Flash News Hausa

Flash News Hausa Domin Samun sahihan labarai

Hausa Novels Cinema - Fauziya D Sulaiman Novels, Hausa Novels Complete Documents, Gidan Uncle Hausa Novels, Free Hausa Novels Groups And Audio Hausa Novels.

Zamfara ta yi cikar ƙwari yayin da Marafa ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensaJihar Zamfara ta cika makil da dand...
14/09/2026

Zamfara ta yi cikar ƙwari yayin da Marafa ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Jihar Zamfara ta cika makil da dandazon jama’a a daren Litinin, yayin da ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NDC, Sanata Kabiru Marafa, ya kai ziyara jihar domin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

A yayin gangamin, Marafa ya gwangwaje wasu jiga-jigan jam’iyyar da manyan motoci na alfarma, inda ya bayyana cewa kowace mota da ya bayar ta yi daidai da motoci 100 da, a cewarsa, ’yan jam’iyya mai mulki ke iya bayarwa.

Marafa ya ce ’yan jam’iyya mai ci ba sa iya yin irin wannan kyauta, yana mai cewa tun bayan ficewarsa daga jam’iyyar ne aka daina yi wa talakawa da al’ummar Zamfara alheri.

Ya bayyana cewa yanzu da ya dawo, zai ci gaba da tallafa wa jama’a, yana mai cewa ya san idan ya fara, ’yan jam’iyya mai mulki za su kwaikwaye shi.

Dan takarar ya kuma bayyana cewa zai raba motoci har sau biyar, ga rukuni biyar na jiga-jigan yaƙin neman zaɓensa da na jam’iyyar NDC, daga sama har ƙasa.

Ya ƙara da cewa matasa da mata ma za su amfana da tallafin da zai bayar, domin rage musu matsin rayuwa da suke fama da shi a ƙarƙashin gwamnati mai ci.

Marafa ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da taimaka wa jama’a, yana mai cewa sauran bayanai za su biyo baya, yayin da zai ci gaba da ganawa da al’ummar Zamfara domin, a cewarsa, share musu hawayensu.

Ya kuma gode wa dandazon jama’ar da s**a halarci taron, tare da ba su haƙuri kan jinkirin da aka samu. Ya ce tun safe ya shigo jihar, amma yawan jama’ar da s**a tarbe shi ya hana shi ci gaba da gudanar da shirye-shiryensa har zuwa bayan ƙarfe 8 na dare.

14/09/2026

"Taimakonku Rarara ya yi da ya jawo ku ƙungiyarsa ta Triple R. Ku ci arziƙi, domin da ya bar ku a inda kuke wani ko shugaban ƙaramar hukumarsa ba zai iya gani ba. Ko ni ma shi ne yake taimako na ba ni ke taimakonsa ba" In Ji Bala Abubakar Musawa.

14/09/2026

Yadda Aliko Dangote ya buga kararrawar bude kasuwar NGX domin buɗe hanyar IPO na matatar mai ta Dangote

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana wasu muhimman manufofi 12 da ya ce zai mayar da h...
13/09/2026

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana wasu muhimman manufofi 12 da ya ce zai mayar da hankali a kansu idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a zaɓen 2027.
‎
‎1.Dawo da tallafin man fetur
‎Atiku ya ce zai dawo da tallafin man fetur domin rage tsadar sufuri da matsin rayuwa.
‎
‎2.Sake duba tsarin NELFUND
‎Ya ce zai sake duba tsarin NELFUND, ciki har da yiwuwar yafewa ɗalibai bashin karatu, domin ilimi ya kasance mai sauƙi da araha.
‎
‎3.Ƴancin ƙananan hukumomi
‎Ya ce zai aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, domin kuɗaɗen da ake ware musu su riƙa isa gare su kai tsaye.
‎
‎4.Farfaɗo da tashoshin ruwa
‎Atiku ya ce zai farfaɗo da tashoshin ruwa na Port Harcourt, Calabar da Warri, tare da ci gaba da shirin Uyo Deep Sea Port.
‎
‎5.Sake buɗe iyakokin ƙasa
‎Ya yi alkawarin sake buɗe iyakokin ƙasa domin bunƙasa kasuwanci da harkokin tattalin arziki.
‎
‎6.Sake fasalin tsarin harajin wutar lantarki
‎Ya ce zai sake fasalin tsarin harajin wutar lantarki domin kawo ƙarshen abin da ya kira wariya wajen biyan kuɗin wuta.
‎
‎7.Tallafin dala biliyan 10
‎Ya yi alkawarin samar da shirin tallafin dala biliyan 10 ga matasa da mata masu sana’o’i da sabbin kamfanoni.
‎
‎8.Ƙarfafa tsaro
‎Ya ce zai ɗauki ƙarin jami’an tsaro, inganta jin daɗinsu, tare da amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan sirri da yaƙi da ’yan bindiga, ’yan ta’adda da sauran miyagun laifuka.
‎
‎9.Farfaɗo da harkar noma
‎Ya ce zai inganta tsaro domin manoma su koma gonakinsu, rage kuɗin samar da amfanin gona, da faɗaɗa hanyoyin samun tallafin kuɗi ga manoma da ’yan kasuwa.
‎
‎10.Inganta harkar lafiya
‎Atiku ya yi alkawarin samar da ingantaccen magani mai araha, magance ƙarancin ma’aikatan lafiya, da inganta albashi da walwalarsu.
‎
‎11.Ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi iko
‎Ya ce zai rarraba wasu ƙarin iko zuwa jihohi da ƙananan hukumomi, ta hanyar sake fasalin jerin ikon Majalisar Tarayya.
‎
‎12.Aiwatar da Rahoton Oronsaye
‎Ya yi alkawarin aiwatar da Rahoton Oronsaye domin rage almubazzaranci, maimaita ayyuka da cunkoson hukumomin gwamnati.
‎
‎Atiku ya ce manufar shirinsa ita ce “Rescue, Revive and Restore.

11/09/2026

Shek Musa Yana cikin Koshin lafiya shi Kuma dan Ta,addan daya kawo masa Hari Yayi Mutuwar wulakanci a cikin kwata

11/09/2026

Ku kalli yadda Hon Ibrahim Masari ya dira garin Malumfashi cikin jirgi, don yin ta'aziyyar Sanata Mandiya

DA DUMI-DUMI: Mabiyan Shiekh Musa Lukwa sun kashe mutumin da ya yanke shi da wuka a SokotoAn kashe wani matashi da ake z...
11/09/2026

DA DUMI-DUMI: Mabiyan Shiekh Musa Lukwa sun kashe mutumin da ya yanke shi da wuka a Sokoto

An kashe wani matashi da ake zargi da daba wa wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukwa, wuka jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a masallacinsa da ke yankin Mabera, cikin birnin Sakkwato.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda rahotanni s**a ce matashin, wanda ake kira Mai Barewa, ya kasance cikin masu ibada a masallacin, kafin ya farmaki malamin tare da daba masa wuka sau biyu a wuya bayan kammala sallar.

Majiyoyi sun ce masu ibadar da ke wurin sun yi nasarar cafke wanda ake zargin, inda daga bisani s**a yi masa duka har ya mutu.

Rahotanni sun danganta harin da wata huduba da Lukwa ya gabatar a baya, inda ya ambaci wani Hadisi da wasu malaman addini, musamman masu alaƙa da ɗariƙar Sufaye s**a ce ya ɓata sunan iyayen Annabi Muhammad (SAW).

Bayan wannan cece-ku-ce, an ce Mai Barewa ya yi barazanar kashe Malam Lukwa da babban ɗalibinsa, Malam Murtala Assada.

Malamin da mabiyansa sun kai rahoton barazanar ga ’yan sanda, lamarin da ya kai ga k**a matashin da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. Kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na wani lokaci, yayin da shari’ar ke ci gaba.

Kwanaki huɗu kafin harin na Juma’a, Malaman sun kuma ziyarci fadar gwamnatin jihar Sakkwato, inda s**a gabatar da rubutacciyar ƙorafi kan lamarin.

Da yake tabbatar da faruwar harin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce Malam Lukwa na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Sakkwato.

Ya ce mabiyan malamin ne s**a kashe wanda ake zargin bayan sun cafke shi.

Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa kawo yanzu ba a k**a wani mutum dangane da tashin hankalin ba, sai dai rundunar ta ɗauki matakan da s**a dace domin hana lamarin ƙara ta’azzara.

Ya ce ’yan sanda na gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa harin da kuma gano duk mutanen da ka iya kasancewa da hannu a lamarin.

10/09/2026

Kalli yadda Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hon. Ibrahim Masari ya bada kudi Naira Miliyan 100 a rabawa wasu mata a jihar Katsina.

Ƙungiyar Triple R. Media, ƙarƙashin jagrancin Dauda Kahutu Rarara tana ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta a garin Kahutu da...
10/09/2026

Ƙungiyar Triple R. Media, ƙarƙashin jagrancin Dauda Kahutu Rarara tana ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta a garin Kahutu da ke Jihar Katsina yanzu haka domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027.

09/09/2026

Yanzu Kenan kowa sai dai ya kare Kansa ko Yaya ?

Address

Zooroad Atiku Abubakar Road
Kano
700001

Telephone

+2349070613079

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Flash News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Flash News Hausa:

Shortcuts

Share