
17/09/2025
Da dumi'dumi: Jihar Kano tazo ta ɗaya wajen cin Jarabawar NECO.
Hukumar shirya jarabawar sakandare ta ƙasa (NECO) ta fitar da jerin jihohin da s**a fi samun nasara a jarabawar 2025.
Ga yadda sak**akon ya kasance:
Kano ta zo ta farko inda ɗalibai 68,159 s**a samu sakandare 5 credits da sama (da lissafi da turanci ciki).
Lagos ta zo ta biyu da ɗalibai 67,007.
Oyo ta tsaya a mataki na uku da ɗalibai 48,742.
Wannan sak**ako ya nuna cigaba da ƙoƙarin da hukumomi da iyaye suke yi wajen inganta ilimi a jihohinsu.