Sahihiya Online

Sahihiya Online Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sahihiya Online, Digital creator, Kano.

Wace Shawara zaku iya bawa masu Sai da Ƙanƙara..?
21/02/2026

Wace Shawara zaku iya bawa masu Sai da Ƙanƙara..?

Kamfanin MOHDIBRA TRAVELING AND TOURS LTD na sanar da jama’a cewa wasu mutane biyu, Adnan da Khalid, suna yin ƙarya da a...
20/02/2026

Kamfanin MOHDIBRA TRAVELING AND TOURS LTD na sanar da jama’a cewa wasu mutane biyu, Adnan da Khalid, suna yin ƙarya da amfani da sunan kamfanin ba tare da izini ba, suna ikirarin mallaka da gudanar da harkokinsa.

Kamfanin ya bayyana cewa Alh. Muhammad Ibrahim ne halastaccen Shugaba (CEO) na kamfanin, wanda ke da ofishi a Suite 12/13b Sanfa Plaza, Plot 2055 Ndola Crescent, Wuse Zone 5, Abuja, Nigeria. Babu wata alaƙa tsakanin kamfanin da waɗannan mutane ko duk wani da ke amfani da sunan kamfanin ba bisa ka’ida ba.

Management ya gargadi waɗanda abin ya shafa da su daina wannan haramtacciyar ɗabi’a nan take, in ba haka ba za a ɗauki matakan shari’a kan laifukan satar suna, jabun takardu da cin zarafin alamar kasuwanci.

An kuma buƙaci jama’a su tabbatar da sahihancin duk wata hulɗa da ake cewa an yi da sunan kamfanin, domin kamfanin ba zai ɗauki alhakin duk wata asara da ta taso daga hulɗa da marasa izini ba.
Duk wanda ke da bayani ko ya fuskanci irin wannan matsala, ya tuntuɓi kamfanin ta adireshin da ke sama.

14/01/2026

Kaji Rabo....

Anyi Nasarar k**a Mutane Uku da ake zargi yan fashi ne tare Binga kirar pistol guda  biyu da harsashi guda 23 A jihar Ka...
09/01/2026

Anyi Nasarar k**a Mutane Uku da ake zargi yan fashi ne tare Binga kirar pistol guda biyu da harsashi guda 23 A jihar Kano

NANS ta koka kan watsi da ɗaliban Najeriya da aka bai wa tallafin karatu a ƙasashen wajeƘungiyar ɗaliban Najeriya (NANS)...
07/01/2026

NANS ta koka kan watsi da ɗaliban Najeriya da aka bai wa tallafin karatu a ƙasashen waje

Ƙungiyar ɗaliban Najeriya (NANS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ma’aikatar ilimi da su gaggauta magance zargin watsi da ɗaliban Nijeriya da aka bai wa tallafin karatu a ƙasashen waje, musamman a ƙasar Morocco.

A wata sanarwa da mataimakin shugabanta mai kula da harkokin waje, Kwamared Kenechukwu Aneke, ya fitar, NANS ta ce ɗaliban da aka tura ƙasashen waje ƙarƙashin shirye-shiryen tallafin gwamnati sun shiga matsanancin hali, inda wasu ke fama da yunwa da rashin kulawa.

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan rahoton mutuwar wani ɗalibi, Bashir Malami, wanda ta ce hakan ya nuna sak**akon sakaci da gazawar hukumomi wajen amfani da kuɗaɗen da aka ware domin tallafin karatun.

NANS ta yi Allah-wadai da abin da ta kira cin amana daga hukumomin da abin ya shafa, tare da kiran shugaban ƙasa Bola Tinubu, ministan ilimi da hukumar tallafin karatu ta tarayya da su ɗauki matakan gaggawa.

Ƙungiyar ta buƙaci a dawo da ɗaliban da abin ya shafa, a biya su dukkan alawus-alawus ɗin da ake binsu, a binciki zargin almundahanar kuɗi, da kuma sake fasalin tsarin tallafin karatu na ƙasashen waje domin hana maimaituwar irin wannan matsala.

Mahukunta sun daƙile yunƙurin juyin mulki a Burkina FasoHukumomin Burkina Faso sun bayyana cewa sun gano tare da kuma da...
07/01/2026

Mahukunta sun daƙile yunƙurin juyin mulki a Burkina Faso

Hukumomin Burkina Faso sun bayyana cewa sun gano tare da kuma daƙile wani shirin juyin mulki da aka tsara don kashe shugaban sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, da kawo rashin kwanciyar hankali a kasar a karshen mako da ya gabata.

BBC ta rawaito cewa Ministan tsaro ƙasar, Mahamadou Sana, ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya yi a daren ranar Talata, inda ya nuna wani bidiyo da ke nuna yadda aka shirya kai hari ga shugaban kasar ko dai ta hanyar harbin shi kai tsaye ko kuma ta hanyar sanya bam a gidansa a daren 3 ga watan Janairu, kafin a kai farmaki ga sauran manyan jami’an soja da na farar hula.

Ministan ya kuma zargi tsohon shugaban kasar da aka hamɓarar a shekarar 2022, Laftanar Kanar Henri Damiba, da tsara juyin mulkin.

Rahotanni sun ce tsohon shugaban ya tara sojoji da magoya bayansa fararen hula inda ya samu kudade kimanin CFA miliyan 70 daga Côte d’Ivoire sannan ya tsara lalata sansanin harba jirage marasa matuƙa kafin sojojin ƙasashen waje su shiga tsakani.

Ministan ya ce an k**a mutane da dama kuma ana ci gaba da bincike, inda za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

Tun bayan karɓar mulki a 2022, Traoré ya fuskanci yunƙuri da dama na juyin mulki da tashin hankali daga kungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

Ko Kanawa Za Su Zabi Gwamna Abba A Zaben 2027 Idan Ya Koma APC?
07/01/2026

Ko Kanawa Za Su Zabi Gwamna Abba A Zaben 2027 Idan Ya Koma APC?

Sahihiya Online — Muryar GaskiyaSahihiya Online kamfani ne na kafafen yada labarai na zamani da ke tsaye kan gaskiya, ad...
07/01/2026

Sahihiya Online — Muryar Gaskiya

Sahihiya Online kamfani ne na kafafen yada labarai na zamani da ke tsaye kan gaskiya, adalci, da sahihin bayani. Zaku iya turomana Rahoto na Gaskiya dake faruwa a yan kunan ku Akan wannan Number 08146605388

Za a Tsige Shugaban Amurka Donald Trump idan Republican ta sha kaye a MajalisaShugaban Amurka, Donald Trump, ya ce zai i...
07/01/2026

Za a Tsige Shugaban Amurka Donald Trump idan Republican ta sha kaye a Majalisa

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce zai iya fuskantar impeachment idan Jam’iyyar Republican ba ta samu rinjaye a Majalisar Dokoki a zaɓen tsakiyar wa’adi mai zuwa. Ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da ‘yan jarida, yana mai cewa sak**akon zaɓen na iya shafar matsayinsa a siyasa.

Wacce shawara za ku bai wa shugaba Tinubu a wannan sabuwar shekara ta 2026?
07/01/2026

Wacce shawara za ku bai wa shugaba Tinubu a wannan sabuwar shekara ta 2026?

Rundunar yansandan jihar Neja sun gano wani bom da bai fashe ba a ƙauyen Zugurma na ƙaramar hukumar Mashegu.
07/01/2026

Rundunar yansandan jihar Neja sun gano wani bom da bai fashe ba a ƙauyen Zugurma na ƙaramar hukumar Mashegu.

Fitowar tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami tare da matarsa Hajiya Asabe Malami daga babban kotun tarayya da ke Abuj...
07/01/2026

Fitowar tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami tare da matarsa Hajiya Asabe Malami daga babban kotun tarayya da ke Abuja bayan bayar da belinsu.

Yanzu dai za a jira a gani ko hukumar kula da gidan gyaran hali za ta sakesu a yau ko kuma.

Address

Kano
700001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sahihiya Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sahihiya Online:

Share