18/06/2026
ina samun irin waɗannan tambayoyi a kullum
Akwai wane abokina jiya yake yi mun magana yauma an sami wane yayi mun magana a kan ƙirƙirar Manyan Application na banki wallet irin su {Opay Plampay kuda Dadai sauransu}
Yana so in taimaka mar ya karasa aikin sa na
Kirkirar Application na banki Kamar irin su
{Opay Plampay kuda) sai nake fada mar wadannan abubuwan Suna bukatar Capital da muka Ilimin
Ni fa ba wai bazan iya kirkirar ko wane irin Application bane no Kawai Akwai application din da yana bukatar Capital da ilimin na Cyber security ethical hackers
Irin wannan app ɗin ba ya zama a hosting na yau da kullum. Yana buƙatar kariya ta musamman daga hare-haren yanar gizo (Cyberattacks) da kuma sabar mai ƙarfi kamar AWS (Amazon Web Services) ko Google Cloud.
Hukumar CBN tana buƙatar kowane app na banki ya tabbatar da BVN, NIN, ko katin zabe na abokan ciniki. Akwai kuɗi da ake biya na kowane bincike guda ɗaya (Verification API fee).
Kuna buƙatar APIs daga kamfanoni kamar su Monnify, Flutterwave, Paystack, ko Providus Bank domin samarwa mutane lambobin asusu (Virtual Accounts) da kuma tura kuɗi zuwa sauran bankuna. Waɗannan kamfanonin suna majallata kuɗi ko kowane transaction.
Tura Saƙon Kwamfuta (SMS/OTP Gateways):
Kuɗin saƙon OTP da ke shiga wayar mutane idan za su yi rajista ko tura kuɗi.
Gargadɗi da shawara daka Ni Usman Ɗuguya
⚠️ Tsararren Gargaɗi (Legal & Security):
Harkar kuɗi tana da zafi. Ka tabbata ka rubuta yarjejeniya (Contract) ta doka. Kada ka yarda ka saki app ɗin muddin ba a gama binciken tsaro (Pe*******on Testing) an tabbatar babu kafar da za a iya hack ɗin kuɗaɗen mutane ba.
Ga masu san a kirkirar musu Websites Application yayi mun magana.......