05/08/2025
Na Taso Rayuwata Cike Da Tausayi Da Son Mutane. Mahaifina Ya Rasu Tun Ina Karama, Mahaifiyata Ta Yi Gwagwarmaya Da Rayuwa Wajen Tarbiyyantar Dani. Duk Da Bamu Dashi Da Yawa, Mun Rayu Cikin Soyayya Da Girmama Juna.
Ina Da Burin Zama Lauya Domin Na Taimaki Mata Irina. Ina Karatu A Makarantar Firamare Lokacin Da Na Fara Fuskantar Tsanani Daga Rayuwa. Muna Zaune A Gidan Haya, Makarantarmu Na Nesa, Kullum Sai Na Yi Tafiya Mai Nisa Domin Kafinnan..
A Cikin Wannan Yanayi Ne Wani Mutum Mai Suna Ahmad. Ya Kasance Maƙwabcinmu, Ya Girme Ni Da Shekara Bakwai. Yana Kula Dani Kamar ƴar'uwarsa, Amma Har Cikin Raina Na Fara Jin Wani Abu, Kamar Dai Soyayya. Ina Girma, Na Taso A Cikin Daddadan Murya Da Tausayin Ahmad. Yana Da Ladabi, Wayewa, Kuma Ko Da Yaushe Cikin Taimako.
Lokacin Da Na Fara Sakandare Ne Na Gane Cewa Idanuna Sun Rufe Da Soyayyarshi. Na Fara Ganin Ahmad A Mafarkina, Na Fara Kiran Sunansa Cikin Addu’o’ina. Sai Dai Ko Da Yaushe, Bai Taɓa Nuna Min Komai Ba. Sai Sannu A Hankali Na Yanke Shawarar Bayyana Masa Abinda Nake Ji.
Wata Rana Da Daddare Bayan Na Kammala Karatu A Falon Gidanmu, Na Rubuta Masa Saƙo A Kan Takarda:
"Ahmad, Nice Zainab. Ina Girmama Ka Fiye Da Kowanne Mutum A Rayuwata. Ban San Yadda Zaka Ji Wannan Kalmar Ba, Amma Ina Sonka."
Na Ajiye Takardar A Ƙofar Gidansu Da Fatan Shi Zai Gan Ta. Washegari Da Safe Lokacin Da Muka Haɗu A Hanya Yana Tafiya, Ya Kalle Ni Cikin Ido Yana Murmushi, Amma Bai Ce Komai Ba. Sai Ranar Da Yamma Ne Ya Aika Min Da Saƙo Ta Waya:
"Zainab... Na Karanta Saƙonki. Kuma Ban Taɓa Tunanin Ke Kina Da Wannan Zuciyar Ba. Na Ji Daɗin Abinda Kika Rubuta. Ni Ma Ina Son Ki... Amma Ki Bari Mu Jira Lokaci, Ki Mayar Da Hankali Wajen Karatunki."
Wannan Kalma Ta Sa Hankalina Ya Kwanta. Na Ji Rayuwata Ta Canza. Kowanne Dare Ina Tunani, Ina Rera Waka A Raina, Na Sanya Sunansa Cikin Dukkan Littafin Karatuna.
Sai Dai Na Manta Da Abu Ɗaya: Duk Wanda Ya Ce A Jira Lokaci... Wataƙila Bai Shirya Ba. Kuma Wataƙila Bai Da Niyya.
Lokaci Na Tafiya. Muna Yawan Hira, Saƙonni, Da Ban Dariya. Amma Ko Da Yaushe Idan Zanyi Maganar Soyayya Sai Ya Dakatar Danj.
Na Kammala Sakandare, Na Samu Admission A Jami’a, Shima Ya Samu A Wani Wajen. Hakan Bai Sa Mun Daina Hira Ba, Sai Dai Ya Rage. Na Fara Jin Sanyi A Cikin Muryarsa. Ya Rage Turo Saƙƙoni. Daga Nan Na Fara Jin Tsoro, Kar Dai Na Rasa Ahmad.
Wata Rana Na Tura Masa Da Hotona Sanye Da Hijabi Tare Da Cewa:
"Dan Allah Inaso Ka Tabbatar Min Da Cewa Har Yanzu Ina Cikin Ranka.”
Bai Min Reply Ba,. Sai Bayan Kwana Biyu Ne Yayi Reply,
"Zainab, Kar Ki Ji Komai. Ina Son Ki Har Yanzu. Karatu Ne Yayi Min Yawa. Na Ce Miki Mu Jira Lokaci. Kada Ki Sa Damuwa A Ranki.”
Daga Nan Na Shiga Tashin Hankali, Tabbas Bana Cikin Ransa.
Wata Rana Na Gan Shi A Status Din Wani Abokinsa… Tare Da Wata Budurwa. Suna Dariya, Har Rangwaɗa Take Masa Suna Nishadi.
Na Rasa Me Zan Ce. Na Rasa Natsuwa. Na Rasa Kaina Gabadaya. Na Sani, Tabbas Na Rasa Ahmad.
Zaka Iya Turo Mana Da Naka Labarin Ko Kayi Sharing Domin Wasu Zasu Amfana 🙏👍