16/09/2025
TARIHIN TAKUTAHA DA LOKACIN DA AKA FARA YIN YA A KANO TUN ƘARNI NA 13TH MILADIYYA.
Hawan Dala da ake da Mauludi a Tarihin Kano shin yaushe aka soma
Asali, kusan shekaru dubbai da s**a gabata, Kano ba gari bane da ke da Tsarin mulki ba, Shirayi(mazauni) ne kawai, kamar yadda marubucin wakar Bagauda ta Kano ya bayyana. Birnin Kano a wannan lokaci ya shahara ne a matsayin wurin bauta, dake cike da addinai kalakala. Wadanda s**a hada da ; masu bautar ruwa, wadanda ke zaune a Bakin Ruwa, kuma asalinsu sun taso daga kasar Gaya ne. Wadannan suke ke bautar ruwan jakara. Kuma sun amince shine yake tsaresu daga dukkan wani balai da zai taso musu, ko kuma ya taso ma garinsu.
Wani nau'in addinin shine Adzna ko Arna. Wadanda ke Gwabron Dutse. Su wadannan sune masu bautar Ubangiji. Wato wani Allahnsu ne da suke bautawa, Wanda a zatonsu yana ko ina. Haka kuma suna da gumaka da suke bautawa a matsayin wakilan Shi wannan ubangiji. Ita wannan kalma, ita ce malaman musulunci s**a amsheta, s**a nuna cewa ba Wanda ya cancanci wannan siffa ta ubangiji in banda Allah (domin shine yake ko ina, ilminsa ya game komai).
Addinin da yafi kowanne karfi da shahara, kuma manyan sarakunan kasar Kano dake da helikwata a Santolo suke bi, shine addinin maguzanci. Wanda babban wurin bautarsu ke kan Dutsen Dala. Masu bin wannan addini su ake kira Maguzawa, Farfesa Murray Last a kasidarsa maitaken : Historical Metaphor in the history of Kano ya bayyana cewa asalin sunan, ya samo ne daga "Majus " wato majusawa. Wadannan bayin Allah na bautar iskokai ne, wato aljannu. Musamman wata aljanna da ake kira Tsumburbura, ko kuma Danko. Malam Adamu na Maaji ya bayyana a littafinsa I'lan bi Tarikh Kano cewa, asalin wannan aljan ana bauta mata tun zamanin Annabi Nuhu, inda ya tabbatar da cewa ita ce 'Yaquqa ' da aka fada a alqurani, cikin suratul Nuh.
Akwai kuma masu bautar Bishiya da aka fi sani da Gazargawa, wanda sheikh AbdurRahman Zagaiti ya sha fama da su. Sune ke zaune a Shirawa, akwai cikakken bayani akan wannan rigima a kundin nan maisuna: Waraqa makatuba, fiha asl al wangariyun ".
Akwai sauran addinai da dama wanda Malam Nasiru Kabara ya yi dogon bayani akan su, a wani kaset na waazinsa da ya Maida martani ga malaman Izala akan gudunmowar sufaye a wurin yada addinin musulunci a Kasar Kano. (Abin bakin ciki na nemi kaset din na rasa).
Dokar kasar Kano a wannan lokaci shine: tunda kasa ce mai tsarki ta gamayyar addinan Hausawa, da suke aikin hajji duk shekara acikinta, kuma malamnsu da limamansu duk na ciki, to baa yadda kayi noma acikinta ba, ba kuma a yadda kayi farauta acikinta ba. Duk yayi wannan to zaiyi fuskantar fushin Allolinsu ko kuma ya fuskanci yaki daga Sarakan Kasar dake zaune a Santolo (wato Tsakuwa kenan dake karamar hukumar Dawakin Kudu a yau). Wannan dalilin ne ya sanya Shi kansa limaminsu mafi shahara (Barbushe), yake tafiyar wuni domin ya farauto nama. Saboda ba damar yin farauta a garin Kano da kewaye. Hakan ta sanya kqbilar Doma s**a bar gari saboda mafarauta ne, s**a koma Kazaure, karkashin jagorancin shugabansu maisuna Kazaure.
Yunkurin Bagaudawa;
Farkon Wanda s**a fara yunkurin rusa wannan addinai sune Abagayawa, asalinsu makera ne da manoma, s**an kuma taba farauta. A wannan lokaci saboda bukatar sabon wurin noma da kuma neman karfe domin kara fadada sanaarsu, ta sanya dole su fara neman sabon wuri, inda zasu samu kasa mai yalwa, da kuma isasshen karfe. Ba kuma inda yake da wannan abubuwa in ba Kano ba. Gashi kuma ba a noma a kasar Kano, kuma baa farauta, ba kuma dama a haki ma'adanan ta. To amma fa, dan wuya ba za a bar dadi ba.
Zuwan Bagauda Kano ya tabbatar da shi fa yaga, domin yaga akwai karfe a kasa, ga kuma kasar noma mai albarka, sannan ga dabbobi kala kala. Don haka ya yanke shawarar Shi fa, sai dai ayi wacce zaayi, amma dole a barsu, su cigaba da rayuwa a kasar Kano. Kuma dole su noma kasa, dole su hako karfe, dole kuma a barsu suyi farauta, don ba zasu bar nama a banza ba.
Wannan yunkuri na Bagauda da mutanensa, ya jawo musu tsangwama daga sarakunan Santolo da kuma tofin Allah tsine daga manyan limaman Kano. Koda yake da farko Bagauda ya keta doka yayi yanda yake so, amma ba a jima ba Santolo ta zo da runduna mai karfi ta fatattake shi, inda ya sha da kyar, ya tattara yanasa-yanasa ya koma Sheme a kasar Kazaure, acan ya rasu!
Sai dai wannan fatattaka da akayi masa ya bar baya da kura, domin ya haifar da gadajjiyar gaba tsakanin Bagaudawa da manyan addinan Kano, inda s**a sha alwashin ko bajima, ko badade, sai sunga bayan wadannan addinai. Sun shafe kusan shekara 100 da doriya suna mulki a kasar garin sheme na Kazaure, kafin daga baya dama ta samu a zamanin Gijimasu su ka dawo su ka kafa gidan sarauta a birnin kano.
Bawani cikakkiyen bayani, akan ko ya akai s**a dawo, cikin Kano, domin kundin Tarikh Arbab bai bada wani bayani cikakke ba akan yadda s**ayi nasarar dawowa cikin garin Kano, da maido da masarautarsu, amma alamu na nuna cewa, a wannan lokaci karfin Santolo yayi rauni ainun! Kila ko saboda yake yake da ya addabe su, musamman da daulolin Tumbi da kuma Washa, ko kuma da Zazzau. Kila hakan ne ya sanya aka bar shirayin Kano ba wani tsayyayen tsaro da zai kareta, daga mamayar Bagaudawa.
Koda yake Bagaudaw sun dawo Kano, amma kuma sai ga shi basu samu yadda suke so, na murkushe tsoffin abokan gabarsu ba. Duk wani yunkuri da s**a yi na tabbatar da mulkinsu, abin yaci tura. Shi kansa Zamnagawa (usmanu) da yayi yunkurin farko, bai kare lafiya ba.
Yunkurin Musulunci
Acikin wannan hali ne, a wata shekara zamanin sarkin Kano Yaji dan Tsamiya, wasu malaman Wangarawa karkashin jagorancin sheikh AbdurRahman Zaiti s**a zo, Kano, baya ga musulunci da kuma kasuwanci, suna kuma da sabbin makamai da dabarun yaki da baa san da su ba a Kano. Wannan ya sanya Bagaudawa s**a karbi musulunci, gami da neman samu hadin kan wadannan baki, su taimaka musu su yaki abokan gabarsu. Kwana daya da zuwansu Sarkin Kano Yaji ya karbi musulunci, ya kuma canjawa kansa suna zuwa Ali. Wanda hakan ke nuna, cewa , shirin yaki za'ayi dan tabbatar da Addinin Allah, domin ana cewa Ali bin Abu Talib shine sarkin yakin manzon Allah (saw).
A farkon watan Rabiul Awwal na wannan shekara, ne Yaji ya tara dukkan Hausawan da basu musulunta ba ya karanta musu dokar-ta-baci. Inda yace musu
"Ku sani, daga yau, ba komai tsakanina daku, sai yaki da tsinin mashi in har ku ka cigaba da yakar musulunci ba yaudara, bawani boye boye, domin ba mayaudari sai matsoraci, ku shirya gani nan zuwa gareku "
Mataki biyu s**a dauka, na farko sunyi kokarin bada cin hanci ga Sarki Yaji, amma yaki karba, yace a maida musu baya so. Na biyu, sai s**a koma ga Tsumburbura, domin neman nasara, amma ta gaya musu, cewa wannan yaki ba nasara, domin lokacin karshen addininsu a kasar Kano yazo.
Acikin watan dai, rundunar musulmi s**a fuskanci, rundunar mabiya addinin gargajiya,a gefen Dutsen Dala, inda s**a hadu, aka gwabza. A wannan lokacin ne, Jarmai Bajere ya samu nasarar Kutsa kai cikin shigifar Tsumburbura, inda ya samu wani halitta na tsaye, rike da maciji a hannunsa, ya daga mashi ya bugawa halittar nan, tayi kuwwa ta fito a guje wannan yaƙi ya faru ne a Ranar 19th ga Rabi'ul Awwal wanda kuma yayi dai-dai da Ranar bakwai ga haihuwar shugaba sallahu alaihi Wasallam. Bayan fitar wannan halitta sai Nan da nan s**a bita, inda ta nufi kofar liƙwai wato kofar ruwa a Yanzu, ta fada cikin ruwan Dankwai. Wannan Shi ya kawo karshen Tsumburbura, da kuma addinin gargajiya (maguzanci)a garin Kano a lokacin Mulkin Sarkin Musulmi Ali yaji ɗan Tsamiya a ƙarni na 13th.
Takutaha
Samuwar wannan Nasara, ba karamin abu bane a wurin musulman Kano. Wanda aka shafe sama da shekaru 100 ana nema. A dalilin haka ne, ya sanya musulman kanawa duk shekara, s**an taru su hau Dutsen Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci. Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe addinin kafirai. Domin kafin zuwan musulunci, ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci, yanzu kowa ma sai ya hau, ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake takutaha a duk shekara a Kano, Wanda wasu da basu san tarihin ba, ke ganin jahilci ne, ko kuma abu ne, da ya sabawa musulunci.
Allah ya sa mu dace