13/11/2023
Labarin Talle Da Jan Wake.
A wani ƙauye anyi wani saurayi mai suna Talle, yana zaune da mahaifiyar sa, da kuma wata ramamiyar Saniyar su wadda bata samar da madarar da zasu siyar su sayi abin ci har ma su siyawa saniyar.
Sai wata rana mahaifiyar Talle ta yanke shawarar saida Saniyar nan don su sai abinci, ta kira Talle tace ya kai Saniya kasuwa don sayarwa.
Talle ya k**a saniya ya nufi kasuwa domin sayar da ita, yana cikin tafiya sai ya gamu da wani dattijo. Dattijo yace da Talle ina zaka da wannan saniya? Sai Talle ya amsa masa da cewa zani kasuwa ne don na sayar da ita.
Sai dattijo yace ina so amma zan musanya maka ita da waken Sihiri Wadda zai sa ka wadata sosai. Talle yayi tunani cikin zuciyarsa yana cewa amma ta yaya wannan waken zai sanya ni wadata kuma ma waken ba mai yawa ba ƙwaya biyu kawai.
Wata zuciyar kuma tana gaya masa cewa wannan mutum Dattijo ne kuma ga farin gashi don haka bazai ƙarya ba. Nan take Talle ya amince da musanya saniyar sa da waken Sihiri daga wurin dattijo.
Dattijo ya sanya hannu a aljihu ya curo jajayen wake guda biyu ya bawa Talle. Talle ya koma gida a ruɗe da zulumin tayaya wannan jajayen wake zasu wadata su da arziƙi?.
Da isar Talle gida sai mahaifiyar sa ta tambaye shi, ka sayar da Saniyar? Sai ya amsa mata da cewa E , sai tace nawa aka sayar da ita, sai Talle ya bawa mahaifiyar sa labarin yadda s**ayi da Dattijo ya kuma ɗauko waken Sihirin ya bata, sai mahaifiyar Talle ta fusata matuƙa tace ka san cewa wannan saniya ita kaɗai muka mallaka amma ka musanya ta da ƙwayar wake guda biyu.
Sai mahaifiyar Talle ta watsar da waken ta taga, Talle yayi matuƙar baƙin ciki ganin yadda mahaifiyar sa ta damu sosai.
Kasancewar wannan lamari talle ya kasa cin abinci yana ta saƙe saƙe a cikin zuciyarsa yana cewa yanzu wannan saniya ta tafi a banza bamu amfana da komai ba gashi nayi sanadiyyar ɓatawa mahaifiyata rai.
Talle na cikin wannan yanayi na tunani har bacci ya kwashe shi.
Talle ya farka daga bacci sai yaga haske sosai a cikin ɗakin sa ba k**ar yadda ya saba ganin hasken rana na haska ɗakin sa ba, sai ya cika da mamaki yana cewa wannan wanne irin haske ne haka?
Sai yaje ya leƙa tagar ɗakin sa kwatsam sai yaga wata ƙatuwar bishiya wadda bai taɓa ganin irinta ba, Talle yayi mamaki sosai amma koda yaje kusa da bishiyar sai ya fahimci ashe waken Sihirin da mahaifiyar ta watsar ne ya fitar da wanna ƙatuwar bishiya haka, kuma daga samanta ne wannan haske yake fita har ya haska ɗakin sa.
Talle ya yanke shawarar hawa wannan ƙatuwar bishiya don ganewa idanun sa, yayi ta hawa har saida ya kai ƙarshen ta
Bayan hawan Talle bishiyar ne sai idanunsa s**a gane masa wata ƙatuwar fada ga haske ko ina kai kace wata daren goma sha biyar, Talle bai tsaya wani dogon tunani ba kawai ya shiga cikin fadar.
Talle na shiga sai ya cika da mamaki ganin yadda aka ƙayata fadar da kayan ado iri daban daban, ga kuma ƙwarangwal na mutane suna gadin wani ƙaton dodo.
Talle ya firgita matuƙa amma ya yanke shawarar cigaba da tafiya a cikin fadar kasancewar ganin wannan dodo yana bacci, ganin Talle yana tafiya cikin fadar bai tsaya ba sai waɗannan ƙwarangwal s**a fara fitar da wani sauti wanda hakan ya sanya wannan ƙaton dodo farkawa daga baccin da yake, koda Talle ya ga dodo ya farka sai yay wuf ya ɓuya a bayan manyan kujerun dake cikin falon.
Dodon yay nema iya nema amma baiga Talle a cikin falon ba, don haka sai ya nufi kicin ya ɗauko nama yaci, bayan ya gama sai ya ajiye ragowar naman ya kuma sanya hannu a aljihun sa ya ɗauko jakar zinari ya ajiye akan teburin dake gabansa ya koma yaci gaba da bacci abinsa.
Koda Talle ya fahimci cewa dodo ya koma bacci sai yay saurin fitowa daga inda ya ɓoye, ya nufi kan teburin kai tsaye ya ɗauki jakar zinari ya gudu da ita.
Da gari ya waye Talle ya ɗauki zinari ya kaiwa mahaifiyar sa, koda mahaifiyar Talle ta ga zinari sai kyalli ya ke, sai tayi farin ciki amma ta tambayi Talle shin a ina kasami wannan zinari haka. Talle ya bata labarin duk abin da ya faru, tayi farin ciki sosai har s**a sai da guda ɗaya s**a sayi abinci.
Koda dare yay sai Talle ya kuma tashi ya hau kan wannan bishiya, ya shiga cikin fadar k**ar yada ya shiga jiya.
Da shigar sa sai ya kuma iske ƙaton dodo yana bacci, amma da ƙwarangwal s**a ganshi sai s**a fara fitar da wannan sauti mai ƙara k**ar na jiya wanda hakan yasa dodon ya kuma farkawa, yana ta dube dube amma baiga Talle ba.
Don haka sai ya nufi kicin ya ɗauki nama yaci yasha ruwan inibi, ya kuma ɗauko kaza mai rai ya nufi kan teburin sa ya ajiye ta ya kuma ce mata maza kiyimin kwai na zinariya, nan take kazar tayi ƙwan zinari ya ɗauka ya saka a aljihun sa ya kuma koma bacci harda munshari.
Koda Talle ya fuskanci bacin dodo yayi nisa sai ya fito daga maɓoyar sa ya ɗauke kaza ya sauka daga kan bishiya.
Washegari ya ɗauki kaza ya kaiwa mahaifiyar sa ya bata labarin duk abin da ya faru, nan take Talle ya umarci kaza tayi masa ƙwan zinari, kaza tayi ', s**a ci gaba da tara zinari.
Da dare yay Talle ya sake komawa wannan fada a karo na uku sai dai amma wannan karon ya samu dodo baiyi bacci ba yana buga garaya, kasancewar Talle yana son garaya don haka ya samu wuri ya ɓoye yana ta sauraron garayar da dodo ke kaɗawa har bacci ya ɗauke dodo.
Koda Talle ya ga dodo yayi baci sai ya fito daga maɓoyar sa ya nufi inda dodo ya ajiye garayar, ya sanya hannu zai ɗauka ashe garaya ta Sihiri ce sai ta k**a kururuwa da ƙarfi tana cewa “Ka cece ni ya uban gidana Talle zai sace ni” nan ta ke Dodo ya farka ya kaiwa Talle cafka amma bai same shi ba don haka yabi Talle da gudu har ya kusa cimma sa.
Nan take Talle ya nufi hanyar sauka daga kan bishiyar waken Sihiri, koda Talle ya sauka sai ya ga cewa dodo ma na ƙoƙarin saukowa don haka sai ya nemo Gatari ya fara saran gidin bishiyar waken Sihiri har ya sareta ta fado shima dodo ya faɗo ƙasa matacce.
Yayin da Talle da mahaifiyar sa s**a ga abin da ya faru sai s**ayi ƙaura daga garin s**a sayi babban gida da shanu masu yawa wanda zasu iya tatsar madara don su sayar.
AlummarHausa
13/11/23