MATAN Sunnah

MATAN Sunnah Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MATAN Sunnah, Publisher, Kano.

25/10/2020

😂😂

04/12/2018

MATAN SUNNAH.
abin mamaki ya tabbata ga macen datake suturta jikinta saboda tsoron sanyi, amma bata suturta jikinta saboda ALLAH.
For more visit

30/07/2018

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

SUNA: Bayan Duhu

Fitowa ta 9

30-July-2018M

DAGA TASKAR: Hadiza Balanti chediyar yan gurasa.
___________________________
Budurwa balagaggiya, ita ce wadda hankali da tunani s**a tabbata a kanta sha’awa da danshin mata s**a farmata, mai sanin sauyin lamari da gamsarwa da fahimtar yadda al’amura ke wakana, da sauyin yanayi.

Amma mace akasin haka mara karfin sha’awa sanadiyar rashin nukuwa da danshin mata, sanadiyar raunin inganci da matanci, zata iya zama mai azabtuwa da kuntata a yayin gamaiya.

Kuma wannan takurar zata haifar da kiyayya tsakanin ta da mijinta, kiyayya ta har abada.

Domin azabtuwa sanadiyar saduwa matsalace, kamar yadda hakan yake zama silar tsagewa da hujin mahaifa.

Wani sa’in yawan bari ko mutuwa a gun haihuwa.

Akan samu wasu matsaloli haka siddan da s**a bijiro ga mata ta fannin halaye ko dabi’a, kamar ta hanyar gado, ko kuma matsalar ta samu a rashin sani tun yarinta.

Irin wannan matsalolin sun hada da talewar matanci da rashin ni’ima, da matsanancin ciwon kai ko mara a lokacin al’ada, saurin sakin jiki da zubewar nonuna da karanci ko rashin sha’awa ko fargaba kullum da tsauri ga miji a yayin gamaiya.

Abin takaici shine yadda mata galibi har yanzu basu farga da cewar jam’in matsalolin kwayoyin cuta ne na zahiri, duk da cewa tasirin su a badini yake.

Kasancewar shine jigo na biyu bayan shafar aljanu da rashin tarbiyya wanda yake murkushe auren ya kuma hallaka tafarkin ma’aurata, baya ga dagulewar al’amura da jallin kashe kudi wajen neman magani idan kenan an farga da wuri da fahimtar matsalar da sanadinta akan gaba.
____________________________
Zaku iya kasancewa tare damu da dukkan aikace-aikacenmu, ko tuntubarmu ko aiko da shawarwari da tambayoyi, ta wadannan hanyoyin dake kasa;

SAKON KIRA DA WHATS’APP: 0812 222 8484

E-MAIL: [email protected]


https://www.dakeake.com

12/07/2018

Mace musulmah, muminah , bata bukatar Auren namiji, wanda a kullum yake kewatar da ita da Abubuwan duniya kawai, da nuna mAta jindadi na duniya da kyalekyalen ta kawai.

Tana bukatar ne ta auri miji, musulmi, kamili, WANDA yake tausayin ta, WANDA yake bata farin ciki , WANDA a kullum yake kara kusanta ta ga Allah, WANDA zai riki hannayen ta zuwa Aljannah.

WANDA a kullum zai dunga Tuna mAta akwai ranar sayuwa a gaban ubangiji.

Wanda a kullum yake mata addu'a, da sanya mata albarka.

WANDA Idan tayi masa laifi zai yafe mata, sa'annan ya nuna mata Soyayya tsanani da Allah.

Wanda zai bata abinci safe da yamma, ta hanyar halal.

Mai tsafta , mai iya magana, mai daraja iyayen ta da yan uwanta.

Mai kamewa daga matan banza, mai fada mAta gaskiya , mai yawan murmushi, da iya magana.

Mai karantar da ita, WANDA in tayi laifi zai kirata yace ta gyara, wanda in tayi fushi zai rarrashe ta, sa'annan yaji dalilin fushin.

Mai rike sirri, mai amana, mai kyawawan Hali, da riko da sunnah .

Mai siya mAta tufafi, mai kishin ta, mai nuna mAta yana qaunar ta

Mai wasa da dariya. Mai nuna mAta ita kyakkawa ce , wanda ya iya tsokana, wanda yake shagwabantar da ita.

âœđŸ» *Fatima* *Shamsu* *Gwadabe* *Daughter* *Of* *Islam*

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY Sunan shirin: BAYAN DUHU DAGA TASKAR: Hadiza Balanti chediyar yan gurasaSHIMFIDA:Dukkan Godi...
26/04/2018

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

Sunan shirin: BAYAN DUHU

DAGA TASKAR: Hadiza Balanti chediyar yan gurasa

SHIMFIDA:
Dukkan Godiya da yabo da kirari da jinjina da bambadanci da roko tare da daga hannu sama sun kebantu ga Allah madaukakin sarki, sarki Allah mahalicci, mahakurci, makadaici, mawadaci, majibinci, mabuwayi, mai Rahma mai jin kai, wanda bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba, sannan babu wani abin halitta da ya zama kini ko tamka a gareshi.

Tsira daraja da aminci su kara tabbata ga masoyin mu mai ceton mu Annabi dan gatan Allah cikamakin Annabawan Allah da Manzonni, manzo Sallallahu alaihi wa sallama, tare da alayensa da dukkanin sahabbansa da salihan bayi masu bin tsarin koyarwarsu sau da kafa cikin kyautatawa har izuwa ranar karshe.

Yan uwana masu albarka muna karanta muku gaisuwa ta kauna da addu’a tare da fatan alkhairi a gareku, da farkon fara haduwarmu daku a yau, a wannan sabon shiri mai albarka na BAYAN DUHU

“Allah ka taimakemu akan duk abinda zamu zaiyano ya zama daidai ga mai karatu kuma ya amfanar dasu, musamman yan uwana mata.

Allah muna rokonka kar ka jarabcemu da abinda ba zamu iya ba, kuma Allah abinda muka sani kar ka sa ya zama musiba a garemu Amin”.

Allah Subahanahu wa ta’ala ya halicci mace a matsayin jinsi mai zaman kansa, mai dauke da martabobi bila-adadin, darajarta tana misaltuwa ne a matsayin sutura wadda ta zama wajibi a kula da ita kasancewarta ginshikin rayuwa kuma gishirin al’umma, mace alkibla ce mai zaman kanta dangane da koyarwar addinin musulunci.
____________________________
IN DAI ANA BIYE DAMU CIKIN NUTSUWA DA FAHIMTA, ABINDA YAFI WANNAN BAYANI YANA NAN TAFE A MAKON GOBE, IN SHA ALLAH, DA FATAN ZA'A YI MANA ADDU'A.
____________________________
Zaku iya kasancewa tare damu da dukkan aikace-aikacenmu, ko tuntubarmu ko aiko da shawarwari da tambayoyi, ta wadannan hanyoyin dake kasa;

https://www.dakeake.com

https://www.twitter.com/dakeake

https://www.instagram.com/dakeake

https://m.facebook.com/dakeakeglobal

htt

We make a woman feel like a real woman

21/04/2018

Yadda ake razanar da yaro
Daga: Aminu Bashir Aminu (ABU MUS’AB MEDILE)
Daga lokacin dakake nunawa yaro idan kanason hanashi wani abu kana kokari wajan cewa ga dodo nan ko makamancin wani abu oh wannan lokacin zai dinga tsorata amma fa kasani dazarar yayi wayo yagane babu wani dodo ko kamashi ko sauran wasu abu. Zaice ashe ma duk karya ne zai cigaba da aikata wannan abun. Abinda yakamata, mukuyarda yaran mu shine tsoron ALLAH idan yayi laifi kanayi masa nasiha kadinga yawan ce masa kasani duk abinda kakeyi Allah yana kallonka kuma kaji tsoransa. Toh wannan zaiyi tasiri har cikin zuciyarsa kuma zai dinga tunawa idan ya tashi yin abu zaice Abba yace Allah yana ganina. Kuma wataran kaima zai tunatar dakai idan yaga kasauka daga kanrayi. Yadawo dakai kan gaskiya.
kamar yanda yazo awata hikaya, anyi wani mahaifi ya koyar dashi akan dukkan wani abu dazaiyi Allah yana kallon sa. Rannan sai rayuwa ta canja babu abinci a wannan gidan sai mahaifinsa yajashi suje gonar wani bawan Allah da zuwansu wannan gona sai mahaifinsa yace zanhau bishiyar sai dinga tsinkuwa ina baka kana tare mana, yace to sai yace gana ganin wani kagaya min yaro yace,
Mahaifinsa kuwa ya haukan bishiyar nan yana jefomasa, can sai yaro yace baba gawani nan mahaifin nan yai maza cikin rawar dari ya sauko. Sai ya tambaye shi ceawa ina wanda yake ganin mu. Sai yace baba bakace komai muke Allah yana ganinmu ba. ALLAHU AKBAR nan take wannan mahaifin a juya da baya yana neman Afwar ALLAH.

14/04/2018

Sheikh Yusuf Usman Kofa Yayi bayani akan cewa babu wani gari a duniya da ake zuwa ziyara a wannan ziyarar anashan wahara. duk shan wuyar da akeyi haka duk shekara zakaji wanda yaje wannan ziyara sai yaso ya dinga komawa wannan kasa.
duk wanda yaje aikin hajji yana bada labarin irin wuyar daya sha. amman wata shekara sai yaso ya kuma.
daga
Aminu Bashir (ABU MUS'AB MDL)
https://www.facebook.com/Masjidul-ANSAR-Medile-1749882705037484/

DARUL IRSHAD ISLAMIC PROPAGATION

16/12/2017

Ga Maison shiga group namu na Whatsapp
+2349039417200

TUNATARWA NASIHA               FADAKARWAALLAH yana cewa:  FAZAKKIR FA INNAN ZIKRA TAMFA’UL MUMININNa saurari wani karatu...
15/12/2017

TUNATARWA NASIHA FADAKARWA
ALLAH yana cewa: FAZAKKIR FA INNAN ZIKRA TAMFA’UL MUMININ
Na saurari wani karatu na MAL Yusuf Tijjani Gurumtum, wannan yasa nace ya kamata na bada gudummawa wajan rubuta wannan zinariyar shawara. Saboda yawancin mu bamu da tunani irin na malamai.
Haka akwai Nasiha ta Sheikh Ja’afar Mahmud Adam( R.T).
Wanda Ni AMINU BASHIR yasa nayi kokarin wajan haka
Yar’uwa ki nutsu ki karanta insha ALLAH zai miki amfani anan Duniya da kuma Lahira.
ZAkuji bayanai masu mahimmanci wanda duk wanda ya dauka, zai sami Rayuwa mai dadi. Amatsayin kin a budurwa shin kina wannan tunanin.
Ki bada mahimmanci wajan karantawa. Kuma bas au daya ba.


BISMILLAHIR RAHMANUL RAHIM
GODIYA TA TABBAT GA ALLAH SUBHANAHU WATA’ALA MAI KOWA MAI KOMAI.
DUBUN SALATI YA TABBATA GA CIKA MAKIN ANNABAWA SALAWATULLAHI WASALAMUHU ALAIHI.
AMMA BA’adh

Wajibine akanki ku Mata ku tashi kufuskanci kalubalen dake gareku.
Maganar rayuwarki ba maganar maganar text massage bace ba maganar flower bane.
Magana ne naki tashi kiceto rayuwarki abisa tsarin da ALLAH ya halicceki.
Babu wani mutum da rayuwar sa takusa fadewa hatsari adaidai wannan lokacin sama da ‘ya mace, saboda dalili idan kakasa mata kasha goma (10) kashi tara basu san itace wacce ita ba.
Abu nafarko ‘yan uwana mata ku tashi ku fuskanci kalubalen dake gareki.
Ku bawa kanku kariya a rayuwarku ta duniya data lahira daga fadawa mummunar makoma. Wanda bama fatan haka insha ALLAH.
Na biyu kiyi taka tsantsan iyaka matuka wajen zabar mijin dazaki aure.
Karkiyar da ki sadaukar da kanki wa gurba tacciyar Soyayya
Karkiyar da ki sadaukar da kanki ga soyayyar da batada manufa.
Kiyiwa kanka fada zauna kiyi tunani ki kalli makomar ki a wannan rayuwar.
Kima kanki fadan ta nutsu wannan watsi da kanki da k**eyi ke zaki dandana gubar wannan bayyanar daji kinki da k**eyi a banza zakiyi dana sani cikin rayuwarki,bashi k**eci dan zaki biya wannan bashin.
Ki kalli makomar ki a wannan zamanin ki kalli yawan ZAURAWA da k**e

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MATAN Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category