Hausa News Report

Hausa News Report Dan samarda ingantattu Kuma sahihan labarai daga fadin duniya cikin harshen Hausa

Hakakuma kaima/kema kinada damar kawo lavari,inda halima mutum zai iyasaka hotuna dandai agamsu,kuma dan Allah banda batawa wani mutum ko kungiya suna

08/05/2024

Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karbar la'adar ajiya da bankuna ke yi a hannun abokan huldarsu. Bankin na CBN ya bayyana hakan ne a wata sanarwa.

08/05/2024

Hukumar jami'ar ilimi, kimiyya da fasaha ta jihar Ekiti ta kori ɗalibai.mata biyu bisa laifin dukan da aka yi wa wata ɗaliba a wani faifan bidiyo da ya bazu a X.

08/05/2024

Yan sandan jihar Ogun sun sanar da kashe masu garkuwa da mutane biyu tare da kwato kudin fansa naira miliyan 7.9. Sun kuma sanar da cewa suna kokarin kamo sauran.

26/04/2024

Sojjojin kasar Burkina Faso sun dakatar da gidajen rediyon BBC da VOA daga watsa shirye-shirye na sati 2 saboda yada labarin kai hari kan fararen hula

26/04/2024

Babbar kotun jihar Kogi ta umarci shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya hallara a gabanta kan saɓa doka da ya yi kan binciken tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.

16/04/2024

Rahotanni sun tattabar da cewa ragowar daliban da aka yi garkuwa da su a jami'ar tarayya ta Gusau sun samu 'yanci bayan shafe watanni a hannun masu garkuwa da mutane

16/04/2024

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya bawa jami'an tsaro umarnin harbe 'yan daba nan take tare da sanya dokar ta baci a jihar. Dokar ta biyo bayan wani hari ne a jihar

16/04/2024

Kasar Amurka ta gargai Isara'ila kan sake takalo yaki da Iran sakamakon gudun tada yaki a gabas ta tsakiya. Amurka ta aike sakon ne wa Isara'ila ta wayar tarho

16/04/2024

Wasu miyagun ƴan bindigan daji sun je har ƙofar gidan sakataren jam'iyyar PdP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, Musa Ille, sun harbe shi har lahira.

16/04/2024

Sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan ta'addan ne a garin Maru a jahar Zamfara bayan sun yi kazamin fada. Sun kuma kwace makamai da dama wurin 'yan ta'addan

16/04/2024

Jam’iyyar NNPP bisa amincewar mahukunta ta dakatar da gwamna Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano na tsawon watanni shida kan zargin ayyukan zagon kasa.

16/04/2024

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnoni na amfani da hukumomin zabe na jihohi domin tafka magudin zabe.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa News Report posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa News Report:

Share