10/12/2025
BA'A YI MANA ADALCI BA!
Sanata Abdul Ningi ya koka kan cire masa Dogarin dansanda!
A zaman majalisar dattawa na yau Laraba, an ga fushin sanatoci bayan Sanata Abdul Ningi ya tayar da batun cire masa ɗansanda guda ɗaya, duk kuwa da cewa wasu manyan jami'an gwamnati da ’ya’yansu da ’yan kasuwa har da mawaka suna ci gaba da amfani da ’yan sanda masu dauke da mak**ai a matsayin tsaro.
Sanata Ningi, yayin amfani da Order 42, ya zargi cewa an yi amfani da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 23 ga Nuwamba wanda ya bukaci a maida ’yan sanda zuwa ayyukan su na asali — don a muzgunawa ƴanmalisar, yayin da wasu manyan mutanen ke ci gaba da jan dogayen ayarin tsaro.
“Na ga ministoci biyu jiya da dogayen ayarin tsaro. Na ga ’yan kasuwa, ’ya’yan manyan masu mulki, har ma mawaka suna da tsaro. Amma ni Sanata mai aiki shekaru da dama — ɗan sandana guda ɗaya aka janye min,” in ji Ningi.
Ya ce ya amince da sabuwar manufar gwamnati kan tsaro, amma sai an aiwatar da ita daidaito ba tare da nuna bambanci ba.
A cikin martaninsa, Mataimakin Shugaban Majalisa, Sanata Jibrin Barau, ya tabbatar da cewa shugabancin majalisar ya tattauna batun tun ranar Talata, kuma an ɗauki matakin da zai dawo da orderlyn Sanata Ningi.
Ya kuma ba da umarni ga Kwamitin Harkokin ’Yan Sanda ya binciki yadda wasu mawaka, ’yan kasuwa da ’ya’yan manyan jami’an gwamnati ke ci gaba da gudanar da ayarin tsaro duk da umarnin Shugaba Tinubu.
Barau ya yi nuni da cewa manufar Shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga manyan mutanen an yi ta ne domin ƙarfafa aikin rundunar cikin gida, yana mai cewa majalisa na goyon bayan gwamnati akan haka, amma dole a yi komai bisa ka’ida da adalci.