Aminci Radio 103.9FM

Aminci Radio 103.9FM Gidan Rediyon Aminci (Aminci Radio) mai taken "Domin Cigaban Al'umma..." muna yada shirye-shiryen mu akan mita 103.9 akan zangon FM.

Mun yi muku tanadin kayatattun shirye-shirye masu fadakarwa, ilimantarwa, wa'azantarwa har ma da nishadantarwa. Duk Domin cigaban al'umma bakidaya.

Zanyi amfani da 60% na alawus dina, na wannan watan wajan buga katin gani Likita a Asibiti Tsanyawa.
30/07/2025

Zanyi amfani da 60% na alawus dina, na wannan watan wajan buga katin gani Likita a Asibiti Tsanyawa.


Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Mr Olumode Samuel a Matsayin sabon Shugaban Kashe Gobara ta Kasa.Sabo...
30/07/2025

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Mr Olumode Samuel a Matsayin sabon Shugaban Kashe Gobara ta Kasa.

Sabon nadin zai fara Aiki daga Ranar sha Hudu ga Watan Julin wannan Shekara.

Bayanan Hakan na kinshe cikin wata sanarwa Mai dauke da sa Hannun Sakataren Hukumar kula da Hukumomin Dake karkashin Ma'aikatar Harkokin cikin Gida Manjo Janar Abdulmalik M. Jibrin(Mai Ritaya), Nadin na sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ya biyo bayan Cikar wa'adin Shekarun Ritayar Tsohon Shugaban Hukumar Engr Jaji Olola abdulganiyyu bayan da yacika Shekara Sittin da Haihuwa.


fitaccen dan kasuwa a nan Kano Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya bukaci gwamnatoci a matakai daban daban na k...
30/07/2025

fitaccen dan kasuwa a nan Kano Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya bukaci gwamnatoci a matakai daban daban na kasar nan dasu maida hankali wajen gudanar da ayyukan da zasu rage talauci a tsakanin al'umma.

Dan kasuwar ya shawarci gwamnoni a wadannan shekaru biyu da s**a rage masu duba da irin manyan ayyuka da s**a gudanar a shekaru biyun da s**a gabata , a yanzu lokaci ne da yakamata dasu karkata wajan aiwatar da kananan ayyuka da zasu taba rayuwar alumma kai tsaye, wanda hakan zai rage aikata kanana laifuka a tsakanin allumma.

SKY ya bayyana hakanne a yayin bikin rufe karatun littafin Ashfa wanda Malam Abdulkadir Shehu mai Anwar ya gabatar a unguwar Tudun Yola dake karamar hukumar Gwale.

Ya ce a halin yanzu mutane suna cikin halin matsi da talauci wanda yake hana su walwala, a don haka ya kamata gwamnati tayi tunanin samar da ayyukan da zasu taba rayuwar alumma kai tsaye wanda zai rage musu radadin halin da suke ciki.

Sky ya bukaci gwamnoninmu dasu ware wasu makudan kudade da zasu dunga tallafawa yan kasuwa da sauran masu gudanarda sana oi daban daban ; domin karfafa musu gwaiwa wajan bunkasa kasuwancinsu.

Yace a wannan lokaci da yawa daga cikin yan kasuwa masu karamin karfi jarinsu ya karye, ya kamata gwamnatin Tarayya da gwamnoni jahohi musamman na Arewacin Nigeriya su fito da wasu hanyoyi da zasu tallafawa alummarsu yadda za a rage talauci da fatara da samar da ingantacciyar Rayuwa da zaman lafiya a cikin al’umma.

Sky ya shawarci gwamnatin jihohi dasu samarwa da mañoma Taki kyauta domin a halin yanzu manoma suna bukatar tallafi daga gwamnati domin basa iya sayan Taki sakamakon tsadar da yayi , wanda hakan ne zai taimaka wajan kokarin da gwamnati take na samarda abinci a cikin farashi mai sauki .

Ya kuma bukacesu dasu samarda Gidaje kanana a gurare daban daban, duba da cikonso da ake fama dashi acikin gari wanda yana taimakawa wajan haifarda aikata kananan laifuka a a tsakanin matasa .kuma idan akayi hakan ma aikata da sauran masu karamin karfi zasu amfana da wannan aiki.

Taron ya samu halartar alumma da dama da s**a hadarda limamai da s**a hadarda hakimin kauran Namoda a jihar Zamfara da sauransu.

Release kamalu yakubu Ali
Amadadin Alhaji kabiru sani kwangila yakasai.

30/07/2025

Shirin Ankwana Lafiya na Yau Laraba 30/07/2025, Inda muke karbar Bakoncin Kwamitin shirya Taron Kungiyar Malaman dake koyar da Ilimin Zaman takewar Dan Adam da Al'adunsa ta Kasa.

Dafatan za'ayi sauraro Lafiya.



Inna Lillahi Wainna Ilaihin Rajiun Allah ya yiwa Alhaji Ahmad Makama rasuwa, (Makaman Hardawa) Shugaban Hukamar Zabe ta ...
30/07/2025

Inna Lillahi Wainna Ilaihin Rajiun

Allah ya yiwa Alhaji Ahmad Makama rasuwa, (Makaman Hardawa) Shugaban Hukamar Zabe ta Jihar Bauchi Wato (Bauchi State Independent Electoral Commission BASIEC) kuma tsohon kwamishinan hukumar zabe ta ƙasa a (INEC) a Jihohin Nasarawa, Taraba da Yobe.

Allah ya gafarta masa. Ameen


Cikin hutuna.Yadda magoya bayan Jam'iyyar APC Mai Mulki S**a Tarbe Sabon Shugaban Jam'iyar Prof. Nantawe Yilwatda a Ofis...
30/07/2025

Cikin hutuna.
Yadda magoya bayan Jam'iyyar APC Mai Mulki S**a Tarbe Sabon Shugaban Jam'iyar Prof. Nantawe Yilwatda a Ofishin Jam'iyyar na Ƙasa dake birnin tarraya Abuja.

Labarai cikin hotuna. Yadda Gwamnatin jihar Zamfara ta miƙa  takardar naɗin ga sabon  Mai Marbata Sarkin Katsinan Gusau ...
30/07/2025

Labarai cikin hotuna.

Yadda Gwamnatin jihar Zamfara ta miƙa takardar naɗin ga sabon Mai Marbata Sarkin Katsinan Gusau Alhaji Abdulƙadir Ibrahim Bello ajiya Talata.

Yadda aka gudanar da bikin taya murna sami karin girma ga wasu daga cikin jami'an Yan sanda na Karamar hukumar Bichi, wa...
29/07/2025

Yadda aka gudanar da bikin taya murna sami karin girma ga wasu daga cikin jami'an Yan sanda na Karamar hukumar Bichi, wanda Babba Baturen yan sanda na Bichi SP Murtala Muhammad Fagam ya jagoranta tare da taimakawar iyalan wanda s**a sami karin girma.

Wanda s**a sami karin girma sun hada:
1. Zakari Bahago daga Sefetor yan sanda zuwa mataimakin Sifitandar yansanda.
2. Saminu Usman daga Sajan ɗin yan sanda zuwa Sefetor yan sanda.
3. Sani Ibrahim daga Sajan ɗin yan sanda zuwa Sefetor yan sanda.
4. Umar Habibu daga Sajan ɗin yan sanda zuwa Sefetor yan sanda.
5. Muhammad Umar daga Sajan zuwa Sefetor yan sanda.
6. Lawan Muhammad daga Sajan ɗin yan sanda zuwa Sefetor yan sanda.
7. Ado Sale daga kofir din yan sanda zuwa Sajan ɗin yan sanda.
8. Musa Ahmad daga kofir din yan sanda zuwa Sajan yan sanda.
9. Muhammad Hussaini daga Kofir din yan sanda zuwa Sajan din yan sanda.
Taro ya sami halartar Shugaban Kwamiti PCRC na Bichi Alh Aliyu Ibrahim Bichi da mataimakinsa Alh Nasiru Yakasai da sauransu yan sanda da jama'a garin.



Shugaban karamar hukumar Fagge Hon. Salisu Usman Masu, yace inganta ilimi ne zai kawo karshen fadan daba a Jahar Kano Sh...
29/07/2025

Shugaban karamar hukumar Fagge Hon. Salisu Usman Masu, yace inganta ilimi ne zai kawo karshen fadan daba a Jahar Kano

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da kwamiti daga majalisar dokokin Kano ya kai ziyarar gani da ido makaranta firamare ta Kurna dake kan titin Katsina a karamar hukumar Fagge.

Hon. Salisu Masu ya bayyana godiyar sa ga gwamna Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, bisa yadda ya ke bai wa kananan hukumomin Jihar ƙuɗaɗe domin tallafawa ilimi a faɗin Kano.

29/07/2025
29/07/2025

Shirin Doka da Oda na yau Talata 29/07/2025, Tare da Mai magana da Yawun Hukumar EFCC ta Kasa shiyyar Kano (Kano, Katsina da Jigawa) Malam Idris Isyaku.

Ghazali Maimashi Bebeji.

Tsohon Ɗan takarar Mataimakin Gwamna Jihar Kaduna ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023,  John Ayuba a ya fice daga jam’i...
29/07/2025

Tsohon Ɗan takarar Mataimakin Gwamna Jihar Kaduna ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, John Ayuba a ya fice daga jam’iyyar ta PDPya kuma komawa jam’iyyar ADC.

Ayuba ya sanar da ficewarsa ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban PDP na unguwar Unguwan Gaiya da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.


Address

No. 71 Sharada Phase 3 Industrial Estate
Kano
700281

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminci Radio 103.9FM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminci Radio 103.9FM:

Share

Our Story

Gidan Rediyon Aminci (Aminci Radio) mai taken "Domin Cigaban Al'umma..." muna yada shirye-shiryen mu akan mita 103.9 akan zangon FM. Mun yi muku tanadin kayatattun shirye-shirye masu fadakarwa, ilimantarwa, wa'azantarwa har ma da nishadantarwa. Duk Domin cigaban al'umma baki daya.