01/12/2025
BADARU ABUBAKAR YAYI MURABUS DAGA MINISTAN TSARON NIGERIYA
A wata wasika wacce ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, Abubakar ya bayyana cewa ya ajiye aiki ne saboda dalilai na rashin lafiya.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin, tare da gode masa kan hidimar da ya yi wa ƙasa.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da majalisar dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru a mako mai zuwa.