22/05/2025
JARABAWAR DA AKAIWA SARKIN BARAYI NOMAU
Cigaban Labarin Sarkin Noma da 'ya'yansa.
Littafi: Magana Jarice 2
Mawallafi: Alhaji Abubakar Imam
Da gari ya waye Sarki ya aika Sarkin Noma ya zo da shi da Nomau, ya ce masa, “Tun da ka ce sata ce ka ke tak**a da ita, in za ka shiga cikin maneman ’yata, zan jarraba ka da abu hudu. In ka kasa ko daya na kashe ka, don fa ka zo yi mini sata ne. Ka yarda?”
Sarki ya ce, “Gobe ka zo ka sace zobena. Ga shi nan zan ajiye shi bisa tebur da rana ana fadanci. Ba na ko yarda da a yi layar zana.”
Nomau ya ce, “To, Allah ya kai mu.” Ya yi ban kwana ya tafi.
Mutane s**a ce, “Ai ko gobe muna shirin ganin bidiri yadda za a saci zobe da rana gata gabammu muna ji muna gani, ba da ko an yi laya ba.”
Kashegari Sarki ya fidda zobe ya ajiye a tebur, mutane s**a kewaye ana ta fadanci. Sun tabbata zoben ba ya satuwa. Suna nan zaune sai ga wani tsoho da sanho a rike, ya leko Majalisan nan, yana bara yana cewa, “Allah ya bu ku na Allah, Allah ya sa mu cikin cetattu.”
Da wani bafade ya gan shi sai ya buga masa tsawa ya ce “Kai, tafi daga nan, ba ka san nan fada ba ce? Tsufa hauka ne?”
Sarki ya ce, “Kyale shi ya yi ta yi, ai yanzu shi dai dai ya ke da yaro.” Sai tsohon nan ya kaikaici idonsu ya saki zomo a zauren. Da ganinsa sai fadawa s**a ce, “Ihu, ga zomo! Ihu, ga zomo!” Sarki ya ce, “Kai, ku kyale shi, ku lura da abin da ku ke yi.”
Sai tsohon nan kuma ya sake sakin gudan. Fadawa s**a ce, “Ai, ga wani , ga wani! Ashe biyu ne! Ai ko firda-firda ne. Watakila ko da mace da namiji ne, sa yi raha a gwama su da naman dajin da Sarki ke kiwo.”
Sarki ya ce, “Har yau ko ban ta6a kiwonsu ba. Amma dai kuci gaba da aikinku" tsohon nan na nan tsaye na ta bara, ya sake sakin guda.
Sarki ya yi wuf ya tashi, ya ce, “Ku tara a k**a su, in gama cikin wadanda nake kiwo.” Mutane s**a tashi suna bin zomaye cikin gida su k**a, s**a bar zobe nan bisa tebur. Da suke k**a zomayen s**a dawo. Ko da Sarki ya zo ya duba tebur, sai ya yi salati, ya ce, “Wa ya dauki zoben da ke nan yanzu yanzu?” Ba wanda ya amsa. Duk fadawa s**a shiga lalabe-lalabe cikin qura ba zobe ba dalilinsa.
Can da azahar sai ga Nomau ya zo da zoben Sarki, ya yi gaisuwa ya ce, “Ga shi, Allah ya ba ka nasara.”
Sarki ya karbi zobe ya duba, ya ga dai nasa ne, ya ce, “Karya dai ka ke yi, layar zana ka yi ka zo ka dauka, an ko ce ban da layar zana.”
Nomau ya ce, “Ba layar zana na yi ba, Allah ya ba ka nasara. Ni ne na yiwo shiri k**ar tsoho, na zo ina bara a wajenku dazun da hantsi, na saki zomaye don ku bi. Wannan ai ba wani abu ba ne. Sai ka fadi na biyu.”
Sarki ya huta, ya ce, “To, yau da dare ka zo ka sace gunya din nan nawa Dan-tsito.”
Sarkin Barayi Nomau ya yi gaisuwa ya fita ya tafi gida, ’yan’uwansa s**a yi ta yi masa dariya.
Tun kafin rana ta fadi ya je ya sami tulun giya ya sayo ya ajiye. Da dare ya raba, ya yi shiri k**ar ’yar tsohuwa, ya dauki tulun giya ya nufi gidan Sarki. Kafin ya kai hadarin ruwa ya taso, ruwa ya yi ta dukansa, ya isa gidan sarki tsamo-tsamo yana makyarkyata. Da isarsa sai ya tarad da Sarki ya sa dogarai takwas na tsare da Dantsito, ko wanensu ga baka da kwari rataye. Ya tarad da hudu daga cikinsu kowa ya k**a qafar dokin nan guda ya rike. Daya ya sa masa ragama ya rike, ga wani can kame da wutsiya, wannan kuwa ya k**a dokin ya dare. Guda kuwa, watau babbansu, shi sai kewayar gida ya ke yi yana gadi. Da ya fito wajen zauren barga yana leqe, sai ya ga ’yar tsohuwa da kayan tulu duk ta jika, sai makyarkyata ta ke yi, haqora na qaf qaf qaf, ga ta tsugunne gindin katanga daga waje. Sai ya fito ya daka mata tsawa, “Ke tsohuwa, ina za ki?”
Yar tsohuwa ta durkusa jiki na rawa, ta gigice, ta ce wa dogarin nan, “Na fito kasuwa ne, dare ya yi mini, har na sha kashin ruwa, shi ya sa na ra6o in la6e. Giya na kawo kasuwa tun daga qauye, ga shi na yiwo dare ba ta sami kasuwa ba.”
Dogari ya matsa ya kwace tulun giya, ya kafa kai kwakwal kwakwal, wai ya yi maganin barci. Bai san giyan nan akwai banju a ciki ba. Tsohuwa ta ce, “Don Allah yi hankali kada ka fasa mini tulu.”
Dogari ya harare ta, ya ce, “Tulun banza! Wane tulu ke gare ki?” Ya sami giya ya kyankyama dayan cikinsa, sa’an nan ya koma gefe guda ya kishingide, wai ya shakata sa’an nan ya shiga wajen aikinsa. Can sai kafirar ta fara dibarsa yana tangadi, kafin a yi haka banju ya taso ya shiga aikin nasa, sai barci. Tsohuwan nan da ta ga ya yi barci ta tashi sannu kan hankali, ta tube rigar dogarin nan da rawaninsa ta sa, ta dauki umararsa ta rike, ta nufi inda dogaran nan ke qumun Dantsito, ta ce musu k**ar ita ce dogarin, “Ba ku sani ba fa, fitan nan tawa sai da na gamu da ja’irin, na dana kibiya zan dirka masa, ya fadi yana roqona gafara. Tausayi ya k**a ni na kyale shi, bayan na sa ya rantse ba ya dawowa. Mai so duk ya yi ta barcinsa, ba kome. Kuma in wani na tsoron wani abu, ko Sarki ya tambaye ku da safe ku ce ni na ce ku yi. In ko kun fi so ku yi ta zama, ku yi ta yi, ni dai don sule ashirin da biyar ba na wahal da kaina, kun ga kwanciyata.” Sai ya bingire k**ar yana barci.
Sauran dogarai sun samu babbansu ya ce ko wani abu ya faru da safe su ce shi ne, to, me ya dame su? Sai s**a yi ta gyangyadi nan har da minshari. Da Nomau ya ji sun fara jan rago sai ya tashi ya fita waje ya dauko kayan da ya hoye, ya sa itatuwa hudu masu gwafa ya gina rami ya kafa su, biyu baya, biyu gaba, ya aza wadansu itatuwa bisa k**ar masaqa, ya ciccibi wanda ke bisan dokin nan ya aza bisa itatuwa, ga shi yana gyangyadi bai sani ba. Ya dauki igiyoyi ya daura wa itatuwan nan: Dogarin da ke rike da wutsiya, da mai riqe da ragama, ya ba su s**a rike igiyoyin dai dai, suna barci ba su sani ba. Wadanda ke rike kafafuwan ko wanne ya ba shi icen nan guda ya rike. Shi kuwa ya kwance dokin, ya daura masa tsumma a kofato, ya ja ya surare da shi, ya bar dogarawa nan na ta sharar gyangyadi, Sarkin Dogarai kuwa babbansu na kofar gida, giya ta buge shi.
Da gari ya waye Sarki ya bude gida ya tarad da yadda Nomau ya yi wa zababbun dogarawansa, abin kuma ya wuce na ban haushi, sai ya bushe da dariya. Ya ra6a ya fita, ya bar su nan kowa na ta sharar barci, wadansu da ice a hannu, wadansu da igiyoyi sun rike. Ya aika aka ta da Waziri, s**a zo s**a yi ta dariya. Sa’an nan Sarki ya dauki bulala ya yi ta tsala musu, ’s**a farka suna ta zurawa a guje.
Hantsi ya yi sai ga Nomau da Tlantsito yana janye, ya kawo wa Sarki. Sarki ya fusata, ya ce, “Yau da dare ka shigo turakata ka sace bargon da na ke kwance sama. Zan hada bindiga, in ka zo ko in kashe ka. Yau ko na ke so ka zo, ban ce gobe ba ko jibi. Ba na sa kowa gadinka.”
Sarkin Barayi Nomau ya ce, “Allah ya kai mu.” Ya mike tsaye ya ce, “Sai ni daki bari na Sarkin Noma, kushewar badi sai badi!” Ya sallami Sarki ya tafi.
Magariba na yi ya tafi hurumi, ya duba wani sabon kabari ya tone, ya dauko gawar ya kawo gida, ya sami tsani ya gama ya boye. Can da dare ya tashi ya dauki gawan nan da tsanin, ya nufi gidan Sarki ya shiga. Ya tasam ma turakarsa ya tarad da taga bude, ga fitila na ci k**ar rana. Sai ya jingina tsani daidai taga, ya dauki gawan nan ya sa6a a kafada ya-k**a hawan tsani da ita. Can kan gawa ya kai daidai da taga sai Sarki ya gan shi, ya aune shi da bindiga kwararam, ya sami gawa a ka. Sai’ Sarkin Barayi ya saki gawan nan kasa tim.
Sarki ya ce wa uwargida da ke nan tare da shi, “Haba kin ji na kashe shi, kowa ya huta. Amma fa a ce ’yar cikina ta rasa wanda za ta aura sai 6arawo, ai kin san da sake! Sai ya tashi ya dauki fitila, ya biyo matakin soro ya gangaro ya gani.
Sa’ad da yana gangarowa sai Sarkin Barayi ya shiga ta taga, ya ce wa matar Sarki, “Miqo mini bargon nan da mu ke kwance kai in yafa, wannan luru bai ishe ni ba, dari! Haba, abu yau sai ka ce daren nan jaura ke wucewa.”
Abu cikin duhu, matar na tsammani Sarki ne, ta dauki bargo daga kan gado ta durkusa ta ba shi, ta ce, “Mun dai huta da wannan qanqama.”
Nomau ya ce, “Da ma daga an kyale shi, ai rashin jini rashin tsagawa.” Yana nan k**ar yana gyarawa, da ya ji Sarki na hawowa shi kuma sai ya sake bin ta taga ya fita da bargon.
Da Sarki ya hawo da fitila sai ya ce wa matar, “Na kashe shi, amma na ga k**ar ba shi ba ne, don wannan har yana da gemu, shi kuwa saurayi ne, bai isa tsai da gemu ba. Watakila ja’irin ne ya rikide.”
Matar ta ce, “Ya aika.”
Sarki ya duba bai ga bargo ba, ya ce wa matar. “Ina bargo?”
Matar ta ce, “Wane bargo kuma ban da wanda ka zo ka karba yanzu?”
Sarki ya ce, “Yaushe na zo na kar6i bargo?”
Matar ta bayyana masa yadda aka yi. Ko da ya ji haka sai ya yi salati, ya san abin da ya faru. Da gari ya waye ya gaya wa Waziri. Suna nan sai ga Sarkin Barayi ya zo da bargo, ya yi gaisuwa ya mika wa Sarki, ya yi sallama ya koma gida ya bar su nan suna kakabi.
Suna nan saí Limamin garin da ladaninsa s**a zo gaisuwa. Da s**a ji abubuwan da Nomau ya aikatawa sarki, sai .haushi ya k**a Liman, ya dubi Sarki, ya ce, ‘“Allah ya ba ka nasara wannan labari ai bai k**ata mu bari wadansu suji ba, kada ayi mana dariyar wauta. Abunki ne kuke yi kullum ba shawara sai kace wai komai waziri ya gaya maka ya isa. Mutum guda ya ta6a shawara shi kadai? Da kun sanad da ni wannan abu, habawa! Nomau din banza, ba cikin ’yan shekarun nan muka gama share masa majina ba?” Ya dai sami Sarki nan ya yi ta yi masa qanqanci. Ga shi ya tsufa, saboda haka Sarki ke raga masa, shi ko bai sani raga masa a ke yi ba, yana neman ya wuce gona da iri.
Liman ya fita ya bar Sarki na cizon yatsa, sai ga Sarkin Barayi ya shigo. Sarki ya dube shi a fusace, ya ce masa, “Yau da dare ka sato mini Liman, ka kawo mini shi nan gobe da safe! Aikinka na hudu ke nan.”
Sarkin Barayi ya ce, “Don wannan ta kwana gidan sauqi, ni ban ci sarautar 6arayi ba sai da na shirya.” Ya yi gaisuwa ya fice.
Da isarsa gida ’yan’uwa s**a ji abin da ya faru, sai s**a ce, “Ku bar shi, ai ba hullum a ke kwana a gado ba. Yau ko shi ne Gwamnan Barayi, ba Sarkin Barayi ba, ma ga yadda zai yi ya saci mutum.”
Sarkin Barayi dai bai ce musu kome ba, sai ya fita bakin rafi da wani sanho, ya yi ta neman qaguwa yana k**awa yana zubawa cikin sanho. Da ya cika shi fal da kaguwa sai ya dauko ya kawo gida ya boye. Ya tafi kasuwa ya sawo kyandir dauri dauri. Ya kuma sawo katuwar waga ya kawo ya gama ya ajiye. Can da tsakad dare sai ya tashi ya nufi masallaci da kayan nan nasa. To, masallacin kuwa yana kusa da gidan Liman ne. Da shigarsa masallacin sai ya yi ta fid da qaguwoyin nan yana likawa ko wannensu kyandir, yana kunna wuta daga bisa k**ar fitila, ya bi su duka ya lilliqa, ya sake su nan cikin masallaci suna yawo. Sa’an nan ya tashi ya k**a kiran salla, bayan ya bi jikinsa ya nade qal da wani farin zawwati.
Da Liman ya ji kiran salla sai ya fito yana tsammani ladan ya rude ne. Da shigowarsa masallaci sai ya ga masallacin duk ya haske, ga wadansu halicce-halicce k**ar dari sai yawo su ke yi da fitilu suna ci bayansu. Ga wani mutum kuma fari fat yana jan tasbi. Liman ya ja da baya ya buga salati, zai ruga sai Nomau ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, wajenka aka aiko ni, an ce ba don kai ba zunubin mutanen garin nan ya isa a kife su. Saboda haka aka ce in zo in tafi da kai, don mutane su ga misali daga gare ka, su kara lura da al’amarin addini.”
To, Allah ya ba ka nasara, ban taba ganin jahilin Liman irin wannan ba. Da ma ba Musulmin asali ba ne, irin mujusan nan ne da s**a tsinci Musulunci da rana tsaka. Sai ya yarda da maganar Nomau, ya durqusa gabansa ya ce, “To.”
Sarkin 6arayi Nomau ya dauko waga, ya ce, “Ga abin da aka umurce ni in dauke ka ciki, in tashi da kai zuwa sama. Shiga ciki ka yi ta salati, in ina tashi da kai.”
Liman na rawar jiki ya k**a waga ya shige ya dunqule. Sarkin Barayi ya bi bakin waga ya rufe, ya sa igiya ya layyace ram yadda Liman ko ya so fitowa ba ya iya yi. Ya daura wa wage igiya, ya yi ta janta ya nufi gidansa kuwuwuwu. Liman tun yana salati har zafi ya sa ya kasa. in sun fada dutse Liman ya ji bugunsa ya buge sai ya ce, “M.”
Sarkin Barayi ko sai ya ce, “Yi shiru! Nan sama ta biyu mu ke, mun wuce sama ta daya tuni.”
Da s**a fada wani kwari, waga ta birkice, bakin Liman ya bugi kasa qumus, ya ji zafi har ya yi kara, “Wayyo!”
Sarkin Barayi ya ce, “Yi shiru! Yi ta salati mana, mun kawo sama ta hudu.”
Kai, ya Allah ka kiyashe mu da aikin jahilci! Can Nomau na ta tikar gudu da shi wai yana tashi, sai s**a tarad da wani tabki. Nomau ya ji kwadi na ta kuka kwa, kwa, kwa, cikin tabki, sai ya ce, “An kawo sama ta biyar, ka ji ana yi maka maraba. Kai dai yi ta salati.”
Liman ya taqarqare da sâlati. Can bayan an jima s**a isa gidan su Nomau, ya buda sakin tattabarunsu ya tura Liman ciki ya rufe. Tattabaru s**a yi fafafafafafa. Sarkin Barayi ya ce, “Kwanta kurum ka yi ta salati, har Sarki ya ba da izni in isa da kai. Nan inda ka ke sama ta bakwai ke nan, wannan motsin da ka ke ji Mala’iku ne masu tashi ke maka maraba. Za ka ji suna wani abu bu, bu, ku, bu, bu, irin harshensu ke nan k**ar na tattabaru. Ni zan tafi in nemo iznin isa da kai.” Nomau ya tafi ya bar jahili nan yana ta salati, shi kuwa ya je ya yi ta shara barcinsa.
Da gari ya waye ya taho ya bude dakin tattabaru ya jawo shi, ya ce, “An ce in isa da kai. In ka lura ka ga annuri ya sake, ba k**ar na yadda muka baro duniya ba.” Ya yi ta jansa har gidan Sarki. Ya yi gaisuwa. Liman na ta alla-alla a bude shi ya ga abin da zai gani. Sarkin Barayi ya ce wa Sarki, “Ga wata ’yar gaisuwa irin tamu na kawo maka. Sai ka buda da kanka ka gani.”
Sarki ya tashi ya buda waga, sai ga Liman ciki ido wuri wuri, da tasbaha a hannu yana salati yadda Sarkin 6arayi ya ce ya yi. Ko da Sarki ya gan shi haka bai san sa’ad da ya 6arke da dariya ba. Mutane s**a yi k**ar za su suqe don dariya. Sarki ya k**a Sarkin Barayi, ya cire hular da ke kansa da rawaninsa ya nada masa, ya ce, “ Na tabbatad da sarautarka ta 6arayi. Batun aure kuma sai mun yi shawara tsakaninka da ’ya’yayenka.” Don kunya Limamin nan ya kasa fitowa sai da aka k**a shi aka kai shi gidansa.
Da aka watse Sarki ya dubı Waziri, ya ce, “To, Waziri, baki fa shi kan yanka wuya. Yaya ke nan?”
Waziri ya ce, “Ba yadda za a yi sai mu san yadda za mu yi mu rarrashi sauran su dangana, mu kuwa mu ba Kosau. Don wanda ya gina wannan gida cikin dare guda, ba mai jayayya da shi.”
Sarki ya ce, “Gaskiyarka, sai mu aika Sarkin Noma ya zo da su, su duka.” Da aka zo da su Sarki ya shiga rarrashin Jimrau da Nomau su yarda kosau ya auri ’yar tasa. Jimrau ya ce ya yarda. Nomau ya ce shi faufau ba ya yardam masa, sai dai in za a hana shi da karfi a hana shi, ya san Sarki ya bar batun adalci.
Da Sarki ya ji haka sai ya dubi Waziri. Waziri ya fusata da maganan nan ta Nomau, ya dube shi, ya ce, “Mece ce sana’arka?”
Ya ce, “Sata.”
Waziri ya ce, “To, kai ko a ranka ka ga ya yiwu a ce ’yar Sarki ta rasa wanda za ta aura sai 6arawo? In dai mu muka haifi ’yarmu, to, mun ba kosau.” Duk fada ta watse. Daga nan aka tafi aka yi ta shagalin biki.
Da gari ya waye Sarakuna s**a taru za a daura aure, sai Sarki ya ce wa Sarkin Gida ya je taska ya dauko masa kayansa na ado, da lambobinsa na girma. Sarkin Gida ya ruga. Jim ya dawo a guje, duk ya rude, jiki na rawa, ya fadi gaban Sarki, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai duk taskokin nan na tutafi ba sauran ko kyalle yau, sai wannan tsohon bargo da a ke daure alkyabbu.”
Mutane duk s**a yi zugudun suna jin abin mamaki, Sarki zai bude baki ya yi magana sai ga ma’aji kuma a guje rawani a hannu ya zube gaban Sarki, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ka ji qaina, na tuba, na bi ka!”
Mutane s**a ce, “Me ya faru haka?”
Ma’aji ya ce, “Ai yau baitulmali 6arayi sun yi masa kat, ban da ahu da na tarar bakin qofa ba abin da aka bari !’
Yana cikin ba da labari kuma sai ga Sarkin Zagi ya zubo a guje ya nufo fada, ba ko wando. Shantali zai yi masa magana sai ya ga ya durkusa gaban Sarki, ya ce, ,“Allah ya ba ka nasara, ai barga yau ba sauran doki, duk an sace!”
Sarki ya mike tsaye, sai kuma ga Jakadiya ta fito daga cikin gida, ta durqusa, ta ce wa Sarki, “Mun taru za a yi wa amarya kunshi, mun duba, qasa da bisa cikin gidan nan duk ba mu gan ta ba.”
Sai aka ga Sarki ya yi shiru. Can ya dubi dogarawa baki na rawa, ya ce, “Ku yi maza ku zo mini da Nomau!” Dogarawa s**a zuba a guje s**a nufi gidan Sarkin Noma. Jim kadan s**a dawo, s**a ce, “Ai an ce rabonsa da gida tun jiya da dare.” Sarki ya baza mutane cikin kasa aka yi ta nema, amma ko duriyarsa ba a ji ba.