/jastaheerdata/signup/?ref=jabirstahir

We are excited to inform our users and partners that the Jastaheer Data Professional Application is in its final development stage. The app is designed to provide a faster, more reliable, and more secure experience for all your data, airtime, and bill payment needs.

The official release is expected by the end of this month or early next month. Once launched, users will enjoy:
✅ Seamless transactions
✅ Improved wallet and referral features
✅ Better performance and user-friendly design
✅ Full support for our services (Data, Airtime, Electricity, Exam Pins, and more)

Stay tuned for the official release date. Thank you for being part of the Jastaheer family!

— Jastaheer Information Technology Team

Ya Allah Mai rahama, Mai jin ƙai, Mai iko akan komai…Muna roƙonka da sunanka Mai girma da siffofinka masu daraja, ka alb...
08/06/2025

Ya Allah Mai rahama, Mai jin ƙai, Mai iko akan komai…

Muna roƙonka da sunanka Mai girma da siffofinka masu daraja, ka albarkaci Jagora ka yawaita masa ni’ima a cikin rayuwarsa, ka tsare shi daga dukkan sharri da fitintinu, ka cika zuciyarsa da hikima, fahimta, da haske a dukkan al’amuransa.

Ka sanya albarka a cikin ayyukansa da burinsa, ka cigaba da ba shi damar zama jagora mai tsayawa akan gaskiya da adalci, wanda yake amfanar da jama’a da al’umma gaba ɗaya.

Ya Allah, muna roƙonka da rahamarka, ka gafarta wa iyayensa marigayi, ka sanya su cikin rahamarka mara adadi, ka sanya kabarinsu ya zama dausayin Aljanna. Ka gafarta musu kurakuransu, ka daukaka darajarsu a cikin Aljannar Fiddausi.

Ka albarkaci ’yayansa da ‘yan uwansa, ka sanya su su zama madogararsa da farin cikinsa. Ka ba su tarbiyyar da ta dace, ka tsare su daga sharrin zamani, ka buɗe musu kofofin alheri da arziki, ka sanya su cikin bayinka na ƙwarai.

Ya Allah, ka cika zuciyar Jagora Abdul Amart da haƙuri da ƙwarin gwiwa bisa rashin iyayensa, ka saka musu da alheri bisa irin kulawa da tarbiyyar da s**a bashi kafin rasuwarsu.

Allahumma, ka ba shi nisan kwana cikin lafiya da ɗaukaka, ka sanya masa nasara a cikin duniya da lahira.

Barka Da Sallah Jagora 01

Wani lokacin rayuwa tana mana kyauta ta musamman a cikin surar mutum.  daya ne daga cikin wadannan manyan kyaututtuka da...
16/05/2025

Wani lokacin rayuwa tana mana kyauta ta musamman a cikin surar mutum. daya ne daga cikin wadannan manyan kyaututtuka da yazo mana A wannan zamanin.

Mutum ne mai kyakkyawar zuciya – tawali’u da girmama mutane, tsantsar mutunci da himma mara misaltuwa wajen ciyar da al’umma gaba.

A kowane mataki da muka kalleshi, zaka ga mutum mai hangen nesa da zuciya mai tsafta wacce ke cike da buri nagari da tausayin na ƙasa dashi.

Daga mu abokansa na tuntuni, zuwa abokan aiki, kowa na da kalma guda ga Jagora,

Abdul Amart Maikwashewa mutum ne na kwarai.
Yana tafiya da kowa da kyautatawa, kuma bai tsaya ga daukaka kansa kadai ba, ya zabi ya zama haske ga duk Al'ummar dake kewaye dashi.

Yau da gobe, addu’armu gareka ita ce: Allah Ya baka dubban nasarori, ya dawwamar dakai a cikin alheri, ya kare ka daga sharri da hassada. Allah Ya kara baka ikon kaiwa inda burinka ke son zuwa, kuma ya saka maka da mafifinci alheri.

sunanka alamar daraja ce.

Jagoran Futa Kunya! , jagora mai jan matasa a jiki, yana ƙarfafa su wajen dogaro da kai da neman halak cikin gaskiya da ...
15/04/2025

Jagoran Futa Kunya!
, jagora mai jan matasa a jiki, yana ƙarfafa su wajen dogaro da kai da neman halak cikin gaskiya da rikon amana.

Jiya da kan sa ya jagoranci al'ummar sa tattaki daga Kano zuwa Katsina domin bude Dageji Media, kamfanin ɗaya daga cikin matasan da yake massa Aiki. Wannan ba ƙaramin abin alfahari bane—samun jagora kamar Abdul Amart wata baiwa ce da dole mu gode wa Allah.

Muna roƙon Ubangiji ya ƙara masa ƙarfin guiwa da nasara a dukkan al’amuransa.

Yanzu haka Dageji Media ya fara aiki!
Ku garzaya zuwa Kofar Kaura Underground, Maikudi Abdullahi's House, Katsina State domin cin moriyar Aiki na zamani.

Alhamdulillah Abinda samu ci kuma musha Allah ya H**e Mana, Kuma Allah yayi Mana Rufin Asirin da baza'a gan mu muna bin ...
06/03/2025

Alhamdulillah Abinda samu ci kuma musha Allah ya H**e Mana, Kuma Allah yayi Mana Rufin Asirin da baza'a gan mu muna bin layin karɓar Shikafa ba, Amma abin jan hankalin shine Ayi kwaikwayo da wanɗanda s**a gaba ta wajen irin wannan rabon wajen taɓo Kowanne batare da ƙabilanci ko wariyar launin fata ba!

Kada ka tilasta wa mutane son ka, Allah ya riga ya so ka fiye da ajizancinka.
02/01/2025

Kada ka tilasta wa mutane son ka, Allah ya riga ya so ka fiye da ajizancinka.

“Lokacin da kuka cutar da mutane masu zuciyar kirki, ba za su yi kururuwa ba, za su ci gaba da jin zafi a ciki.  Za su y...
02/01/2025

“Lokacin da kuka cutar da mutane masu zuciyar kirki, ba za su yi kururuwa ba, za su ci gaba da jin zafi a ciki. Za su yi shuru a hankali ba za su dawo ba. Ba za su daina zama nagari ba, ba za su ƙara amincewa da kai ba. Wannan shi ne daidai lokacin da kuka rasa su. " ✨

In the name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful, we begin this new film project with humility and hope. We se...
25/11/2024

In the name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful, we begin this new film project with humility and hope. We seek Your guidance, O Allah, in every step we take, and ask for Your blessings upon this endeavor. Grant us creativity, wisdom, and unity among the team. May this project be a source of success, inspiration, and positive impact. Protect us from challenges beyond our ability and make this journey smooth and fruitful. Ameen.

Allah Duk Wanda yayi Sanadin Farin Cikin mu.Allah ya Dauwamar Da farin Ciki a cikin Zuri'ar sa.   Allah ya baka Aljannah...
23/11/2024

Allah Duk Wanda yayi Sanadin Farin Cikin mu.
Allah ya Dauwamar Da farin Ciki a cikin Zuri'ar sa. Allah ya baka Aljannah maɗaukakiya

Kyakkyawar ɗabi'a ke kawo mutuntawa.Tabbas ina mutunta jagora   Saboda kyawawan Halayen sa na mutunta Dan Adam Da Girmam...
22/11/2024

Kyakkyawar ɗabi'a ke kawo mutuntawa.

Tabbas ina mutunta jagora Saboda kyawawan Halayen sa na mutunta Dan Adam Da Girmama Duk wanda yazo gareshi.

Wannan ita dabi'a ce ta kwarai daya samu a wajan magabata.

Albarkarcin wannan rana ta Juma'a nake Addu'ar Allah ya saka maka da gidan Aljannah

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albarkatv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category