
28/07/2025
Na Taso Cikin Rayuwar Ƙunci Da Ba Kowacce Yarinya Ke Fuskanta Ba. Mahaifina Ya Rasu Tun Ina Shekara Goma Sha Ɗaya, Mahaifiyata Ta Biyo Bayansa Shekara Biyu Bayan Rasuwar Sa. Daga Wannnan Lokaci Rayuwata Ta Canza Gabadaya. Ba Domin Rashin Iyaye Kadai Ba, Har Ma Da Yadda Duniya Ta Fara Juya Min.
Ina Zaune A Gidan Kawuna Allah Bai Bashi Haihuwa Ba, Tare Da Wata Yar Yafendona Maimuna A Unguwar Da Gabadaya Marasa Karfi Ne A Wajen. Akwai Wani Matashi A Unguwar, Sunansa Sameer, Farin Mutum Tsiriri, Da Idanu K**ar Na Zaki. Ko Wace Yarinya A Unguwar Tana Masa Kallon Zinari, Kowa Sha'awarsa Take Saboda Kyawu Da Kwarjininsa. Amma Ni Ban Taɓa Zaton Zan Iya Faɗawa Tarkonsa Ba… Har Sai Da Hakan Ta Faru.
Na Fara Lura Da Shi Ne A Lokacin Da Yake Wucewa Kofar Gidanmu Kullum Yakan Yi Min Murmushi. Daga Baya Ya Fara Tsayawa Yana Tambayata, Ko Kuma Yace Na Kawo Masa Ruwa, Daga Baya Ya Nemi Lambar Waya Na Domin Yana So Mu Ringa Gaisawa Idan Ya Tafi Kasuwa. Na Fara Jin Wani Abu Daban A Zuciyata, Wani Yanayi Da Ban Taɓa Fahimta Ba. Maimuna Ta Sha Fadamin Na Lura Da Irin Wadannan Mazajen, Amma Nace Mata “Wanda Bai Da Wata Manufa A Kanmu Tayaya Zai Cutar Damu?”
A Hankali Na Fara Mantawa Da Gargaɗinta, Ina Faɗawa Cikin Duniyar Da Ban Sani Ba. Na Fara Tsayawa Ina Bata Lokaci Mai Tsayi Tare Dashi Muna Hira, Yana Jefo Min Kalaman Kwantar Da Hankali Da Zance Irinsu "Kin Fi Kowacce Mace Mutunci Da Kima", Da Kuma "Ban Taɓa Ganin Mace K**ar Ki Ba", Har Da "Da Zan Samu Mace Irin Ki, Da Babu Abinda Zai Hana Ni Aure Nan Bada Jimawa Ba."
Watarana Da Dare Bayan Sallah, Sai Ya Kira Ni A Waya Ya Ce Zai So Muyi Magana Sosai, Face To Face, Inda Ba Mai Jinmu. Na Ce Masa To. A Lokacin Maimuna Ta Sake Min Gargadi Na Kula Da Kyau Kar Na Kuskura Na Barshi Ya Fara Min Ɗabi'ar Da Zanzo Ina Da-Na-Sani Wato Ya Taɓa Jikina Ko Mak**ancin Haka. Na Yarda, Na Wuce Wajen Da Muka Shirya Haɗuwa.
Muka Hadu A Bayan Wani Tsohon Shago, Inda Fitilar Solar Ke Aiki. A Nan Ya Dube Ni Cikin Ido Yace:
"Ina Son Ki… Ba Don Ke Marainiya Bace. Ni Da Gaske Nake, Kuma Ina Jin Kece Maacen Da Zata Iya Zama Matata."
Na Ji K**ar Sama Zata Fashe. Wannnan Shi Ne Karo Na Farko Da Wani Ya Furta Min Irin Wannnan Magana Kuma Cikin Tausasawa, Kulawa Da Girmamawa. Na Yarda Da Shi Da Zuciyata, A Lokacin Naji Na Faɗa Sabuwar Duniya.
Bayan Kwana Biyu Ya Roƙe Ni Da Na Zo Gidansa Saboda Bashi Da Lafiya, Kuma Ba Shi Da Kowa A Kusa. Da Farko Na Ki, Amma Kalamansa S**a Ja Ni. Mukayi Magana Da Yar Uwata Maimuna Na Fice Ta Katanga A Sulale Ba Tare Da Kowa Ya Sani Ba.
Na Wuce Inda Yake Kwana, Ina Shiga, Na Tarar Da Gidan A Tsaftace, Ya Buɗe Min Kofa Da Murmushi, Yana Sanye Da Kayan Bacci. Na Zauna. Sai Ya Fara K**ar Kuka, Yana Cewa Yana Jin Tsoro Kar Na Barshi, Babu Abinda Zai Same Ni. Na Dube Shi Cike Da Tausayi Nace "Ba Zan Taba Barinka Ba." Wannnan Shine Lokacin Da Komai Ya Canza Min Nayi Alkawarin Da Yafi Ƙarfi Na.
Ya Matso Kusa Dani, Yana Kokarin K**a Hannaye Na. Nikuma Na Janye Ina Kallon Gefe. Ya Saki Miko Hannunsa Kan Kafaduna A Hankali Na Ji Hannunsa Yana Yawo A Jikina, Da Yana Ambaton "Ki Yarda Dani, Wallahi Ina Sonki Ne, Banida Da Yadda Zanyi, Ke Tawa Ce Har Abada". Na Juya Na Kalle Shi Har Cikin Idanu Yana Kallona, Muka Jima A Haka, Sa'annan Ya Turo Bakinsa A Hankali Ya Fara Sumbata Ta.
Abin Da Ya Faru Daga Nan Ba Zan Iya Cewa Komai Ba. Amma A Wannnan Rana Na Sadaukar Da Komai, Jikina Da Amincina, A Daren Nan Don Kawai In Tabbatar Da Soyayyata A Gare Shi.
Washegari, Na Farka Da Hasken Rana Yana Haskawa Kofar Dakin. Na Juyo, Na Same Shi Yana Shiryawa. Bai Ce Min Komai Ba, Ba Tare Da Ya Kalli Inda Nake Ba Yace “Ki Koma Gida Kafin A Fara Neman Ki.” Babu Abinda Ya Kara Faɗa. Haka Na Tashi Na Koma Gida Zuciyata Gabadaya Tayi Nauyi.
Bayan Kwana Biyu… Na Kira Wayarsa Bai Ɗauka Ba. Na Aika Masa Da Text, Bai Amsa Ba. Na Aiko Maimuna Ta Leƙa Gidansa, Tace Min Ya Tafi Abuja Tun Shekaranjiya.
Daga Nan Ne Zuciyata Ta Fara Girgiza K**ar Girgizar Kasa.
Na Fara Jefowa Kaina Tambayoyi Shin Ya Cutar Da Ni Ne Kawai Don Ya Biya Bukatarsa? Ko Kuwa Wani Abu Ne Ya Faru Da Bai Sanar Da Ni Ba?...
✍️ Cigaban Labarin Zaizo Bayan Kunyi Mana Sharing 100 😊 Da Comments ✊ Muje Zuwa