29/11/2025
29/11/25
Majalisar Zartarwar jihar Kano Ta Amince da Naira Biliyan 54.8 Domin Manyan Ayyuka a Sassa Daban-Daban na jihar Kano.
Bayan tattaunawa mai zurfi kan muhimman al’amuran gudanarwa, Majalisar Zartarwa ta amince da abubuwa da yawa daga cikin muhimman shawarwari na ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na jihar Kano.
An amince da adadin kudi ₦54,798,217,384.19 domin aiwatar da wadannan ayyuka.
Ga yadda aka rarraba kudaden zuwa ga sassa daban daban:
1. SASHEN ILIMI
Gwamnati ta sake jaddada kudirinta na inganta makarantun gwamnati musamman na fasaha da na firamare.
Jimillar kudin da aka amince a sashen ilimi shine ₦4,680,187,008.16, ta hanyar wadannan ayyuka:
1. Karin aikin gyare-gyare a GTC Dambatta – ₦242,011,541.88
2. Karin gyare-gyare a GTC Ungogo – ₦188,428,006.10
3. Gyaran makarantar Falgore Primary School tare da kayan more rayuwa – ₦167,428,123.59
4. Mayar da kudaden da aka ware wa CRC zuwa SUBEB domin gyaran makarantu da samar da kayan aji – ₦1,891,985,000.00
5. Siyan kujeru da tebura ga Kananan Hukumomi 13 – ₦1,000,000,000.00
6. Biyan kason da ya rage na kayan ɗakunan karatu 34 – ₦190,605,836.00
7. Ayyukan gina ajujuwa da gyare-gyare domin fara karatun Polytechnic Gaya – an haɗa su a sashen ayyuka da manyan makarantu.
2. MANYAN MAKARANTU (Higher Education)
1. Siyan motocin aiki ga kwamitin kafa Polytechnic a Gaya – ₦345,000,000.00
3. SASHEN Kula da LAFIYA (HEALTH)
An amince da ayyuka domin ƙarfafa rigakafi da kiwon lafiya matakin farko:
1. Ayyukan rigakafi na Q4 2025 – ₦344,731,419.00
2. Gyaran PHC Malikawa Garu da Malikawa Sarari Health Post, Bichi – ₦522,914,486.8
Jimillar kuɗin Sashen Lafiya: ₦867,645,905.87
4. Sai bangaren RUWAN SHA (Water Resources)
Kudaden da aka amince da su domin bayar da wutar lantarki da samar da mai:
1. Biyan kudin lantarki ga KEDCO – Satumba 2025 – ₦214,240,393.05
2. Siyan Diesel – Oktoba 2025 – ₦153,400,000.00
3. Siyan Diesel 120,000l da PMS 17,000l – ₦288,515,480.00
4. Siyan Diesel 100,000l – ₦260,000,000.00
Jimillar kuɗin Ruwan Sha: ₦916,155,873.05
5. SASHEN AIYUKA DA GINE-GINE (Works & Infrastructure)
Wannan sashen ya samu mafi girman kaso – sama da ₦39 biliyan.
Daga cikin ayyukan da aka amince da su akwai:
– Aikin titin Unguwa Uku–Yanwaki–Limawa – ₦352,964,168.05
– Ƙarin kuɗi da gina kotunan Shari'a 4 – ₦428,522,234.01
– Gyaran gidan Governor a Kwankwasiyya – ₦249,058,296.40
– Gina gada mai span 3 a Rogo – ₦5,279,560,621.59
– Titunan Gama – ₦3,285,725,696.72
– Titin Sarkin Yaki Fagge – ₦2,606,388,055.53
– Gyaran Independence Road – ₦3,548,978,367.49
– Titin Sokoto/Iyaka – ₦3,983,628,095.10
– Titin Rano–Saji – ₦4,981,950,431.41
– Gyaran Zaria Road – ₦2,108,603,250.00
– Titin Sabuwar Tasha zuwa Ring Road – ₦2,248,190,680.94
– Kayan gida a gidan Mataimakin Gwamna – ₦444,529,428.07
– Ayyukan fara Polytechnic Gaya – ₦3,190,779,669.85
– Kafa traffic lights – ₦2,121,895,215.50
– Ayyuka a Governor’s Wing (Phase I & II) – kusan ₦2.4 biliyan
– Kayan ofis da gyare-gyare – ₦318,027,454.62
6. GINE-GINEN MULKI & BIRANE (Housing & Urban Development)
1. Kafa Cibiyar Gaggawa a Government House – ₦1,004,342,689.86
2. Ginin gidan Chief Judge – ₦440,618,554.38
3. Gyaran Protocol Lounge a Filin Jirgin Sama – ₦192,538,439.38
4. Ginin dakunan kotu 3 da ofisoshi a Audu Bako – ₦663,555,718.51
5. Gyaran Islamiyya a Kwankwasiyya – ₦585,839,353.00
7. KANANAN HUKUMOMI
– Kammala titin 5km da ƙarin tituna a Gaya – ₦5,557,757,168.91
8. OFISHIN SAKATAREN GWAMNATI
– Biyan bashin Royal Tropicana Hotel – ₦150,000,000.00
10. SAURAN AIYUKA (Procurement & ICT)
– Kafa tsarin e-Procurement (Phase I) – ₦385,600,000.00