
19/06/2025
Mun kai hari ne kan hukumar leƙen asirin sojin Isra'ila ne ba asibiti ba in ji Iran.
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa hare-haren da ta kai a safiyar Alhamis sun nufi cibiyoyin leƙen asirin soja na Isra’ila a kudancin ƙasar, ba asibiti ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai s**a bayyana.
Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ce an kai harin ne kan hedikwatar rundunar sadarwa da kuma wata cibiyar leƙen asiri, sai dai fashewar bam ɗin ta shafi wani asibiti a kusa da wurin.
A gefe guda kuma, Isra’ila ta kai hari kan matatar ruwa ta Arak da ke Iran, amma an kwashe ma’aikata kafin faruwar lamarin.