24/10/2025
SHIN YAUSHE DUNIYA TA SOMA, DA KUMA HALITTAR DAN ADAM NA FARKO? ADDINAI DA DAMA SUNYI BAYANI A KAN HAKA.
🕌 ISLAM
Addinin Musulunci, Al-Qur’ani mai tsarki bai bayyana shekarun da duniya ta fara ba, haka kuma bai faɗi shekarar da aka halicci Annabi Adamu (AS) ba. Abin da aka sani shi ne Allah ya halicci sama da ƙasa cikin kwanaki shida, amma waɗannan kwanaki ba lallai su zama kwanaki irin na duniya ba, domin a wurin Allah lokaci daban yake. Don haka, Musulmai na cewa halittar duniya ta faru cikin tsari da hikima, da kudirar ubangiji ba tare da adadin shekaru tabbatattu ba.
Sai dai Ibn Kathir ya yi cikakken bayani kan farkon halitta:
Ya ce Adamu shi ne mutum na farko.
Allah Ya halicce shi daga turɓaya.
Bayan haka ne ya halicci Hauwa’u daga shi.
Sun zauna a Aljanna kafin su sauka duniya.
Amma Ibn Kathir bai taɓa ambaton shekara ko lokaci na duniya ba , ya ce “Allah ne mafi sani”.
✡️ YAHUDANCI (JUDAISM)
Yahudawa suna ganin duniya tana da shekaru kusan 5,786 a yanzu. A ƙididdigarsu, halittar Annabi Adamu ta faru ne a shekara 3761 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Wannan lissafi ya fito daga Littafin (Genesis), inda s**a haɗa shekarun da annabawa s**a rayu. Saboda haka, a ra’ayinsu, duniya ta fara shekaru ƙasa da 6,000 da s**a wuce.
✝️ KIRISTANCI (CHRISTIANITY)
Kiristoci da dama, musamman na gargajiya, sun gaji ƙididdigar Yahudawa. Malamin coci Bishop James Ussher ya ce Allah ya halicci duniya a ranar 23 ga Oktoba, shekara 4004 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Wannan ya sa wasu Kiristoci ke ganin duniya tana da kusan shekaru 6,000. Amma Kiristoci na zamani da dama sun rungumi bayanan kimiyya, suna ganin “ranaku shida” na halitta a Bible na nufin matakai ne, ba kwanaki na zahiri ba.
Raayin Kiristocin Gargajiya sunce halittar Adamu ta faru kimanin shekaru 4,000 kafin haihuwar Annabi Isah
Raayin Kiristocin zamani( masu lakari da kimiyya) dan Adam ya wanzu kimanin shekaru 200,000 zuwa 300,000 da s**a gabata
🕉️ HINDUISM
Addinin Hindu yana ɗaukar cewa duniya tana rayuwa cikin zagaye na lokaci da ake kira Yugas. Kowanne zagaye yana ɗaukar shekaru biliyan 4.32, sannan duniya tana lalacewa ta sake kafuwa. A halin yanzu, ana cikin Kali Yuga, wani zamani na ƙarshe da aka ce ya fara a shekara 3102 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Don haka, a ra’ayinsu, duniya tana da tsawon lokaci mara iyaka, tana sake kafuwa da lalacewa sau da dama.
Sannan A Hinduism, babu mutum guda da ake kira “mutum na farko” kamar Adamu.
Amma akwai labaran Manu, wanda ake ganin shi ne mutum na farko da ya tsira daga ambaliyar ruwa (kamar labarin Nuhu), wasu ma Sunce Annabi Nuhu ne.
Manu ana ganin shi ne “Uban ɗan adam” a fassarar Hindu.
Hindus suna ganin ɗan adam yana sake haihuwa (reincarnation) a cikin waɗannan zagayen lokaci, rai ba ya bacewa, sai dai yana komawa cikin sabon jiki.
🔬 KIMIYYA (SCIENCE)
Masana kimiyya sun gano cewa duniya tana da shekaru biliyan 4.54, bisa ga nazarin duwatsu da kayan taurari. Mutum irinmu (Homo sapiens) ya farane shekaru 200,000 zuwa 300,000 da s**a wuce a Afrika ta gabas. Kimiyya ba ta amfani da ruwayoyi ko littattafai, sai hujjojin zahiri kamar duwatsu, ƙasusuwan tsoffin mutane, da nazarin DNA.