01/01/2026
GAWURTACCEN SARKI
***
CHAPTER 124*Haduwar Shubairu Da Lumsaila* 3
***
**
✍️✍️✍️Marubuci: YUSUF IMAM BASHIR JEGA Y*I*B*J
***
*Gargadi*: Idan Kasan Bazaka iya Yin Like Da comment Da Sharhi ba, Pls Kada Kakarantamin Littafi.
***
~ My Whatsapp Number : 08164613474
***
*Ina Godiya Ga Wadanda Suke Karanta Wannan Litafin Gaskiya Kuna Sakani Cikin Farin Ciki allah Yabarmu Tare*.
***
Pls Vote
*Comment
*Like
*Share
*Sharhi
For My Encouragement.
***
Shinfida : Allah mun godemaka, da ka bamu ikon dawowa domin cigaban wannan Littafin wanda yanzu yakai shekara biyu da fara rubutawa.
***
Allah ya bamu ikon kai karshen sa lafiya 💅🌟⭐️
***
💪Admin Yusuf Imam Bashir Jega💪🌟
***
★Birnin Damashram, Fadar Birnin
***
Sarki Ashram ne zaune saman karagar mulkinsa, sanye yake cikin shigar yaƙi mai kwarjini da kuma ban tsoro.
Ya ratayo wata zabgegiyar takobinsa, sannan yana riƙe da wata kwari da baka doguwa mai tsini.
A saman cinyar sa kuwa, wasu kibiyoyi ne masu dinbin yawa ya saƙalo, sannan yalulluɓe ƙugun sa da kuma jikinsa da sulken yaƙi mai mugun ƙwari da tare hari.
Gefen sa kuwa, abokin sa ne, Shugaban Yam Fashin Duniya, ɗan fashi Jurgus ɗan Ramnaz na ƙauyen jilata.
Jurgus ya rufe fuskarsa da baƙin mayafi, sannan shima yana riƙe da wata rantsetsiyar takobi wadda bamu taɓa ganinsa rike da itaba sai yau, ko a yau kuma yanzu .
Yana zaune a saman wata kujera mai fuskantar karagar mulkin Sarki Ashram, da alama wataƙila tattaunawa sukeyi ko kuma zasu yi.
Sarki Ashram ne yayi saurin zaro Madubin tsafin sa da gaggawa, ya shafe sa da hannun hagu.
Yana mai karanto wasu ɗalisman tsafi , take Madubin tsafin yayi haske ya nuno fuskar Aljani Raihil-sam-hauzul .
Shugaban Aljannun Sararin samaniya na duniya, ɗan aiken sarki Ashram kuma bawan sa.
Idan baku manta ba, Sarkin matsafan duniya ya aika Sarki Shubairu da da Sarki Muzairu Birnin Lolusur.
Domin yana son Sarki Shubairu ya samo soyayyar Gimbiya Lumsaila ɗiyar Sarki Agjadarul-duwal na birnin Lolusur.
Domin suyi amfani da iya wurin kamo Sarkin Yam Fashin Duniya Jurgus, domin kuwa Lumsaila tsafi baya tasiri akanta ,wanda tsafi shine babban tinƙahon Sarkin Yam Fashin Duniya a cewar su.
Bayan Sarki Shubairu ya samu nasarar jefama Gimbiya Lumsaila soyayyarsa karo na farko kuwa a rayuwarta.
A ɗakin bautar su, bayan ya burgeta wurin ƙin jin tsoron wazirin mahaifinta, yaƙi bin umarninsa gaban kowa.
Kuma Gimbiya Lumsaila ta bashi goyon baya a bainar jama'a inda ran Waziri ya ɓace.
Bayan kowa ya koma gida bayan kammala bautar, bari mu ɗan koma bayan kaɗan .
Domin na tunatar daku baya, yadda idan muka cigaba bazai yimuku wahalar ganewa ba.
***
★Bayan kammala bauta
★Masaukin su Sarki Shubairu da Sarki Muzairu
***
Sarki Shubairu ne Zaune Kishingide A Saman Lumtsetsin Gadonsu ( inda s**ayi masaukin su, a birnin Lolusur a kyakykyawan Lambun nan nasu, Yana Mai Fuskantar Sarki Muzairu.
Sarki Shubairu ne Yayi Murmushin Farin Ciki ya Dubi Sarki Muzairu Yace, Da Alamu Yau Munje da Sa'a a Aikinmu Na Farko, Domin Kuwa Tabbas Gimbiya Lumsaila ta fada Komata, Ko Da ita zanyi Amfani Domin Cimma Burinmu , Yanzu Shin Minene Motsinmu Na Gaba ?
Sarki Muzairu ya Dubi Sarki Shubairu Ya Numfasa Kadan yace, Tabbas yanzu Mun Haye mataki Na Farko Yanzu Gimbiya Lumsaila ta afka kogin soyayyarka
" Mataki Na Biyu Shine Yayi Fitowarta Yawon Rangadi Cikin Kasuwa Duk Karshen Sati Wanda Zaik**a Nan da Kwana Biyu, Zata Zo Cikin Kasuwa Da ita Da Kuyanginta da Zugar Mayakan Sadaukai Masu Bata Tsaro da Kariya, To A Wannan Lokacin Zaka Samu Damar Jaddadamata Cewa kana Sonta !
" Wannan Shine Mataki Na Gaba, Abinda ya Ragemuna Shine Jiran Wannan Rana, Dalilin da yasa Nike Biyarka duk Inda Zaka Gudanar da Aikinka Shine, Domin Taimak**aka Koda ka Hadu da Bacin Rai A Wurin Gudanar da Aikinka, Ko A Yanzu ma Zan bika..... Tabbas Zaka Saye Zuciyar Gimbiya Lumsaila......
***
Al'amarin Gimbiya Lumsaila Kuwa Tun da Koma Turakarta Babu Abinda take Tunani Sama da Sarki Shubairu wanda ya burgeta matuka saboda Jarumtar sa.
Ita kanta Gimbiya Lumsaila Ta Cika Da Tsananin Mamaki Ganin Wai ita Lumsaila itace ke Tunanin Wani Da Namiji ?.
Duk da tayi Zamani da Manyan Kyawawan Samari Na Duniya Tun Zamanin Sarki Balunzar, Kai Har Sarki Balunzar Wanda Yakasance Kyakykyawa Nagaban Kwatance.
Amma Miyasa Bata fada Komar Soyayyarsa ba Ko da Kadan ne, Amma Zata iya cewa Saboda Shi Azzalumi ne ita kuma batason Zalunci Kuma babban burin ta shine kashe zalunci da wanzar da adalci a doron kasa tun wancan Camano har yanzu tana da wannan burin.
To ! Amma Ko A Yanzu Kamin Zowar Sarki Shubairu Birrninsu Tasha Gamuwa da Samari Masu bayyanamata Soyayya Masu Kudi Kuma diyan Sarauta.
Amma Koda A Kuskure Bata taba Kebewa Tana Tunanin su ba Sai Yanzu akan Sarki Shubairu ? To, Minene Dalili ?
Minene Yasa Haka ?, Wasu ma Masu Cemin Suna sona Sunfishi Kyawu Fa nesa ba kusa ba, Miyasa Sai Shi Naji Inaso ?
Tambayoyinda Gimbiya Lumsaila Keyima Kanta kenan A Cikin Turakarta A Wannan Lokacin bayan dawowa daga wurin bauta.
Gimbiya Lumsaila Kenan Batasan Da Wanene tayi Gamo ba, Daya daga Cikin Manyan Yaran Sarkin Matsafan Duniya Sarki Shubairu...............
Gimbiya Lumsaila taji Tana Bukaci da Sake Kallon Fuskar Sarki Shubairu Domin Ta Riga da takamu da Sonsa Farat Daya.
Kuma Batasan Yadda Za'ayi Ta Gansa A Wannan Lokacin ba, Kawai Ta Kudire A Ranta Sai tayi duk yadda Zatayi Ta Gansa A Ranar Fita Rangadin ta Dake Tafe A nan da kwana biyu.
***
Sarki Shubairu da Sarki Muzairu ne Zaune Cikin Tantinsu Na Lambun Nagtib Suna Tattaunawa da Shugabansu A Cikin Madubin Tsafi.
Shugabansu ne Yayi Murmushi yace, Tabbas Shubairu kayi Aiki yadda Akeso Kuma Komai Na tafiya Daidai , Zamuyi Nasara na rantse da darajar tsafi.
Sarki Shubairu Ya Numfasa Yana mai cewa, Ya Shugabana Anya Babu Saka Hannun Tsafinka Wurin Shawo Kan Gimbiya Lumsaila da Wuri Wuri Haka .
Shugabansu Ya Bushe da Dariya ya Dubi Sarki Shubairu Yace, Shin A Labarin Gimbiya Lumsaila da Sarki Balunzar Dana Baku Kunsan Minene Ya Hana Takubban Sarki Balunzar Guda Biyu Tasiri Akanta ?
Sarki Shubairu da Sarki Muzairu S**ayi Caraf S**ace , A'a Bamusan Dalili ba Amma Munason sani A Yanzu Domin Munyi Mamaki Sosai .
Shugabansu Ya Murmusa Yace, Saboda Sihirin Tsafi Baya Tasiri Akan Gimbiya Lumsaila, Sukuma Takubban na Sarki Balunzar An Samar dasu daga Sihirin Tsafi ne, Dan Haka Nima Sihirin Tsafi Na Bai Isa Yayi Tasiri Akan Gimbiya Lumsaila da sauri haka ba
"Tabbas Yana daga Cikin Dalilin da yasa Nikeson ka samo soyayyar Gimbiya Lumsaila Shine, Muddin ta Fada Kogin Soyyarka, Mukuma Munasace Takobin Zinaren mahaifinta Sarki Agjadarul-duwal Zaku Gudo Izuwa wurina, Tabbas Zata Biyoka Har Wurina, Nikuma Zan Kafamata Sharadin Muddin tana Sonka da Aure Dole ta Koma Tawagarmu Domin Zata Taimak**ana Sosai Wurin Gamawa da Emsahir 1 Sarkin Yam Fashin Duniya, Dan Fashi Jurgus Dan Ramnaz
"Gimbiya Lumsaila tana da Wata Baiwa Wadda Zata Kawoma Sarkin Yam Fashin Duniya Cikas, Baiwar Gimbiya Lumsaila itace BATAYIN TSAFI KUMA TSAFI BAYA TASIRI AKANTA....... Wannan Shine Kawai.......Kun Fahimta ?......
Sarki Shubairu da Sarki Muzairu S**a Jinjina Kai Alamun Fahimta Da Kuma Al'ajabin Wannan Baiwa ta Gimbiya Lumsaila Wadda Ba Kowane keda ita ba A Duniya.
Shugabansu Yacigaba da Cewa, Babban Dalilin da yasa ka Sace Zuciyar Gimbiya Lumsaila Shine, Jarumtar da Kanuna Wurin Rashin Tsoron Waziri Wanda Babu Abinda Gimbiya Lumsaila tafiso Ga Mutum Irin Jarumtaka
"Kasancewar Gimbiya Lumsaila Bata Nuna Fifikon Mai Kudi Akan Talaka, Shikuma Waziri Sabanin Hakane Bai shan Inuwa Guda da Talaka Yana Wulakantasu Sosai
"Ko Laifi Guda da Talaka da Mai Kudi S**ayi Mai Kudi Zaifi Samun Rangwame A Wurin Waziri, Ko Kuma Shi A Yafema mai kudin ma gaba ɗaya
"Wannan Dabi'a ta Waziri Tana bakanta Ran Gimbiya Lumsaila Sosai Batada Yadda Zatayi ne Shiyasa ta Hakura, Shi Mahaifinta Sarki Agjadarul-Duwal Bata Gayamasa ba
"Muddin ta Bari Yasani Zasu iya Samun yar Tsama Tsakaninsa da Waziri Wanda Zai iya Komawa Gaba Ko Rashin Jituwa A Tsakaninsu
"Shiyasa daka Nunamasa Taurin Kai Gimbiya Lumsaila Ta Goyi Bayanka, Kuma Dakarun Basu Isa Su K**akaba Muddin Gimbiya Lumsaila Ta Hana, k**ar yadda waziri yayi umarni ga dakaru da su k**aka
"Domin Umarnin Sarki Agjadarul-Duwal Shine Babba Gaba daya A Birnin , Na Gimbiya Lumsaila Shine Na Biyu, Na Waziri Shine Na Uku Saboda Babu Sarauniya Matar Sarki
"Umarnin Na Sama Yafi Na Kasa Tasiri, Umarnin Sarki Agjadarul-Duwal Yafi Na Gimbiya Lumsaila Tasiri, Umarnin Gimbiya Lumsaila Yafi Na Waziri Tasiri, Umarnin Waziri Yafi Na Kowa Tasiri A Birnin idan ka Cire Na Sarki Agjadarul-Duwal Dana Gimbiya Lumsaila
"Tabbas itama Gimbiya Lumsaila Da Kanta Zata Neme Sake Haduwa Dakai Domin Tabbas ta Kamu Da Sonka, A Tarihin ta Bata Kula Namiji ba Idan ba Mahaifinta ba Ko Dan Uwan sa Waziri
"Amma Farat Daya Gashi ta Kamu Da Matsanancin Sonka, Abinda nikeso Gareka Shubairu, Idan Gimbiya Lumsaila Ta fito Rangadin nata, Kayi Wani Abin Burgewa A Gareta Musamman Abubuwa Guda Biyu
"Ko kayi Wani Abu Na Jarumtaka Ta Hanyar Fafatawa da Wani Bujumin Sadauki Ko Kuma Kaga Ana Zalunci Kayi iya Kokarin ka ka hanashi, Tabbas Zaka Kara Samun Gurbi A Zuciyar Gimbiya Lumsaila
"Amma ka tabbata Gimbiya Lumsaila taga Wannan Abun dakayi, Idan Bata ganekaba Lamarin baiyiba, Domin Dama domin tagani Zakayi.
Sarkin Matsafan Duniya Yana Zowa Nan Azancinsa Sai Ya Dubi Sarki Muzairu Yace, Kai Kuma Muzairu Inason Kayi iya Kokarin Ka Domin Ganin Shubairu Bai Samu Cikas A Cikin Shirinsa ba
" Sannan Inason Kamin Gudanar da Gasar Jarumtaka da Za'ayi A Nan Birnin Na Lolusur Nan Kadan Ku Kaima Boka Sumrawa'il Ziyara, Akwai Wasu Abubuwa Dana Gayamasa Wasu Kuma Na Bashi Nace idan Kuka Zo Ya Gayamuku Su, Kuma Yabaku Su .
Daga Nan Sarkin Matsafan Duniya Yayi Bankwana dasu ya bace bat daga Cikin Madubin Tsafin.
***
★Saura Kwana Guda Fitowar Gimbiya Lumsaila Rangadi
***
Waziri Ne Zaune Saman Kujerar sa kusa da Sarki Agjadarul-Duwal Suna Tattaunawa.
Cikin Tsananin Damuwa Waziri Yadubi Sarki Agjadarul-Duwal Yana Mai Cewa, Yakai Dan Uwana Tabbas Na Cika Da Gagarumin Mamaki Wai Ace Gaba Gareka Kana Gani Wani Dan Wulakantattu ya Wulakantani A Bainar Jama'a Na Kasa Gareni Kuma Wai Kayi Shuru
"Sannan ita Lumsaila Har da ita Ake cimin Mutunci Gaba da Kowa, A Wannan Rana Na Fuskaci Hantara Daga Jama'a daban Daban, Wasu Abokan Gaba ta Na Birane daban Daban Sunyi ta Hantara ta
"Wasu Har da aikomin Wasikar Ban Dariya Da Yimin Habaici wai bani da Amfani A Birnin Nan Namu....
Sarki Agjadarul-Duwal Ya Dafa Kafadar Waziri Yace, Kayi Hakuri Yakai Dan Uwana, Nima Bada Son Raina Akayimaka Wannan Abun ba.
........Gimbiya Lumsaila ce Ta Shigo Fadar Cikin Ado Na Sarauta Tazo Gaban Mahaifinta ta duka ta Gaishe sa Ya Amsa Cikin Fara'a Da Annashuwa.
Tazo Gaban Waziri Ta Duka ta Gaishesa, Mikewa Tsaye kawai Yayi ya Kakkabe Alkyabbar sa Zai Ficewa Daga Fadar.
Sarki Agjadarul-Duwal Ya Dubesa Yace, Dawo Ka Zauna. Ko Saurarensa Waziri Baiyiba ya Cigaba da Tunkarar Kofar Fita Daga Fadar.
Sarki Agjadarul-Duwal Yakara cemasa, Nace Maka Ka dawo Ka Zauna Saman Kujerar ka Banason Shirme .
"Bazan dawo ba Domin Nafi Karfin Karamar Yarinya tayimin Rainin Wayo Na Zauna Wuri Guda da ita , BAZAN DAWO BA SHINE KAWAI.... " Waziri Ya Fada A Fusace Yana Mai Karasa Ficewa Daga Fadar.
Sarki Agjadarul-Duwal Yabi Waziri da Kallo Yana sake Sake A Ransa Yana Mai Tunanin Zafin Kai Irin Na Waziri , Sannan Ya tanadi Matakin da Zai Dauka Akan Sa Domin ya Sabama Umarninsa Karara.
***
Sarki Shubairu ne da Sarki Muzairu Zaune Gaban Wani Aljani Mai Mummunan Siffa, Suna Daddaure da Ankwa Kuma Sun Durkushe Bisa Guiwowinsu Suna Sheda Sama Sama A Matukar Galabaice .
Aljani RAIHIL- SAM-HAUZUL Kenan, Shugaban Aljannun Sararin Samaniya Na Duniya, Dan Aike Daga Sarki Ashram Na tare da Sarkin Yam Fashin Duniya.
Sarki Ashram Ya Turosa ne Domin Ya Kamo Su Sarki Shubairu da Muzairu, Muddin Wannan Aljanin ya K**asu a Yanzu To Shirin Sarkin Matsafan Duniya ya Lalace Gaba daya.
Kuma Ga Alamu Shirinsa ya Lalace Tun da Aljani Raihil-Sam-Hauzul Shugaban Aljannun Sararin Samaniya Na Duniya Ya Sacesu.
Kuma A Halin Yanzu Suna Cikin Karkashin Tekun Bahar Sulaijil Na Birnin Farisa, Birnin Su Yarima Rashbanul-Urfu Wanda Sarki Muzairu Ya Kashemasa Mahaifinsa Sarkin Birnin Farisa.
Kuma Ya Maida Birnin Karkashin Ikonsu, Ta yaya Sun Shigo Hannu Yarima Rashbanul-Urfu Zai Yadda A Kyalesu Su Tafi Salun-Alun Hakanan ?.
Aljani Raihil-Sam-Hauzul Ya Dubi Sarki Shubairu da Sarki Muzairu Yace, Yau dinnan Kuma A Yanzu Zaku Girbi Abinda Kuka Shuka A Tarihin Rayuwarku ta Duniya , Yanzu Abinda Ya Rage Shine Zan Tambayi Shugabana Ashram Wane Hukunci Za'a Yankemuku ....
Aljani Raihil-Sam-Hauzul Yana Zowa Nan Azancinsa Ya Zago Wani Madubin Tsafinsa Daga Aljihunsa Domin Tambayar Sarki Ashram Hukuncin da Za'a yankemusu.
*Wannan shine abinda ya faru a baya kaɗan *
***
Tunatarwa 1 : Muna da tawagar Kalkur, Boka Kalshur, Sarki Kulhum, Sarki Raibulu suna can a kurkukun Yarima Jarwazu ta Emsahir 2 ya ɗaure su bisa umarnin Sarkin matsafan duniya, domin Sarkin matsafan duniya ya sihirce Yarima Jarwazu yana ƙarkashin ikon sa sai abinda yace masa yayi yake yi.
Tunatarwa 2 : Muna da Yarima Rashbanul-urfu na birnin Farisa wanda Sarki Muzairu yaje yayima mahaifinsa yankan rago a birnin Farisa sannan ya mallake birnin, har yanzu Yarima Rashbanul-urfu yana son daukar fansa akan Sarki Muzairu.
Tunatarwa 3 : Muna da Yarima Jarwazu wanda shine Emsahir 2 wanda babban burin sa shine kamo Emsahir 1 Sarkin Yam Fashin Duniya Jurgus.
Tunatarwa 4 : Muna da Gimbiya Darwina wadda ɗiya ce ga Sarki Shubairu ɗan Shaljan na birnin kalsur ( na tare da Sarki Muzairu ), wadda a yanzu haka tana tare da Sarki Fairul wanda shine Hazbulul-shadul, matakin da tauraruwa Jelsara ta bashi kamin Jurgus ya shafe ta daga doron ƙasa.
* Wannan shine, mun tuna muku baya, yanzu zamu cigaba daga inda muka tsaya*
***
Yau 1/1/2026
Next Chapter On Litanin 5/1/2026 Insha Allah
***
Gawurtaccen Sarki Littafin Yaki
Pls Follow This Page For more Book Of War.